"Tun Ina NYSC," Datti Baba Ahmed Ya Dura kan Jagoran ADC, Atiku Abubakar

"Tun Ina NYSC," Datti Baba Ahmed Ya Dura kan Jagoran ADC, Atiku Abubakar

  • Tsohon abokin takarar Peter Obi a LP, Yusuf Datti Baba-Ahmed ya ce lokaci ya yi da za a ba matasa masu jini a jika damar karbar ragamar mulkin Najeriya
  • Datti ya bayyana cewa tun lokacin yana NYSC Atiku Abubakar ke neman takarar shugaban kasa kuma da alama yana shirin sake fitowa a 2027
  • Tsohon Sanatan ya ce akwai matasa 'yan zamani da za su iya warware matsalolin kasar nan amma tsadar siyasa da tsarin ubangida ya hana su fitowa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa a inuwar LP, Yusuf Datti Baba-Ahmed ya ce lokaci ya yi da tsofaffi za su kauce su ba matasa masu jini a jika damar jagorantar Najeriya.

Datti Baba-Ahmed ya kuma nuna damuwa kan tsawon lokacin da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya dauka yana neman mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

Datti Baba Ahmed ya ayyana tsayawa takarar shugaban kasa, ya kara da Tinubu a 2027

Datti Baba Ahmed.
Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa, Datti Baba-Ahmed yana hira da manema labarai a Abuja Hoto: Datti Baba-Ahmed
Source: Twitter

A wata hira da Channels TV, Datti ya bayyana cewa tun lokacin da yake yi wa kasa hidima watau NYSC, ya san Atiku Abubakar da neman kujerar shugaban kasa.

Yusuf Datti Baba-Ahmed ya soki Atiku Abubakar

Jigon jam'iyyar LP ya ce duba dadewar irinsu Atiku a duniya, ya kamata a bar matasa masu danyen jini dama a siyasar Najeriya.

Datti ya ce:

"Tun ina NYSC Baba Atiku ke neman takarar shugaban kasa, amma a 2018 zai ga shi mun fafata da shi a zaben fitar da gwani.
"A zaben 2023 kuma mun gwabza da shi, ni ina matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa, yanzu wanda ya masa dan takarar mataimaki ya gudu ya bar sa, kuma dan Allah sai ya sake takara a 2027?
"Muna bukatar samun sababbin shugabannin kasa matasa yan zamani, kuka akwai su. 'Yan zamanin yanzu suna bukatar canjin shugabanci, su na bukatar sabon jini ya jagorance su."

Kara karanta wannan

Malami ya fadi manyan Najeriya 3 da za su tilasta wa Atiku janye wa Jonathan

Shin matasa za su iya gyara Najeriya?

Datti Baba-Ahmed ya kara da cewa Najeriya cike take da matasa, wadanda za su iya warware matsalolin da aka jima ana fama da su a kasar nan.

Sai dai a cewarsa, galibinsu sun koma gefe ne saboda tsoro, tsarin siyasa mai tsada da kuma rashin iyayen gida da za su mara masu baya.

A rahoton Daily Trust, jigon na LP ya ce:

“Akwai ‘yan Najeriya masu nagarta da za su iya warware matsalolin kasar nan amma suna jin tsoro saboda tsarin siyasa mai tsada, wahala, da tsarin ubangida da siyasar Najeirya ta gada."
Atiku Abubakar.
Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma jagoran adawar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar Hoto: @Atiku
Source: Getty Images

Datti Baba-Ahmed ya ce akwai matasa ‘yan siyasa na zamani da ke da sha’awar kawo sauyi a tsarin siyasar Najeriya, amma yadda tsarin ya ke, yana masu wahala tare da hana su samun dama.

Atiku na shirin hakura da takara a 2027?

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya tabbatar da shirinsa na sake neman takara a zaben 2027.

Kara karanta wannan

An fadi shekarun da mulki zai yi a Kudu kafin ya dawo yankin Arewa

Atiku Abubakar ya sha alwashin cewa ba zai janye wa kowa daga takarar shugaban kasa a zaben 2027 ba da ke tafe ba.

Wazirin Adamawa ya kuma zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da yunkurin mayar da Najeriya kasa mai jam’iyya daya, ta hanyar raunana jam’iyyun adawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262