Boye Boye Ya Kare, Majalisar Kano Ta Yi Magana kan Shirin Gwamna Abba na Komawa APC

Boye Boye Ya Kare, Majalisar Kano Ta Yi Magana kan Shirin Gwamna Abba na Komawa APC

  • Majalisar dokokin Kano ta ce ya zama dole Gwamna Abba da duk wani zababben shugaba a jihar ya bar jam'iyyar NNPP
  • Shugaban masu rinjaye, Hon. Lawan Hussaini ya ce rikicin da ke faruwa a NNPP ne ya sa aka ba Kwankwaso da Abba shawarar sauya sheka
  • Ya ce Gwamna Abba da sauran zababbun shugabanni a Kano ba za su yi sakaci abin da ya faru da APC a Zamfara ya faru da su ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Majalisar Dokokin Kano a yau Alhamis ta tabbatar da rade-radin da ke yawo cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na shirin ficewa daga jam'iyyar NNPP zuwa APC mai mulki.

Majalisar ta kuma bayyana dalilin da ya sa ya zama dole Abba ya dauki wannan mataki a daidai wannan lokacin da ake shirye-shiryen tunkarar zaben 2027.

Kara karanta wannan

Abin da Kwankwaso da Ganduje suka fadawa Abba ana batun shigarsa APC

Majalisar dokokin Kano.
Zauren Majalisar dokokin Kano da ke Arewacin Najeriya Hoto: Kano State House
Source: Facebook

Majalisa ta yi magana kan shirin Abba

A wani rahoto da Premium Times ta kawo, Majalisar ta ce sauya shekar gwamnan Kano ya zama dole saboda rikicin shari'a da sauran rigingimun cikin gida da suka dabaibaye NNPP.

Shugaban masu rinjaye a Majalisar kuma wakilin mazabar Dala, Hon. Lawan Hussaini, ya shaida wa ’yan jarida a ranar Laraba cewa yana da haɗari a siyasance ga gwamna da sauran zababbu su ci gaba da zama a cikin NNPP.

A cewarsa, jam’iyyar NNPP na fama da rikicin shugabanci mai tsanani, wanda zai iya jefa kujerun da suka samu a zaɓe cikin hatsari yayin da ake tunkarar zaɓukan gaba.

Dalilan Abba da 'yan Majalisa na barin NNPP

Lawan Hussaini ya ce:

“Akwai hukuncin kotu da ya amince da wani bangare na NNPP, don haka ba za mu zauna a jam’iyyar ba mu iya fuskantar irin kalubalen shari'a shari’a da ya faru a jihar Zamfara ba.

Kara karanta wannan

Shekarau ya tsoma baki kan shirin Abba na komawa APC, ya tona wa Kwankwaso asiri

"Wannan ne ya sa ake ƙara kira ga Gwamna Abba Yusuf da jagorsnmu, Rabiu Musa Kwankwaso da su sauya sheƙa zuwa APC ko wata jam’iyya mai kwanciyar hankali.”

Majalisar Kano ta fara lallashin Kwankwaso

Ya ƙara da cewa Majalisar Dokokin jihar na ci gaba da tattaunawa da lallashin gwamna da Kwankwaso domin su cimma matsaya kan yadda za a fita daga NNPP cikin hikima.

Hon. Hussaini ya nuna damuwa cewa idan ba a magance rikicin shugabanci da shari'o'in da ke raba NNNP ba, kotu na iya yanke hukuncin cewa ’yan takarar jam’iyyar ba su da inganci, in ji TVC News.

Kwankwaso da Gwamna Abba.
Jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso tare da Gwamna Abba a wurin taro Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

A cewarsa, hakan na nufin ko da Gwamna Abba Yusuf da sauran 'yan takara sun sake lashe zaɓe a ƙarƙashin NNPP, kotu na iya tube su daga mukamai, kamar yadda ya faru da APC a Zamfara bayan zaben 2019.

A zaɓen 2019, APC ta lashe kusan dukkan muƙamai a Zamfara ciki har da gwamna da ’yan majalisa, amma saboda gazawar gudanar da sahihin zaɓen fitar da gwani, Kotun Koli ta yanke hukuncin cewa jam’iyyar ba ta da ’yan takara a idon doka.

Kara karanta wannan

Yadda Kwankwaso da Abba Kabir ke shirin ɓaɓewa bayan shafe shekaru 40 tare

Kwankwaso ya sake tabo batun shirin Abba

A wani rahoton, kun ji cewa jagoran NNPP na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso na ci gaba karbar magoya baya da ke jaddada mubaya'arsu a gidansa da ke jihar Kano.

Kwankwaso ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa shi ne zai yi dariya a ƙarshe game da rade-radin sauya sheƙar gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa masu cewa shi yaro ne a siyasa su jira lokaci, shi daagoya bayansa, za su nuna masu yarinta idan lokacin zabe ya zo.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262