Atiku ko Peter Obi?: ADC Ta Yi Magana kan Wanda Za Ta Ba Tikitin Takara a 2027

Atiku ko Peter Obi?: ADC Ta Yi Magana kan Wanda Za Ta Ba Tikitin Takara a 2027

  • Jam'iyyar ADC ta musanta jita-jitar cewa ta riga ta zabi wanda za ta ba tikitin takarar shugaban kasa a zaben shekara ta 2027 mai zuwa
  • Jita-jita ta karu ne bayan da aka samu yawaitar masu sauya sheka zuwa jamm'iyyar ADC a kwanan nan, ciki har da Peter Obi
  • A halin yanzu, akwai kusoshi a ADC da suka riga suka bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar shugaban kasa, ciki har da Atiku Abubakar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Jam’iyyar ADC ta yi fatali da jita-jitar da ake yaɗawa cewa ta riga ta tsaida ɗan takarar shugaban ƙasa da zai fafata mata a zaɓen 2027.

ADC ta ce bai kamata a fassara kwararar da ’yan siyasa ke yi zuwa jam’iyyar a halin yanzu a matsayin wata yarjejeniya ta sirri kan wanda zai riƙe tutar jam’iyyar ba.

Kara karanta wannan

Babban alkawarin da APC ta yi wa Gwamna Caleb bayan komawarsa jam'iyyar

Jam'iyyar ADC ta ce ba ta tsayar da dan takarar shugaban kasa ba tukunna
Nasir El-Rufai na magana da Peter Obi, tambarin jam'iyyar ADC da Atiku Abubakar yana magana a wajen taro. Hoto: @PeterObi, @atiku
Source: Twitter

Jam'iyyar ADC ba ta tsayar da 'dan takara ba

Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ne ya bayyana hakan a ranar Talata, 6 ga Janairu, 2026, yayin da yake zantawa da Channels TV.

Bolaji Abdullahi ya jaddada cewa kofar jam’iyyar ADC tana buɗe ga kowa, kuma babban burinta shi ne tabbatar da adalci ga dukkan mambobinta ba tare da fifita kowa ba.

Ya bayyana cewa ba a kai ga maganar rarraba mukamai ko tikitin takara na shiyya ba, kuma ba a tsayar da wani ɗan takara a halin yanzu ba.

"Idan lokaci ya yi, jam’iyyar za ta yi amfani da hanyar sulhu don tsaida ɗan takara, amma idan hakan ya gagara, za mu gudanar da zaɓen fitar da gwani na gaskiya da adalci wanda kowa zai aminta da shi."

- Bolaji Abdullahi.

A halin yanzu, akwai wasu jiga-jigan 'yan siyasa a ADC da suka riga suka bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar shugaban kasa, ciki har da Atiku Abubakar da Peter Obi.

Kara karanta wannan

'Babu wani mahaluki': Atiku ya magantu kan janye takarar shugaban kasa a 2027

ADC ta soki gwamnatin Bola Tinubu

Baya ga maganar zaɓen 2027, Bolaji Abdullahi ya soki gwamnati mai ci yanzu kan abin da ya kira tsananin yunwa da rashin tsaro da ’yan Najeriya ke fuskanta wanda ba a taɓa ganin irinsa ba.

Mai magana da yawun jam'iyyar adawa ta ADC, ya kuma zargi gwamnatin da yin biris da halin da talakawa ke ciki yayin da take ƙara haraji.

Haka kuma, ya nuna damuwa kan yadda Najeriya ke rasa tasirinta a idon duniya, inda ya ce a yau muryar Najeriya ta dusashe a duk lokacin da ake tattauna manyan batutuwa na ƙasa da ƙasa kamar yadda aka saba a baya.

Bolaji Abdullahi, ya ce ADC za ta shirya tunkarar zabukan 2026.
Bolaji Abdullahi, sakataren yada labaran jam'iyyar ADC na kasa. Hoto: @BolajiADC
Source: Facebook

ADC za ta shirya tunkarar zabukan 2026

Sakataren ya ƙara da cewa ADC tana shirin tunkarar zaɓukan gwamnoni da za a yi a jihohin Ekiti da Osun, da kuma zaɓen kananan hukumomi na Abuja.

Ya bayyana cewa jam’iyyar za ta kafa wani kwamiti na musamman wanda zai samar da dabarun farfaɗo da tattalin arziƙi don gabatar wa ’yan Najeriya a matsayin mafita.

Kara karanta wannan

Shekaru 7 bayan tsige shi daga shugaban DSS, Lawal Daura zai fito takarar gwamna

A cewarsa, babu wani sauran albishir na cewar 'akwai haske a ƙarshen rami' da zai sa mutane su manta da tsananin duhun da suke ciki a halin yanzu.

ADC: Obasanjo na shirin hada Obi da Kwankwaso

A wani labari, mun ruwaito cewa, ana duba yiwuwar haɗa Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso a tikitin shugabancin ƙasa domin fuskantar Atiku Abubakar a zaben fitar da gwani na ADC.

Rahotanni sun nuna cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo na taka rawa wajen sulhunta bangarorin biyu, yana ganin haɗin kai zai ƙara wa ’yan adawa ƙarfi a 2027.

Duk da cewa Peter Obi ya riga ya shiga ADC, Rabiu Kwankwaso na ci gaba da tattaunawa da shugabannin siyasa, inda ake sa ran zai bayyana matsayinsa nan gaba kaɗan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com