Gwamna Abdulrazaq Ya Gano Jam'iyyar da Ta Dace da Mulkin Najeriya
- Mai girma Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ya yi tsokaci kan jam'iyyar da ta dace da mulkin Najeriya
- Shugaban na kungiyar gwamnonin Najeriya ya bayyana cewa jam'iyyar APC ita ce mafi dacewa da jan ragamar al'amuran Najeriya
- Gwamna Abdulrazaq ya nuna cewa APC ce kadai jam'iyyar da ta kawo ci gaba a matakin kasa, jihohi da kananan hukumomi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kwara - Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bayyana cewa jam’iyyar APC ita ce jam’iyya mafi dacewa da tafiyar da al’amuran Najeriya.
Gwamna Abdulrazaq ya bayyana APC a matsayin wata babbar kungiyar siyasa ta musamman, wadda ake ganin ita ce jam’iyya mafi girma a Afirka baki ɗaya.

Source: Facebook
Jaridar The Nation ta ce gwamnan ya yi wannan jawabi ne yayin kaddamar da taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki na APC a jihar, tare da fara rajistar yanar gizo da tantance mambobin jam’iyyar.
Gwamna Abdulrazaq ya yi rajistar APC
Gwamna AbdulRazaq, wanda aka rubuta sunansa a matsayin mutum na farko da ya yi rajista a jam’iyyar a Kwara, ya ce an shirya wannan aikin ne domin Karfafa APC tare da samun sahihin adadin mambobinta don kyakkyawan shiri da tsari.
Ya ce duk wanda ke da sha’awar shiga jam’iyyar ya kamata a ba shi dama, yana mai gargadin cewa kada a ware ko a hana kowa shiga rajistar.
Gwamnan ya kuma sanar da cewa duk masu niyyar tsayawa takarar kujerun siyasa a 2027 za su samu dama iri daya, ba tare da nuna wariya ba.
Gwamna ya ba masu neman takara shawara
Abdulrahman Abdulrazaq wanda kuma shi ne shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), ya shawarci duk masu neman yin takara a jihar da su nemi goyon bayan mambobin jam’iyyar tare da jawo sababbin mambobi, jaridar Vanguard ta kawo labarin.
“Yana da matuƙar muhimmanci mu san adadin mambobin wannan kungiya ta musamman (APC), wadda ake ganin ita ce jam’iyya mafi girma a Afirka."
"Ita ce kaɗai jam’iyyar da ta bunkasa Najeriya da dukkan jihohinta, har ma da kananan hukumomi."
- Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq
Jiga-jigan jam'iyyar APC sun halarci taro
Manyan jiga-jigan jam’iyyar daga sassa daban-daban na jihar sun halarci taron masu ruwa da tsaki da kuma kaddamar da aikin rajistar da sake tantance mambobin APC.
“Muna son sanin adadinmu domin mu iya tsara tsare-tsare, neman goyon baya, da kare kanmu yadda ya kamata, tare da karfafa kanmu ba tare da barin kowa a baya ba."
“Ga waɗanda aka ɗora wa wannan aiki, kada ku hana kowa. Muna bukatar dukkan mambobin da za mu iya samu. Ku tabbatar kun yi rajistar ba mambobinmu kaɗai ba, har da neman sababbin mambobi."
“Wannan dama ce ta jawo sababbin mambobi. Kun ga ayyukan da aka yi daga matakin tarayya zuwa jiha da kananan hukumomi. Ku yi amfani da su wajen tallata jam’iyyar domin mu faɗaɗa ta fiye da inda muke a baya.”
- Gwamna Abdulrahman AbdulRazaq

Source: Facebook
Gwamna Abdulrazaq ya ce gwamnatinsa ta aiwatar da ayyuka masu yawa a dukkan fannoni, wanda hakan ya sa jihar Kwara ta samu ci gaba fiye da kowane lokaci a tarihinta.
PDP ta soki Gwamna Abdulrazaq
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP mai adawa a Kwara ta caccaki Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq.
Jam'iyyar PDP mai hamayya a jihar da Najeriya ta soki Gwamna Abdulrazaq kan rashin mayar da martani bayan fashewar da ta auku a Offa.
Hakazalika, jam'iyyar PDP ta ce shiru da gwamnatin ta yi ya bar mazauna Offa cikin damuwa, tsoro da neman karin bayani kan abin da ya faru.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


