Jam'iyyar PDP Ta Yi Zazzafan Martani kan Jita Jitar Gwamna Bala Zai Koma ADC

Jam'iyyar PDP Ta Yi Zazzafan Martani kan Jita Jitar Gwamna Bala Zai Koma ADC

  • Jam’iyyar PDP ta yi karin haske game da jita-jitar cewa Gwamna Bala Mohammed zai koma ADC a jiya Alhamis a Bauchi
  • Jam'iyyar ta karyata jita-jitar cewa Gwamnan na shirin ficewa daga PDP da ake ta yadawa a kafofin sadarwa na zamani
  • Shugaban PDP na jihar, Sama’ila Burga ya musanta zargin na a taron masu ruwa da tsaki da suka tabbatar da cikakken goyon baya ga gwamnan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bauchi - Jam’iyyar PDP reshen jihar Bauchi ta yi magana game da rade-radin shirin sauya shekar gwamna Bala Mohammed.

Jam'iyyar ta yi watsi da rahotannin da ke cewa Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na shirin ficewa daga jam’iyyar zuwa ADC.

PDP ta musanta rahoton cewa Bala Mohammed zai koma ADC
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi. Hoto: Sen. Bala Abdulkadir Mohammed.
Source: Twitter

PDP ta musanta rahotanni game da Gwamna Bala

Jam’iyyar ta bayyana rahoton a matsayin ƙarya, mara tushe da rashin da'a, tana kira ga jama’a da su yi watsi da jita-jitar kafafen sada zumunta, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: NNPP ta yi roko na musamman ga Abba Kabir kan shirin shiga APC

Hakan na cikin wata sanarwa da shugaban PDP a Bauchi, Hon. Sama’ila Adamu Burga ya fitar ya ce gwamnan ba shi da wata niyyar barin PDP.

Burga ya ce babu shakka ko kaɗan, Gwamna Bala Mohammed bai shirya komawa ADC ko wata jam’iyyar siyasa a Najeriya ba.

A taron, shugabanni da jiga-jigan jam’iyyar sun tabbatar da biyayyarsu ga PDP tare da kada ƙuri’ar amincewa ga Gwamna Bala Mohammed.

Burga ya ce manyan jami’an jam’iyya da suka halarta sun haɗa da mataimakin shugaban PDP na ƙasa, ‘yan majalisar dokoki da shugabannin kananan hukumomi.

Sauran sun haɗa da mambobin majalisar zartarwa ta jihar, tsofaffin sanatoci, tsofaffin kakakin majalisa da sauran manyan ‘yan siyasa a Bauchi.

PDP ta bayyana tasirin Gwamna Bala a jam'iyyar
Gwamna Bala Mohammed yayin jawabi a wani taro. Hoto: Sen. Bala Abdulkadir Mohammed.
Source: Twitter

'Kokarin da Gwamna Bala ke yi a Bauchi'

Masu ruwa da tsaki sun yaba da jajircewarsa, tawali’u, kishin dimokuraɗiyya da ƙoƙarinsa na tabbatar da shugabanci na gari a Bauchi.

Burga ya ce tsayin dakan gwamnan kan adalci da bin kundin tsarin mulki ya jawo masa matsin lamba da hare-haren kafafen yaɗa labarai.

Sai dai ya ce duk waɗannan ƙalubale ba su raunana ƙudurinsa ko sauya alkiblarsa ta kare dimokuraɗiyya da shugabanci na gari ba.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: An ji abin da Jonathan ya fadawa shugabannin jam'iyyar a Abuja

Shugaban PDP ya ce gwamnan ya nuna godiya matuƙa bisa ƙuri’ar amincewa da aka kaɗa masa daga shugabannin jam’iyya.

Ya jaddada cewa haɗin kai, tattaunawa da shugabanci na bai ɗaya su ne ginshiƙan PDP a dukkan matakai.

Ya ce:

“Babu wani lokaci da Gwamna Bala Mohammed ya taɓa nuna sha’awar ficewa zuwa ADC, APC ko wata jam’iyya."

Kiristoci sun gargadi Wike kan siyasar Bauchi

Mun ba ku labarin cewa Kungiyar Christian Youth in Politics (CYP) ta Bauchi ta gargadi Ministan Abuja, Nyesom Wike, da ya nisanci harkokin siyasar jihar.

CYP ta zargi Wike da katsalandan a siyasa, amfani da hukumomin tarayya, da matakan da ka iya barazana ga zaman lafiya a Bauchi.

Kungiyar ta kare Gwamna Bala Mohammed, tana cewa yana da cikakkiyar kariya ta kundin tsarin mulkin Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.