Ana Batun Sauya Shekar Gwamna Abba, Kwankwaso Ya Aika Sako ga Masu Raina NNPP

Ana Batun Sauya Shekar Gwamna Abba, Kwankwaso Ya Aika Sako ga Masu Raina NNPP

  • Madugun Kwankwasiyya kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya aika da sakon gargadi ga 'yan adawa
  • Rabiu Musa Kwankwaso ya ja kunnen 'yan adawar siyasa da su guji raina jam'iyyar NNPP, inda ya ce za su ga abin mamaki
  • Hakazalika, wani jigo a jam'iyyar NNPP, ya yi magana kan batun sauya shekar tsohon gwamnan na Kano zuwa ADC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Tsohon ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ja kunnen abokan adawa.

Kwankwaso ya gargadi abokan adawar siyasa da ke raina jam’iyyar da su shirya ganin abin mamaki a zaɓen shekarar 2027.

Kwankwaso ya ja kunnen masu raina jam'iyyar NNPP
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na jawabi a wajen taro Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ce Kwankwaso ya yi wannan gargaɗi ne yayin da yake jawabi ga magoya bayansa a gidansa da ke Miller Road, a birnin Kano.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Yadda Gwamna Abba ya yi alkawarin kin yi wa Kwankwaso butulci

Me Rabiu Kwankwaso ya ce kan NNPP?

Kwankwaso ya bayyana cewa NNPP za ta ba waɗanda suke ganin jam’iyyar ta mutu mamaki ta hanyar sakamakon zaɓen 2027.

Ya ce ana raina jam’iyyar ne daga wasu mutane da, a cewarsa, ba su fahimci yadda siyasar Najeriya ke gudana ba.

“Mutane da yawa da ba su san siyasa ba suna raina mu. Wasu ma har suna cewa mu yara ne. Amma za mu ba su mamaki a zaɓe da sakamakon da za su gani."

- Rabiu Musa Kwankwaso

Kwankwaso ya ba magoya baya tabbaci

Tsohon gwamnan na jihar Kano wanda ya yi wa’adi biyu ya tabbatar wa magoya bayansa cewa NNPP na nan daram kuma tana da karfi, jaridar Leadership ta kawo labarin.

Kwankwaso ya yi kira ga magoya bayan nasa da su ci gaba da jajircewa, nutsuwa da ƙwazo yayin da ake tunkarar zaɓubbukan gaba.

Batun sauya shekar Kwankwaso zuwa ADC

A gefe guda kuma, wani jigo a NNPP, Buba Galadima, ya musanta jita-jitar da ke cewa tsohon ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Rabiu Musa Kwankwaso, na shirin barin NNPP.

Kara karanta wannan

Dalilanmu na son Kwankwaso ya ja Abba zuwa APC inji Hadimin Gwamna Alhajiji Nagoda

Kwankwaso zai ci gaba da zama a jam'iyyar NNPP
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Buba Galadima ya yi wannan bayani ne a martani ga rahotannin da ke cewa Kwankwaso na shirin komawa jam’iyyar ADC, sakamakon rikice-rikicen siyasa da ke faruwa a NNPP, musamman a jihar Kano.

“Shi (Kwankwaso) har yanzu shi ne shugaban NNPP. Bai fice daga jam’iyyar ba. Don haka babu yadda za a yi ya koma wata jam’iyya.”

- Buba Galadima

Duk da haka, Buba Galadima ya ki yin tsokaci kan jita-jitar da ke yawo game da shirin gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, na sauya sheƙa daga jam’iyyar.

Kwankwaso ya fadi sharadin ficewa daga NNPP

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi magana kan sauya sheka daga NNPP zuwa wata jam'iyya.

Kwankwaso ya ce zai yi tunanin sauya jam’iyya ne kawai idan aka ba shi tikitin shugaban ƙasa ko mataimaki a 2027.

Tsohon dan takarar shugaban kasar ya bayyana cewa magoya bayansa a faɗin ƙasa ba za su amince da sauya sheƙarsa ba sai idan hakan ya ba shi manyan muƙamai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng