Dalilanmu na Son Kwankwaso Ya Ja Abba zuwa APC Inji Hadimin Gwamna Alhajiji Nagoda
- Hadimin Gwamnan Kano, Alhajiji Nagoda ya bayyana dalilin da ya sa suke kiran Rabi'u Musa Kwankwaso ya jagoranci Abba Kabir Yusuf zuwa APC
- Alhajiji Nagoda ya bayyana yadda zamansu a NNPP ke jawo matsalolin rashin bin umarnin Gwamna ga jami'an tsaro da ke aiki a jihar
- A ganin hadimin gwamnan, sauya sheka zuwa APC za ta kawo gyare-gyare a harkokin tsaro a jihar tare da kara kawo ci gaba mai dorewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Hadimin Gwamnan Kano a kan harkokin yaɗa labarai, Alhaji Nagoda, ya bayyana dalilan da suka sa suke kira ga Rabi’u Musa Kwankwaso da ya jagoranci Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa APC.
Alhaji Nagoda ya yi wannan bayani ne duk da cewa Kwankwaso ya nesanta kansa daga duk wani yunƙuri na ja shi zuwa jam’iyya mai mulki a Najeriya.

Source: Facebook
A wata hira da aka wallafa a shafin Facebook na Iconic Times24, Alhaji Nagoda ya ce zai fi dacewa Kwankwaso ya kai Abba APC, domin shi ne ubangidansa a siyasa.
Hadimin gwamna na addu’ar shigar Kwankwaso APC
Hadimin Gwamnan Kano ya ƙara da cewa sun ga ya zama dole su nemi sauya sheƙa zuwa APC saboda halin da Jihar Kano ke ciki.
A kalaman Alhaji Nagoda:
“Mu magoya baya, mu ne muke kiransu saboda halin da jihar Kano ta shiga na waɗannan abokan zamanmu. Sharri da makirci, da kulle-kullen da suke kullawa jihar Kano don ta shiga wani irin yanayi."
"Muka ce to, muna kira ga shi mai girma jagora da Mai girma gwamna, mu haɗu mu tafi, a ɗebi dukkanin magoya baya, a koma APC.”
“Domin wannan zaman zulumi da tararrabi da ake ciki, har ma jam’iyyarmu aka ce ba tamu ba ce, wai ta wani ce Boniface. An kai ƙara kotu ta farko ta ce ba tamu ba ce, kotu ta biyu ma ta ce ba tamu ba ce.”

Kara karanta wannan
Gwamna Abba ya kafe kan komawa APC, an ji adadin jiga jigan da za su tafi tare da shi
Ya bayyana cewa suna ganin komawa APC zai kawo ƙarshen rikice-rikicen siyasa, tare da samar da mafita da sauƙin al’amura a Kano.
Nagoda ya yi wa Kwankwaso addu’a
A cewar Alhaji Nagoda, ya kamata Kwankwaso ya jagoranci Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa APC saboda shi ne ubangidansa a siyasa.

Source: Twitter
Dangane da furucin Kwankwaso cewa ba shi da alaka da APC, Nagoda ya ce:
“Mu dai muna ta addu’a, Allah Ya daidaita tsakani, Allah kuma Ya sa a zo a haɗu a kama hanya a tafi domin tseratar da rayukan jama’a da dukiyoyinsu.”
“Kowa ya sani Gwamna shi ne shugaban tsaro a jiharsa. Bai kamata a ce gwamna yana ba ‘yan sanda ko wasu jami’an tsaro umarni, su ce a’a ba umarninsa suke jira ba, umarnin wani da ba ya cikin jihar nan.”
“Kana gani, shigowa za mu yi ta ƙofar Nassarawa a garin nan, amma wasu marasa kunya su tsaya suna jifa a ƙofar gida. Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ya je shigowa, aka samu wasu marasa ɗa’a har suka yi jifa wajen motarsa.”
Ya ce suna da yaƙinin cewa shiga APC zai kawo ƙarshen rikicin masarauta, inganta tsaro, da kuma dawo da zaman lafiya a Jihar Kano.
Tinubu ya aika sako ga Gwamnan Kano
A baya, kun samu labarin cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
Shugaba Tinubu ya aike da saƙon taya murnar ne yayin da gwamnan ya cika shekaru 63 a duniya a ranar 5 ga Janairu, 2026, inda ya yabawa jagorancinsa da ƙoƙarinsa a kan al'umma.
A cikin wata sanarwa da mai ba Shugaban Ƙasa shawara a kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga ya fitar a yammacin Lahadi, Tinubu ya kwatanta Abba da Aminu Kano.
Asali: Legit.ng

