Rikicin Ribas: Ministan Abuja Ya Debo da Zafi, Ya Kira Gwamna da 'Mara Tarbiyya'

Rikicin Ribas: Ministan Abuja Ya Debo da Zafi, Ya Kira Gwamna da 'Mara Tarbiyya'

  • Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya ci gaba da sukar Gwamna Simi Fubara a rangadin da yake domin yi wa jama'a godiya a Ribas
  • Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas ya bayyana Mai girma Gwamna Siminalayi Fubara a matsayin dan da bai gaji halin ubangidansa ba
  • Ya gode wa shugabannin al'umma da na siyasa a yankin karamar hukumar Asari-Torubisa jajircewa da goyon bayan da suka nuna masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers, Nigeria - Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya soki Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara bisa rashin ci gaba da wasu ayyuka da ya bari.

Mista Wike, tsohon gwamna jihar Ribas, wanda ke takun saka da mai girma gwamna, ya kira Fubara da, "da mara tarbiyya."

Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike yana jawabi a wurin taro Hoto: @Govwike
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa Wike ya faɗi hakan ne yayin wata ziyara ta godiya da ya kai Ƙaramar Hukumar Asari-Toru a Jihar Ribas, wani ɓangare na rangadin da yake yi.

Kara karanta wannan

Hadimin Abba ya fadi abin da ke shirin kora 'yan Kwankwasiyya zuwa jam'iyyar APC

Nyesom Wike ya caccaki gwamnan Ribas

Tsohon gwamnan ya zargi Fubara da soke wasu manyan ayyuka da shirye-shiryen da ya tafi ya bar masa, ciki har da aikin ɗaukar matasa sama da 10,000 aiki.

“Mulki abu ne da ke gudana a jere. Na ɗauki matasan Ribas sama da 10,000 aiki, amma mutumin da muka mika wa mulki ya soke dukkan ayyukan. 'Da mara tarbiyya kenan.
"Nan ne ake gane halayyar ɗan Adam. Na mika mulki, ga inda na tsaya. Ina roƙonku ku tabbatar an ci gaba da wannan shiri domin jihar mu ta zama ɗaya daga cikin jihohin da ake girmamawa a ƙasar nan,” in ji Wike.

Meya sa Wike ya fara zagaye Rivers?

Ministan ya bayyana cewa ya kai wannan ziyara ne domin godiya ga al'ummar karamar hukumar Asari-Toru saboda halacci da goyon bayan da suka nuna masa tsawon shekaru.

“Mun zo ne domin mu gode muku. Kun kasance tare da mu a kowane irin lokaci. Ko da al’amura sun yi wuya, ku kuna kokarin kawo mana nasara.

Kara karanta wannan

Kwanaki bayan munanan hare hare a Neja, manoma sun ci karo da bam a gona

Yanzu da duka muka haɗu muka zama tsintsiya madaurinki ɗaya, lokaci ya yi da za mu koma gida mu kwanta mu yi barci da ido biyu, muna da tabbacin cewa komai yana tafiya daidai."
“Mu ba mutane ne marasa godiya ba. Idan an yi mana alheri, muna dawowa mu ce na gode. Shi ya sa muka zo yau, domin gobe ku san cewa idan kuka goyi bayanmu, ba za mu taɓa mantawa da ku ba.”

- In ji Nyesom Wike.

Wike da Fubara.
Ministan harkokin Abuja, Nyesom Ezenwo Wike da gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubaga Hoto: Nyesom Ezenwo Wike, Sir Siminalayi Fubara
Source: Facebook

Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya kuma bayyana cewa goyon bayan Bola Tinubu a zaɓen 2023 babban kasada ce a wancan lokacin, amma yanzu wannam kasada ta zama alheri.

Ministan ya yaba wa shugabannin siyasa, jam’iyya da magoya bayansa a yankin, yana mai cewa godiya da riƙon amana su ne ginshiƙan siyasa mai ɗorewa, in ji rahoton Punch.

Wike ya zargi Fubara da saba yarjejeniya

A baya, kun ji cewa Ministan abuja, Nyesom Wike, ya zargi Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara, da karya yarjejeniyar da suka yi karkashin Bola Tinubu.

Wike ya bayyana cewa ba da jimawa ba zai fito ya bayyana wa al’ummar Rivers cikakkun bayanan yarjejeniyar da aka cimma a gaban Shugaban kasa.

Ministan ya gargadi Fubara kan makomarsa ta siyasa, yana mai cewa magoya bayansa sun shirya “gyara kuskuren” zaben 2023

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262