Tsohon Gwamna Ya Yi Amai Ya Lashe, Ya Sauya Sheka daga PDP zuwa Jam'iyyar APC

Tsohon Gwamna Ya Yi Amai Ya Lashe, Ya Sauya Sheka daga PDP zuwa Jam'iyyar APC

  • Sanata Theodore Orji ya yi amai ya lashe watanni kalilan bayan ya aanar da cewa ya jingine siyasa gaba daya a rayuwarsa
  • Tsohon gwamnan na jihar Abia ya sanar da dawowa siyasa gadan-gadan, tare da bayyana ficewarsa daga PDP zuwa jam'iyyar APC
  • Masana da masu sharhi kan harkokin siyasa sun ce sauya shekar Sanata Kalu na iya zama farkon babin sauya akalar siyasa a Abia

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abia, Nigeria - Tsohon gwamnan jihar Abia da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya, Sanata Theodore Orji, ya fice daga Jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulkin Najeriya.

A watannin da suke shige dai Sanata Orji, wanda ya wakilci Abia ta Tsakiya a Majalisar Dattawa daga shekarar 2015 zuwa 2023, ya sanar da jingine siyasa gaba daya.

Kara karanta wannan

PDP ta yi rashi, tsohon sanata ya fice daga jam'iyyar bayan shekara 20

Sanata Theodore Orji.
Tsohon gwamnan jihar Abia, Sanata Theodore Orji Hoto: Theodore Orji
Source: Facebook

Sai dai a wancan lokaci, tsohon gwamnan bai bayyana ficewarsa daga PDP a hukumance ba, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Yadda 'dan Sanata Orji ya fara shiga APC

Haka kuma 'dansa, tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Abia, Rt. Hon. Chinedum Enyinnaya Orji, ya riga ya fice daga PDP tun da farko sakamakon rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyar.

Masu nazari da sharhi kan harkokin siyasa sun fassara ficewar ɗan tsohon gwamnan a wancan lokaci a matsayin alamar da ke nuna mahaifinsa ma zai iya sauya sheka nan gaba.

Kamar yadda aka yi hasashe, tsohon gwamnan Abia, ya yi amai ya lashe game da batun jingine siyasa a rayuwarsa, ya sanar da sauya sheka daga PDP zuwa APC mai mu'kin kasa, matakin da masana siyasa ke cewa an dade ana tsammani.

Tsohon gwamna ya bi sahun 'dansa zuwa APC

Masu lura da sharhi kan al’amuran siyasa sun bayyana cewa ficewar Sanata Orji ta kara raunana PDP a Jihar Abia, la’akari da irin tasirinsa da kuma rawar da yake takawa.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya dage lokacin komawa jam'iyyar APC, an ji dalili

Ana ganin cewa tsohon gwamnan ya na ɗaya daga cikin manyan ginshikan jam’iyyar PDP masu tallafa mata da dukiya a jihar Abia, kuma komawarsa APC na iya rusa tsarinta gaba daya.

Da yake tabbatar da wannan sauyin sheka, mai ba tsohon gwamnan shawara kan harkokin yada labarai, Mista Ifeanyi Umere, ya ce maigidansa ya yanke wannan shawara ne bisa ra'ayin kansa.

Tutar APC.
Tutar jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Hoto: @OfficialAPCNig
Source: Getty Images

Wasu masu ruwa da tsaki sun yi maraba da abin da suka kira ci gaban APC da karfafa taagin adawar siyasa a jihar Abia, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Sai dai wasu na ganin sauya shekar Sanata Orji babban abin damuwa ne domin ya na iya ruguza tsarin PDP da kuma yiwuwar dawo da karfinta a siyasar Jihar Abia.

Sanata Kalu ya shirya kwato Abia a 2027

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Orji Kalu ya sha alwashin ganin jam'iyyar APC ta kwace mulkin jihar Abia a zaben shekarar 2027 da ke tafe.

Tsohon gwamnan Abia ya ce zai yi duk mai yiwuwa domin APC ta kwace mulki daga jam’iyyar LP mai rike da madafun iko a jihar Abia.

Kalu ya ce zai mara wa Shugaba Bola Tinubu da dan takarar gwamna na APC baya, yana mai jaddada cewa zai sa zuciyarsa gaba daya a yakin neman nasara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262