"Ni Zan Masu Dariya a Karshe," Kwankwaso Ya Kara Tabo Batun Sauya Shekar Gwamna Abba

"Ni Zan Masu Dariya a Karshe," Kwankwaso Ya Kara Tabo Batun Sauya Shekar Gwamna Abba

  • Jagoran NNPP na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso na ci gaba karbar magoya baya da ke jaddada mubaya'arsu a gidansa da ke jihar Kano
  • Kwankwaso ya bayyana cewa duk wannan surutun da ake yi game da sauya shekar Gwamna Abba, shi ne zai yi nasara a karshe
  • Ya bayyana cewa masu cewa shi yaro ne a siyasa su jira lokaci, za su nuna masu yarinta idan lokacin zabe ya zo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa shi ne zai yi dariya a ƙarshe game da rade-radin sauya sheƙar gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.

Rahotanni sun nuna cewa Gwamna Abba, wanda aka zaɓe shi a ƙarƙashin NNPP da taimakon Kwankwaso, ya yanke shawarar komawa jam’iyya mai mulki ta APC.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya fadi baiwarsa da abin da ya bambanta shi da sauran ƴan siyasa

Kwankwaso.
Jagoran NNPP na kasa, Rabiu Kwankwaso lokaci da ya karbi bakuncin kungiyoyi 21 a Kano Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Sai dai Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano, ya nuna adawa da matakin, yana mai cewa idan har Abba zai sauya sheƙa, to ya kamata ya ajiye kujerarsa ta gwamna, in ji The Nation.

Rikicin da ya ɓarke tsakanin manyan ’yan siyasar biyu ya raba jam’iyyar NNPP da kuma tafiyar Kwankwasiyya, wato ƙungiyar da ke ɗauke da magoya bayan jam’iyyar a faɗin ƙasar.

Rabi'u Kwankwaso ya ja hankalin mabiyansa

A wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, Kwankwaso ya yi kira ga magoya bayansa da fara daura damarar fara wayar da kan jama’a a lungu da saƙo na jihar Kano domin ƙarfafa Kwankwasiyya.

Kwankwaso, wanda aka ce ya buɗe rijistar mubaya'a a gidansa, ya faɗi hakan ne yayin da yake jawabi ga ƙungiyoyin magoya baya daga ƙananan hukumomi daban-daban da suka kai masa ziyara.

Yayin da yake umartar su da su koma gida su ƙara jawo jama’a cikin tafiyar Kwankwasiyya, tsohon gwamnan ya ce:

Kara karanta wannan

Tuna baya: Yadda Gwamna Abba ya yi alkawarin kin yi wa Kwankwaso butulci

“Wannan shi ne abu mafi muhimmanci a gare ku a yanzu, musamman ganin yadda wasu ke sauya sheƙa.”
Kwankwaso da Abba.
Jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso tare da Gwamna Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature
Source: Facebook

Kwankwaso ya maida raddi ga wasu mutane

Kwankwaso, wanda ake ta jita-jitar yana shirin shiga jam’iyyar ADC, ya tabo masu tsokanarsa, suna cewa ta kare masa a siyasa, kamar yadda Leadership ta rahoto.

“Kar ku damu da wadanda ba su san siyasa ba, wasu suna cewa yara ne mu, idan Allah Ya yarda, masu irin wannan magana za su ga aikin yara yayin da zabe ya zo.

Ya ƙara da cewa: “Mun karɓi kusan ƙungiyoyi 21 daga sassan jihar nan, kuma wasu na tafe. Don haka ku koma gida ku tarbe su.”

Za a iya sayan Kwankwaso da kudi?

A wani labarin, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Injiniya Rabiu Kwankwaso ya ce babu wanda zai iya sayensa da kudi a siyasa.

Kwankwaso ya yi ikirarin cewa shi dan siyasa ne da ba shi da farashi, inda ya bayyana siyasar Kano a matsayin wadda jama’a ke da wayewa.

Kwankwaso ya ce siyasa tana tattare da riba da asara, amma ya jaddada cewa cin amana abu ne da ke janyo fushin jama’a.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262