INEC Ta Matso da Nesa Kusa, Ta Fadi Abin da Zai Sa Ta Samu Nasara a Zaben 2027
- Hukumar INEC ta ce nasarar zaben da za ta shirya a 2027 ta dogara ne kan yadda sababbin masu kada kuri'a suka amince da ita
- Shugaban INEC na kasa, Farfesa Joash Amupitan ne ya bayyana hakan a taron horarwa da hukumar ta shirya wa kwamishinonin zabe
- Ya ce INEC za ta shirya zabubbuka da dama kafin shekarar 2027, wanda ya hada da zaben gwamna a jihohin Ekiti da Osun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta yi tsokaci kan babban zaben 2027 da ke kara gabatowa.
INEC ta bayyana cewa akwai bukatar ta samu yardar miliyoyin matasan Najeriya domin samun damar shirya zaben 2027 cikin nasara.

Source: Twitter
Abin da zai ba INEC nasara a zaben 2027
A rahoton The Cable, INEC ta ce nasarar zaɓen da za ta shirya a 2027 zai dogara ne kan yadda za ta samu amincewar miliyoyin matasa ‘yan Najeriya da za su jefa ƙuri’a karo na farko.

Kara karanta wannan
Matsala ta tunkaro, an yi hasashen gwamnonin APC 8 za su juya wa Tinubu baya a 2027
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana haka a ranar Juma’a a Legas yayin da yake gabatar da jawabin buɗe taron horo da dabaru ga kwamishinoni da manyan jami’ai.
Amupitan ya ce sababbin masu kada kuri'a za su taka rawa a zaɓen 2027, musamman matasa masu gogewar fasahar zamani, wadanda ba za su hakura da rashin gaskiya ba.
INEC ta fadi shirinta ga matasa a 2027
A sanarwar da INEC ta wallafa a X, Amupitan ya ce:
“Dole ne mu fahimci cewa zaben 2027 zai kasance karkashin tasirin sabon rukuni ‘yan Najeriya, ma'£[£ miliyoyin matasan da za su fara jefa ƙuri’a a karon farko.
“Su matasa ne masu ilimin fasaha, waɗanda ke buƙatar gaskiya kuma ba su da haƙuri idan aka gaza bayyana gaskiya. Za mu tabbatar wa waɗannan matasa masu wayau, cewa INEC abin dogaro ce.”
Ya ƙara da cewa, ta hanyar gina tsarin da ya haɗa kowa da kuma amfani da fasaha, hukumar INEC ba kawai za ta shirya zaɓe ba ne, za ta kara gina yardar al'umma da tsarin zabe.

Source: Twitter
Abubuwan da ke gaban INEC kafin 2027
Amupitan ya ce tafiyar INEC zuwa 2027 za ta wuce ta muhimman matakai, ciki har da zaɓen kananan hukumomin Abuja da aka shirya a Fabrairu 2026, da kuma zaɓen gwamna a jihohin Ekiti da Osun.
“Waɗannan zaɓubbuka ba kawai ayyukan yau da kullum bane, su ne za su zama kamar gwaji na jajircewar mu da shirinmu,” in ji shi.
Ya bayyana cewa INEC za ta daidaita muhimman ayyukanta kamar gudanar da rajistar masu jefa ƙuri’a da na'urar tantance masu jefa ƙuri’a (BVAS).
INEC ta saki sunayen 'yan takarar gwamnan Ekiti
A wani rahoton, kun ji cewa INEC ta fitar da jerin sunayen ’yan takarar gwamna da mataimakansu a zaɓen gwamnan Jihar Ekiti da aka shirya yi a 2026.
Abin da ya fi daukar hankali a sunayen da INEC ta fitar shi ne rashin ganin sunan dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a zaben Ekiti.
Jerin sunayen ya ƙunshi ’yan takara daga jam’iyyun siyasa 12 da ke shirin gwabza wa domin neman kujerar gwamna da mataimakinsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
