APC Ta Ɗauki Zafi da Ta Ji Jita Jitar Tsohon Shugaban Jam'iyya Ya Sauya Sheƙa zuwa ADC
- Jam'iyyar APC reshen jihar Nasarawa ta fusata bayan labaran da ke cewa Sanata Abdullahi Adamu ya koma wurin 'yan hamayya, ADC
- An samu wasu labarai da suka ce tsohon Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Adamu ya fice daga jam’iyyar har ya yi rajista da jam'iyyar ADC
- APC ta bukaci jama’a su yi watsi da labaran tare da bayyana asalin hoton da aka ce Abdullahi Adamu ya yanki tikitin ADC a Nassarawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Nassarawa – Jam’iyyar APC a jihar Nasarawa ta musanta jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa tsohon Shugabanta na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya sauya sheƙa zuwa ADC.
Jam’iyyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Sakataren tsare-tsaren jam’iyyar APC na jihar Nasarawa kuma mai kula da rajistar ƴan jam'iyya, Hassan Abubakar, ya fitar a ranar Alhamis a birnin Lafia.

Source: Twitter
Jaridar Punch ta ruwaito a cewar sanarwar, rahotannin da ke yawo ba su da tushe, kuma an ƙirƙire su ne domin yaudarar jama’a da kuma haddasa ruɗani a cikin jam’iyyar APC.
APC ta ƙaryata sauya sheƙar tsohon shugabanta
Daily Post ta ruwaito sanarwar ta jaddada cewa Sanata Abdullahi Adamu, wanda tsohon gwamnan jihar Nasarawa ne, har yanzu cikakken ɗan APC.
Jam'iyya mai mulki ta kuma nanata cewa bai taɓa ficewa ko nuna niyyar ficewa daga APC ba, saboda haka duk wata magana da ke nuna akasin haka ƙarya ce tsagwaronta.

Source: Twitter
A cewar Hassan Abubakar, hoton da ake yadawa a shafukan sada zumunta a matsayin hujjar wai Sanata Adamu ya koma wata jam’iyya, an ɗauke shi ne a lokacin aikin rajistar yanar gizo na APC.
Wannan rajista ta intanet shiri ne na ƙasa baki ɗaya, wanda a cewarsa, an ƙaddamar da shi ne domin ƙarfafa bayanan yan APC da kuma bunƙasa dimokuraɗiyyar cikin gida a jam’iyyar.
Jam'iyyar APC ta soki 'yan adawa
Jam’iyyar ta bayyana yunƙurin wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba na karkatar da wannan sahihin aiki a matsayin sauya sheƙa a matsayin rashin ɗa’a da kuma nuna matsananciyar yunwar siyasa.
Jam’iyyar ta ƙara da cewa irin waɗannan ayyuka na yaɗa bayanan ƙarya na nufin ɓatar da hankalin jama’a ne kawai da jawo rudani.
APC ta bukaci 'ya'yanta, kafafen watsa labarai da al’umma gaba ɗaya da su yi watsi da waɗannan raɗe-raɗi, su kuma dogara da sahihan bayanai daga ingantattun tushe.
APC ta dauki zafi kan batun Ribas
A wani labarin, mun wallafa cewa APC reshen Jihar Ribas ta yi fatali da yunkurin da ake yi a Majalisar Dokokin Jihar na tsige Gwamna Sir Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa.
Jam’iyyar ta bayyana shirin a matsayin abin da ba zai yiwu ba, tana mai gargadin cewa hakan na iya kara tsananta rikicin siyasa da tayar da hankalin gwamnati a jihar da ta samu kanta a kwanan nan.
Rahotanni sun ce kakakin Majalisar, Rt. Hon. Martins Amaewhule, ya bayyana Fubara a matsayin “kuskure,” tare da zarginsa da aikata manyan laifuffuka na rashin da’a a aikin gwamnati.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

