Babban Alkawarin da APC Ta Yi Wa Gwamna Caleb bayan Komawarsa Jam’iyyar
- Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce jam’iyyar za ta daina sukar Gwamna Caleb Mutfwang
- Farfesa Yilwatda ya yi ikirarin cewa APC za ta bai wa Shugaba Bola Tinubu sama da kuri’u miliyan daya a Plateau
- Ya ce APC ta kara karfi a Plateau bayan shigowar manyan ‘yan siyasa, tare da alkawarin cewa babu wanda zai kwace jam’iyyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jos, Plateau - Shugaban jam’iyyar APC ta kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda yayi wa Gwamna Caleb Mutfwang alkawari.
Nentawe Yilwatda ya bayyana cewa jam’iyyar za ta daina sukar Gwamna Caleb na Jihar Plateau a bainar jama’a.

Source: Twitter
Yilwatda ya bayyana hakan ne yayin taron masu ruwa da tsaki na APC na mazabar tarayya ta Pankshin, Kanke da Kanam (PKK) da aka gudanar Pankshin, cewar Daily Trust.
Kur'iun da APC za ta ba Tinubu
Shugaban jam’iyyar ya ce APC na da cikakken tabbacin cewa Plateau za ta ba Bola Tinubu sama da kuri’u miliyan daya a zaben 2027, yana mai danganta hakan da karuwar karfin jam’iyyar da rushewar tsare-tsaren adawa.
A cewarsa, APC ta fi karfi a Plateau yanzu fiye da yadda take a 2023, inda ya jaddada cewa manyan yan siyasar da ke adawa da jam’iyyar a baya sun koma cikinta.
Ya ce:
“Dukkan matsalolin da muka fuskanta a 2023 sun kau. Wadanda suka yi adawa da mu a wancan lokaci yanzu suna tare da mu, ciki har da gwamnan Plateau, Barrista Caleb Muftwang, kwamishinoni, shugabannin kananan hukumomi da sauran masu mukaman siyasa.”

Source: Twitter
2023: Yankin da Tinubu ya fi samun kuri'u
Yilwatda ya bayyana yankin PKK a matsayin tushen APC, yana mai tunatarwa cewa Shugaba Tinubu ya samu mafi yawan kuri’unsa a yankin a zaben shugaban kasa na 2023.
Shugaban APC ya ce jam’iyyar yanzu ta cimma dunkulewa a siyasa, wadda ya kira “yunkuri mai inganci ba tare da rikici ba”.
Ya kara da cewa:
“Idan 2027 ta zo, Shugaba Tinubu zai samu mafi yawan kuri’unsa a nan, duka ta fuskar adadi da kaso. Babu wata mazaba ko rumfar zabe a PKK da ba za mu ci ba."
Yilwatda ya ce karfin APC ya karu sosai bayan shigowar manyan ‘yan siyasa, inda ya bayyana cewa jam’iyyar yanzu ta zama daya a matakin jiha da kasa.
Shugaban APC ya ce dalilin daina sukar gwamna Caleb a bainar jama’a shi ne yanzu jam’iyyar na da damar kai tsaye ta shawarwari da gwamnati.
A cewarsa:
“Ba zan kara sukar gwamnati daga gefe ba. Yanzu ina da dama. Idan gwamnati ta yi kuskure, zan iya kira ko zuwa wajen gwamna mu tattauna yadda za a gyara. Wannan ita ce hanya mafi dacewa wajen gina shugabanci nagari.”
PDP ta fusata bayan sauya shekar gwamna Caleb
An ji cewa jam'iyyar PDP reshen jihar Plateau ta nuna rashin jin dadinta bayan sauya shekar Gwamna Caleb Mutfwang zuwa APC.
Sakataren yada labarai na PDP a Plateau, Hon. Choji Dalyop, ya bayyana cewa gwamnan bai tuntube su ba kafin ya sauya sheka.
Ya yi kira ga mutanen jihar Plateau da ka da su sake ba gwamnan kuri'unsu domin ya ci amanar yardar da suka yi masa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


