Sunan Matawalle Ya Fito a Zargin Cafke Hadimin Gwamna Dauda, APC Ta Yi Magana
- Jam’iyyar APC a Zamfara ta wanke Ministan Tsaro Bello Matawalle daga zargin hannu a kama hadimin gwamna, Dauda Lawal Dare
- APC ta ce rundunar musamman ƙarƙashin ofishin Nuhu Ribadu ce ta kama shi bisa zargin alaƙa da ta’addanci da laifuffukan yanar gizo
- Jam’iyyar ta jinjina wa hukumomin tsaro, tana cewa Matawalle yana ƙasashen waje kan aikin ƙasa lokacin kama mutumin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Jam’iyyar APC ta yi magana game da zargin Bello Matawalle da hannu game da cafke hadimin gwamnan Zamfara ranar Talata, 6 ga Janairu, 2026.
APC ta bayyana cewa Ministan Tsaro na Ƙasa, Bello Matawalle, ba shi da hannu ko alaƙa da kama matashin mai suna Saleem Abubakar.

Source: Twitter
Hadimin Dauda Lawal: Jam'iyyar APC ta kare Matawalle
APC ta ce wata runduna ta musamman ce ta kama shi ƙarƙashin ofishin Mai Ba da Shawara kan Tsaron Ƙasa, Nuhu Ribadu kan zargin ta'addanci, cewar Tribune.
A cewar jam’iyyar, an kama Abubakar ne bisa zargin alaƙa da ta’addanci da kuma laifukan yanar gizo, lamarin da ya shafi tsaron ƙasa kai tsaye, wanda ba sai an nemi izinin kotu ba.
A wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran APC na jihar Zamfara, Mallam Yusuf Idris, ya fitar, ya ce danganta Matawalle da lamarin ba gaskiya ba ne kuma siyasa ce tsantsa.
Idris ya bayyana cewa abin mamaki ne yadda duk wani abu da ya shafi gwamnatin Zamfara ake ɗora laifinsa a kan Bello Matawalle, ko dai daga bakin gwamna ko kuma makusantansa.
Jam’iyyar ta zargi kakakin gwamnan da ɓoye muhimman bayanai kan zargin tsaro da ake yi wa mutumin da aka kama, domin karkatar da hankalin jama’a.
Sanarwar ta ce:
“Gaggawar kare mutumin da ake zargi da alaƙa da ta’addanci na ƙara tabbatar da zarginmu game da alaƙar gwamnatin PDP da wasu masu aikata laifuffuka.”

Source: UGC
APC ta fadi inda Bello Matawalle yake
APC ta yabawa hukumomin tsaro bisa yadda suka gudanar da aikin kama mutumin, tare da kira da a yi cikakken bincike mai zurfi wanda zai iya kai wa ga kama wasu.
Jam’iyyar ta kuma jaddada cewa Bello Matawalle yana ƙasashen waje ne a lokacin da aka kama Saleem, yana aiwatar da muhimmin aikin ƙasa, don haka ba zai yiwu ya yi tasiri kan haka ba.
A ƙarshe, APC ta ce tana goyon bayan ofishin Nuhu Ribadu, Ma’aikatar Tsaro da sauran hukumomin tsaro kan ƙoƙarinsu na kare tsaron Najeriya.
Kamarawa ya yi rantsuwa kan zargin Matawalle
A baya, kun ji cewa tsohon hadimin Bello Matawalle ya sake bayyana kansa kan zargin alakar ministan da ta’addanci a bidiyon da ya tayar da kura.
A bidiyon da aka yada a shafukan sada zumunta, Kamarawa ya ce bai aikata wani abu da kansa ba a zamanin mulkin Matawalle.
Musa Kamarawa ya rantse da Alƙur’ani Mai Girma, yana kalubalantar Matawalle da masu musun zargin da su rantse idan suna zarginsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

