Bayan Fara Shirin Tsige Shi, Majalisar Dokoki Ta Mika Takarda ga Gwamna Fubara

Bayan Fara Shirin Tsige Shi, Majalisar Dokoki Ta Mika Takarda ga Gwamna Fubara

  • Majalisar dokokin jihar Ribas na ci gaba da kokarin bin matakan da doka ta tanada a shirinta na tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa
  • Hakan dai ya biyo bayan sake barkewar rikici tsakanin Majalisa da Mai girma Simi Fubara, wanda rigimarsa da Nyesom Wike ta dawo sabuwa
  • 'Yan Majalisar dokokin Ribas ta tabbatar da cewa ta mika takardun sanar da shirin tsigewa ga Gwamna da mataimakiyarsa wato Farfesa Ngozi Odu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers, Nigeria - Majalisar dokokin jihar Ribas ra tura takardu domin sanar da shirinta ga Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Odu

Tun da farko, majalisar dokokin ta fara bin matakan tsige gwamnan da mataimakiyarsa a ranar Alhamis, lamarin da ya sake dagula rikicin siyasa a jihar Ribas.

Fubara.
Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Fibas da ke fuskantar barazanar tsigewa daga Majalisa Hoto: Sir. Siminalayi Fubara
Source: Facebook

A wani sako da Majalisar Dokokin Ribas ta wallafa a shafinta na Facebook a daren Alhamis, ta bayyana cewa ta mika takardar sanar da shirin tsigewa ga Gwamna Fubara da Odu.

Kara karanta wannan

Siyasar Rivers: Dalilan da suka jawo sabon rikici tsakanin Fubara da Wike

Majalisa ta mika takarda ga Farfesa Odu

Majalisar ta sanar da cewa an samu nasarar mika takardar shirin tsige wa ga Mataimakiyar Gwamna, Farfesa Ngozi Nma Odu, da misalin ƙarfe 7:00 na yamma.

“An mika takardar sanar da shirin tsigewa ga mataimakiyar gwamnan jihar Ribas, Farfesa Ngozi Nma Odu,” in ji majalisa.

Sakon Majalisa ya isa ga Gwamna Fubara

Sa’a guda bayan haka, majalisar ta sake wallafa cewa an mika wa Gwamna Siminalayi Fubara takardar shirin tsige shi.

Majalisar ta ce:

“Mun samu nasarar mika takardar shirin tsigewa ga Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara."

Majalisar ta wallafa kwafen takardun a shafin Facebook ɗinta, sai dai ba ta bayyana hanyar da aka bi wajen mika takardun ba.

Rikicin Gwamna Fubara da Wike ya dawo

Mika takardun na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan majalisar ta fara shirin tsige mai girma gwamna da mataimakiyarsa da misalin ƙarfe 10:15 na safe a zamanta na ranar Alhamis.

Sai dai jam’iyyar APC reshen Jihar Ribas ta yi watsi da yunkurin tsige gwamnan da mataimakiyarsa, inda ta bayyana matakin a matsayin barazana ga zaman lafiyar jihar.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta dauki zafi, ta yi magana kan shirin tsige Gwamma Fubara daga mulki

Fubara da Wike.
Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara da Ministan Harkokin Abuja, Nyesom Wike Hoto: Sir Siminalayi Fubara, @GovWike
Source: Facebook

Wannan ne karo na uku da Majalisar Dokokin Ribas ke yunƙurin tsige Gwamna Fubara tun bayan hawansa mulki a 2023 a yayin da rikici ke ƙara ƙamari tsakaninsa da Ministan Abuja, Nyesom Wike

Rikicin siyasar Ribas na ci gaba da ɗaukar sabon salo a baya-bayan nan, sai dai da ‘yan jihar da masu ruwa da tsaki sun zuba sa ido su ga yadda al’amura za su ƙare.

An nemi Shugaba Tinubu ya kori Wike

A wani labarin, kun ji cewa Kungiyar NADECO ta bukaci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya kori ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike daga aiki cikin gagggawa.

Kungiyar ta bukaci haka ne a matsayin mataki na kawo ƙarshen rikicin siyasa da ya daɗe yana addabar Jihar Ribas.

Shugaban NADECO USA, Dakta Lloyd Ukwu, ya zargi Nyesom Wike da kasancewa jigon rikicin Rivers, yana mai cewa ba za a samu zaman lafiya ba matuƙar ba a hukunta ministan ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262