Shekarau Ya Tsoma Baki kan Shirin Abba na Komawa APC, Ya Tona Wa Kwankwaso Asiri
- Malam Ibrahim Shekarau ya soki wasu daga cikin kalaman Ibrahim Kwankwaso game da rade-radin sauya shekar Gwamnan Kano zuwa APC
- Shekarau, tsohon gwamnan Kano ya ce Kwankwaso ba shi da hujjar cewa Abba Kabir Yusuf ya ajiye kujerar gwamna kafin ya bar jam'iyyar NNPP
- Ya kuma tunawa jagoran NNPP na kasa abin da ya yi lokacin yana gwamna a inuwar jam'iyyar PDP da kuma yaudarar da ya masa a baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya tsoma baki kan dambarwar da ke faruwa a NNPP bayan bullar jita-jitar Gwamma Abba Kabir Yusuf zai koma APC.
Shekarau ya ce bai kamata a zargi Gwamna Abba Kabir Yusuf da cin amana ko butulci ba dangane da rade-radin da ke yawo na yiwuwar ficewarsa daga NNPP.

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa NNPP da tafiyar Kwankwasiyya sun afka cikin rikici bayan bullar rahotannin da ke cewa gwamnan Kano na shirin komawa APC mai mulki.
A wata hira da ya yi da kafar DCL Hausa, Shekarau ya ce sauya sheka a siyasa ra'ayi ne na mutum, wadda ake yi bisa la’akari da yanayi da kuma shawarwari.
Malam Shekarau ya soki kalaman Kwankwaso
Ya soki kalaman Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da ya ce ya kamata Gwamna Abba ya ajiye mukaminsa kafin ya bar NNPP.
Malam Shekarau ya tunawa Kwankwaso yadda ya dauko kujerar gwamnan Kano ya tafi da ita APC kafin zaben 2015.

Kara karanta wannan
Dalilanmu na son Kwankwaso ya ja Abba zuwa APC inji Hadimin Gwamna Alhajiji Nagoda
“Na saurari jawabin dan uwana tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso. Akwai wasu gabobi guda biyu, ko dai Kwankwaso ya manta da abin da ya faru a baya, ko kuma ya dauka mutane sun manta.
"Gaba ta farko, na ji a jawaban Kwankwaso yana cewa idan Abba zai yi gaskiya, ya ajiye musu kujerarsu ta gwamna sannan ya tafi APC, Allah Sarki dadin gobe saurin zuwa.
"Lokacin da Kwankwaso yake gwamnan Kano a inuwar PDP, haka ya kwasa ya tafi da wannan kujera zuwa APC, me yasa bai ajiye wa PDP kujerarta ba? Dan haka ba shi da hujjar cewa Abba ya ajiyewa NNPP kujerara, shi ma haka ya yi."
- In ji Malam Shekarau.
Shekarau ya tuna abin da Kwankwaso ya masa
Tsohon gwamnan ya kara da cewa gaba ta biyu ita ce kalaman da Kwankwaso ya yi cewa duk jam'iyyar da zai koma sai an tabbatar masa da makomar magoya bayansa.
Shekarau ya kara da cewa:
"Haka na ji yana cewa shi kansa sai an tabbatar masa za a ba shi takarar shugaban kasa ko mataimaki kafin ya tafi wata jam'iyya, nan ma zan masa tuni, sanda muka shiga NNPP mun zauna ni da shi.
"A rubuce na ba shi cewa ga yadda za a raba kujerun takara tsakanin mutanensa da na mu, amma a nan falon gidana na Kano, ya ce a kafa kwamitin mutum takwas da za su yi wannan aiki.
"Daga karshe ni na kaddamar da kwamitin karkashin shi Abba Kabir tunda shi ne dan takarar gwamna, amma haka suka fitar da sunayen yan takara, idan banda sunana babu sunan kowa daga cikin mutanen mu.

Source: Facebook
Abin da ya sa ake son Kwankwaso ya koma APC
A wani rahoton, kun ji cewa hadimin gwamnan Kano, Alhajiji Nagoda ya bayyana dalilin da ya sa suke kiran Rabi'u Musa Kwankwaso ya jagoranci Abba Kabir Yusuf zuwa APC.
Alhaji Nagoda ya ce suna son Madugu ya zo a yi tafiyar da shi ne saboda zai fi dacewa Kwankwaso ya kai Abba APC, domin shi ne ubangidansa a siyasa.
Ya bayyana cewa suna ganin komawa APC zai kawo ƙarshen rikice-rikicen siyasa, tare da samar da mafita da sauƙin al’amura a Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

