Dalla Dalla: Matakai 8 da Majalisar Rivers Za Ta Bi domin Tsige Gwamna Fubara
Rivers - Tsige zaɓaɓɓen gwamna a Najeriya, kamar yadda ake shirin yi a jihar Rivers, wani babban al'amari ne na shari'a da siyasa wanda ke girgiza ginshiƙan dimokuradiyya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Wannan tsari ba wai kawai zai tsige Siminalayi Fubara daga kujera mafi matsayi a Rivers ba ne; hakan yana nufin soke zaɓin da dubun-dubatar ’yan jihar da yi na amince wa gwamnan ya jagorance su na tsawon shekaru huɗu.

Source: Twitter
Domin kare martabar kuri’ar al’umma, Kundin Tsarin Mulki na 1999 ya shimfiɗa matakai masu sarkakiya a Sashi na 188 domin tabbatar da cewa ba a tsige zababben gwamna ba tare da kwararan hujjoji na keta doka ba, in ji rahoton BBC.
Matakan tsige gwamna bisa tanadin doka
Kafin a iya tsige gwamna, dole ne a kiyaye matakai takwas, inda rashin bin ko guda ɗaya daga cikinsu zai iya sa kotu ta soke dukkan tsarin gaba daya:
1. Rubutaccen Zargi:
Dole ne akalla kashi ɗaya bisa uku na mambobin Majalisar Dokokin Jiha su rattaba hannu kan takardar da ke zargin gwamna da aikata babban laifi.
Babban laifi (Gross Misconduct) a nan yana nufin keta kundin tsarin mulki ko aikata laifin da a 'yan majalisa suka tsayu a kan ra'ayin cewa ya dace a tsige mutum a kansa.
2. Isar da takarda:
Shugaban Majalisa yana da kwanaki 7 ya tabbatar da cewa gwamna da kowane ɗan majalisa sun sami kwafin takardar da ke kunshe da wannan zargin.
3. Martanin gwamna:
Gwamna yana da haƙƙin rubuta raddi ga zarge-zargen, kuma dole ne a rarraba raddin ga kowane ɗan majalisa.
4. Yarjejeniyar bincike:
A cikin kwanaki 14, majalisa za ta kaɗa ƙuri'a ba tare da muhawara ba domin amincewa ko za a binciki gwamnan. Dole ne kashi biyu bisa uku na dukkan mambobi su amince.
5. Kafa kwamiti:
Idan majalisa ta amince, shugaban majalisa zai nemi Babban Alƙalin jihar ya kafa kwamitin mutum bakwai masu gaskiya waɗanda ba ’yan siyasa ba ne ko ma’aikatan gwamnati domin bincikar zargin.
6. Bincike da kariyar kai:
Kwamitin yana da watanni uku ya kammala aiki. A nan, gwamna yana da haƙƙin kare kansa da kansa ko ta hannun lauyoyi.
7. Tabbatar da laifi:
Idan kwamitin ya ga ba a tabbatar da laifin ba, magana ta ƙare. Idan kuma an tabbatar, za a gabatar da rahoton ga majalisa.
8. Matakin karshe:
Majalisa za ta yi la’akari da rahoton, idan kashi biyu bisa uku na dukkan mambobi suka kaɗa ƙuri’ar amincewa da rahoton, to gwamna zai sauka daga mulki nan take.
Tarihin yunkuri da tsige gwamnoni a Najeriya
Tun bayan dawowar dimokuradiyya a 1999, an yi yunƙurin tsige gwamnoni da dama. Wasu an yi nasara, yayin da wasu suka sha kasa a wajen shari'a, cewar wani rahoton The Guardian.
- Diepreye Alamieyeseigha (Bayelsa, 2005): An tsige shi sakamakon zargin almundahana, sata, cin zarafin ofis da halatta kudin haram. Shi ne Gwamna na farko da aka tsige a Jamhuriya ta Huɗu wanda bai iya komawa kan mulki ba.
- Rashidi Ladoja (Oyo, 2006): Majalisa ta tsige shi, amma Kotun Ƙoli ta mayar da shi bayan ta gano cewa ba a bi matakan da doka ta tanada ba, musamman batun inda aka yi taron majalisar da yawan mambobin da suka halarta.
- Peter Obi (Anambra, 2006): An tsige shi a ranar 2 ga watan Nuwamba, amma kotu ta mayar da shi kan mulki saboda rashin bin ƙa'idojin Sashi na 188.
- Joshua Dariye (Plateau, 2006): Mambobi shida kacal cikin ashirin da hudu suka tsige shi a lokacin. Kotun Ƙoli ta soke wannan tsigewar tare da bayyana ta a matsayin "rashin tarbiyyar majalisa."
- Murtala Nyako (Adamawa, 2014): An tsige shi bayan rikici da majalisa, kuma ko da yake kotu ta bayyana tsigewar a matsayin haramtacciya, bai samu damar komawa kan mulki ba saboda lokacin wa'adinsa ya riga ya ƙare.

Source: Facebook
Matsayin kotu da kalubalen siyasa
Kundin Tsarin Mulki a Sashi na 188(10) ya nuna cewa kotu ba ta da ikon tsoma baki a "hukuncin" majalisa ko kwamiti game da tsige gwamna da mataimakinsa, in ji wani rahoto da aka wallafa a shafin LawPadi.
Sai dai, Kotun Ƙoli ta Najeriya a shari'ar Inakoju vs. Adeleke (na Ladoja) ta kafa wani sabon tsari: Ta bayyana cewa ko da yake kotu ba za ta iya soke"matsayar" majalisa ba, tana da ikon bincikar ko "hanyar" da aka bi wajen tsigewar ta yi daidai da kundin tsarin mulki ko a a.
Wannan ya sa yanzu yana da wahala a tsige gwamna ba tare da bin dukkan matakai takwas ɗin nan sau-da-ƙafa ba, domin kotu za ta iya soke tsigewar idan aka gano wata baraka.
Wani babban ƙalubale shi ne amfani da ikon gwamnatin tarayya' wajen tursasa majalisu su tsige gwamnonin adawa, kamar yadda aka gani a zamanin mulkin tsohon shugaba Obasanjo. Wannan ya sa tsigewa ta zama tamkar takobin da masu mulki ke amfani da shi wajen sare abokan hamayya.
Wike ya kira Gwamna Fubara 'marar tarbiyya'
A wani labari, mun ruwaito cewa, Nyesom Wike ya ci gaba da sukar Gwamna Simi Fubara a rangadin da yake domin yi wa jama'a godiya a Ribas.
Ministan Abujan kuma tsohon gwamnan jihar Ribas ya bayyana Mai girma Gwamna Siminalayi Fubara a matsayin dan da bai gaji halin ubangidansa ba.
Nyesom Wike ya gode wa shugabannin al'umma da na siyasa a yankin karamar hukumar Asari-Torubisa jajircewa da goyon bayan da suka nuna masa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



