Yadda Kwankwaso da Abba Kabir Ke Shirin Ɓaɓewa bayan Shafe Shekaru 40 tare
- Rikici ya barke tsakanin Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da mai gidansa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso saboda rade-radin raba gari a Kano
- Lamarin ya jefa NNPP a Kano cikin ruɗani, inda jam’iyyar ta kasu gida-gida, tare da sake tayar maganganu kan siyasar ubangida a Najeriya
- Majalisar dokoki da shugabannin kananan hukumomi sun karkata ga bangaren gwamna, lamarin da ake ganin ya rage karfin Kwankwaso
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - An shiga sabon yanayi na ruɗani a siyasar Jihar Kano bayan da aka gano cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na shirin barin tafiyar mai gidansa, Rabiu Kwankwaso.
Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya tsananta ne bayan jita-jitar cewa Gwamna Abba Yusuf na shirin ficewa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.

Source: Twitter
Majiyoyi daga jaridar Punch suka ce alakar Abba Kabir da Kwankwaso ta dade wacce ake ganin ta kai shekaru 40.
Jita-jitar Abba zai koma APC ya bar baya da kura saboda an ce matakin bai samu amincewar Kwankwaso ba abin da ya sake rikita lamura.
Yadda dangantaka mai tarihi ta raunana
Dangantakar Yusuf da Kwankwaso ta samo asali ne tun shekarun 1980, lokacin da suka yi aiki tare a hukumar WRECA a matsayin injiniyoyi.
Daga nan ne alakar ta rikide zuwa siyasa, zumunci da kuma hada karfi wurin kafa gwamnati a Kano.
Abba Yusuf, wanda aka fi sani da “Abba PA”, ya kasance mataimaki na kut-da-kut ga Kwankwaso tsawon shekaru, har ya zama surukinsa.
Ya rike mukamai daban-daban ciki har da sakatarensa na musamman da Kwamishinan Ayyuka, kafin daga bisani ya zama gwamna a 2023 da goyon bayan Kwankwaso karkashin NNPP.

Source: Twitter
Farkon rabuwar kai tsakanin Abba, Kwankwaso
Sai dai majiyoyi sun shaida cewa rikicin Kwankwaso da Abba ya samo asali ne daga neman iko, biyayya da ‘yancin shugabanci wanda ke kara dagula lamura.
Wasu rahotanni suka ce Kwankwaso na son ci gaba da tasiri a mulkin Abba Kabir, yayin da gwamnan ke neman ‘yancin kansa.
Rikicin ya bayyana fili ne bayan da aka tabbatar da shirin gwamnan na komawa APC, matakin da aka ce Kwankwaso ya nuna fushinsa a kai saboda rashin neman izininsa, cewar Daily Trust.
Rikici ne na siyasa, ba na kashin kai ba
Majiyoyi daga bangarorin biyu sun ce rigimar ta siyasa ce, ba ta kashin kai ba. Sun bayyana cewa Kwankwaso ya fara jin cewa gwamnan bai nuna irin biyayyar da yake tsammani ba, musamman wajen naɗe-naɗen mukamai da yanke muhimman hukunci.
Wasu sun ce Kwankwaso ya kasance yana da tasiri har a cikin naɗin kwamishinoni da shugabannin hukumomi, lamarin da ya janyo rashin jituwa daga baya.
An ce Kwankwaso ya fara tsara hanyoyin hana gwamna Abba Kabir tikitin wa’adi na biyu, tare da shirin goyon bayan mataimakin gwamna Gwarzo.
Sai dai bayan gano cewa ‘yan majalisa da shugabannin kananan hukumomi sun koma gefen gwamnan, an fahimci cewa tsige gwamnan ba zai yiwu ba.
An ce Abba Kabir na da goyon bayan ‘yan majalisa 33, lamarin da ya kare shi daga duk wani yunkurin tsige shi, cewar Premium Times.

Source: Facebook
Jam'iyyar NNPP ta kara ruguje wa a Kano
Majiyoyi sun ce lamarin ya kara dagula halin da NNPP ke ciki a Kano, inda jam’iyyar ta kasu gida-gida.
An kori shugaban jam’iyyar jihar, sannan aka kafa sababbin shugabanni masu biyayya ga Yusuf.
A martani, bangaren NNPP na Kwankwaso ya rushe dukkan shugabannin jam’iyyar daga matakin jiha zuwa gundumomi, tare da alkawarin kafa kwamitocin rikon kwarya.
Daga bisani, Babbar kotun Kano ta ayyana rusa shugabannin jam'iyyar NNPP a matakin jiha, kananan hukumomi da mazabu a matsayin ba bisa ka’ida ba.
Kotun ta kuma hana kwamitin gudanarwa na kasa na jam’iyyar daukar wani sabon mataki kan shugabancin NNPP a Kano har sai an yanke hukunci.
Tarihin rikicin siyasa a Kano
Masana siyasa sun ce wannan rikici ba sabon abu ba ne a Kano, tun daga zamanin Aminu Kano da Abubakar Rimi ake fama da rikicin siyasa.
Sannan har zuwa rikicin Kwankwaso da Abdullahi Ganduje, da kuma Ibrahim Shekarau da magoya bayansa, Kano ta saba da rikice-rikicen siyasa.

Kara karanta wannan
Tirkashi: Kwankwaso ya bi hanyoyi 2, ya yi yunkurin tsige Abba daga kujerar gwamnan Kano
Me zai biyo baya?
Yayin da bangarorin biyu ke gujewa fito-na-fito a fili, masana na ganin cewa sauya shekar Abba zuwa APC za ta sake fasalta siyasar Kano gabanin 2027, tare da kawo karshen dogon tasirin Kwankwasiyya a jihar.
Majiyoyi sun ce da zarar an sanar da sauya shekar a hukumance, duk tsarin NNPP a Kano na iya rushewa zuwa APC, abin da zai girgiza siyasar Arewa gaba ɗaya.
Kwankwaso ya fadi bambancinsa da sauran 'yan siyasa
Kun ji cewa tsohon ɗan takarar Shugaban Ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce shi ɗan siyasa ne da ba a saye shi da kuɗi.
Ya bayyana siyasar Kano a matsayin wadda jama’a ke da wayewa kuma ba sa yarda da cin hanci sai dai ra'ayin kansu.
Yayin da ake batun sauya sheƙar Gwamnan Kano, Kwankwaso ya gargadi ’yan siyasa da masu zaɓe kan amincewa da ribar gajeren lokaci.
Asali: Legit.ng


