'Yan Adawa Sun Tashi Tsaye, PDP Za Ta Gana da Manyan Jagororin ADC, Atiku da Peter Obi
- Jam'iyyar PDP za ta gana da manyan jagororin hadaka, Peter Obi da Atiku Abubakar yayin da shirye-shiryen 2027 ke kara kankama
- Shugaban PDP na yankin Kudu maso Kudu, Emmanuel Ogidi ya ce hakan wani bangare ne na kokarin sake gina tsagin adawa
- PDP mai hamayya na ci gaba da fuskantar rigingimun cikin gida tun bayan zaben 2023, wanda ya kai ga darewarta zuwa gida biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Babbar jam'iyyar adawa ta fara shirya yadda za ta gana da tsohon 'dan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.
Jigon PDP, Emmanuel Ogidi ya ce za a yi wannan ganawa tsakanin jam'iyyar da Atiku, Obi da wasu manyan jagororin adawa domin sake gina babbar jam'iyyar adawa a Najeriya.

Source: Facebook
Ogidi, wanda shi ne shugaban PDP na yankin Kudu maso Kudu, ya bayyana hakan ne a shirin The Morning Brief na gidan talabijin na Channels TV a ranar Laraba.
Jam'iyyar PDP ta fara tuntubar tsofaffin shugabanni
Ya ce PDP ta fara tattaunawa da shugabanni da manyan mutane masu tasiri a ƙasar nan, inda tuni ta gana da tsofaffin shugabannin ƙasa biyu, Olusegun Obasanjo da Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB).
“Mun riga mun gana da tsohon Shugaban Ƙasa Obasanjo da kuma IBB. Wannan duka wani ɓangare ne na nuna wa ’yan Najeriya cewa PDP na nan da ranta kuma tana ci gaba da motsi.
"Na san za ku tambaye ni batun Peter Obi; Eh, shi ma muna da shirin ganawa da shi,” in ji Ogidi.
PDP na shirin ganawa da Atiku da Obi
Ya ƙara da cewa PDP za ta kuma gana da Atiku Abubakar, yana mai cewa jam’iyyar ita ce ainihin fuskar dimokuraɗiyya a Najeriya.
Peter Obi da Atiku Abubakar dai tsofaffin ’yan PDP ne, inda a shekarar 2019 Obi ya yi takarar mataimakin shugaban ƙasa, yayin da Atiku yake matsayin 'dan takarar shugaban ƙasa.
Atiku kuma shi ne ɗan takarar PDP a zaɓen 2023, daga bisani, su biyun suka koma jam’iyyar ADC, dandalin hadakar manyan 'yan adawa a kasar nan.

Source: Facebook
A ranar Talata kuma, mambobin Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) na PDP sun gana da tsohon Shugaban Ƙasa, Dr. Goodluck Jonathan a ofishinsa da ke Maitama, Abuja.
Taron ya samu jagorancin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Tanimu Turaki, tare da sauran manyan ’yan jam’iyyar, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
A halin yanzu, bangarori biyu na iƙirarin shugabancin PDP a matakin ƙasa, biyo bayan taron jam’iyyar da aka gudanar a Ibadan, Jihar Oyo.
Abin da Jonathan ya fadawa PDP
A wani labarin, kun ji cewa shugaban PDP na kasa, Tanimu Turaki (SAN) ya shaida wa manema labarai cewa sun je wurin Jonathan domin gabatar masa da sabon kwamitin NWC na kasa.
Ya ce tsohon Shugaba Jonathan ya tabbatar masu da cewa har yanzu shi cikakken mamba ne mai katin PDP, kuma zai ci gaba da kasancewa mai bada gudummuwa a jam’iyyar.
Turaki ya ce maganganun Jonathan sun ƙarfafa gwiwar jam’iyyar, tare da ba su kwarin gwiwa kan makomar PDP a siyasance.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

