Tikitin ADC: Obasanjo na Shirin Hada Obi da Kwankwaso Su Fafata da Atiku

Tikitin ADC: Obasanjo na Shirin Hada Obi da Kwankwaso Su Fafata da Atiku

  • Ana ta hasashen cewa ana duba yiwuwar haɗa Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso a tikitin shugabancin ƙasa domin fuskantar Atiku Abubakar a zaben fitar da gwani na ADC
  • Rahotanni sun nuna cewa tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo na taka rawa wajen sulhunta bangarorin biyu, yana ganin haɗin kai zai ƙara wa ’yan adawa ƙarfi a 2027
  • Duk da cewa Peter Obi ya riga ya shiga ADC, Rabiu Kwankwaso na ci gaba da tattaunawa da shugabannin siyasa, inda ake sa ran zai bayyana matsayinsa nan gaba kaɗan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Alamun siyasa sun nuna cewa ana sake duba yiwuwar haɗa tsofaffin ’yan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso su yi takara tare a zaɓen 2027 karkashin jam’iyyar ADC.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya tara 'yan Kwankwasiyya a;hali Abba na shirin hada kai da Ganduje a APC

Rahotanni sun ce ana sa ran cewa Obi da Kwankwaso za su fafata da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar yayin neman tikitin shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC.

Peter Obi, Atiku Abubakar, Rabiu Musa Kwankwaso
Fuskokin jiga-jigan 'yan adawa a siyasar Najeriya. Hoto: Peter Obi|Rabiu Musa Kwankwaso|Atiku Abubakar
Source: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa sabon yunƙuri na zuwa ne bayan gazawar yarjejeniyar haɗin gwiwa da aka yi ƙoƙarin cimmawa kafin zaɓen 2023, inda rashin jituwa kan wanda zai zama ɗan takara da mataimaki ya tarwatsa tattaunawar.

Dalilin neman hada Obi da Kwanwkaso

A zaɓen 2023, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso sun samu kuri'u da dama a yankuna daban-daban a fadin Najeriya da suka nemi mulkin Najeriya a LP da NNPP.

Peter Obi ya samu ƙuri’u sama da miliyan 6 kuma ya yi nasara a jihohi da yawa, ciki har da Legas.

A nasa ɓangaren, Kwankwaso ya yi nasara sosai a jihar Kano, inda ya tabbatar da tasirinsa a Najeriya ta hanyar tafiyar Kwankwasiyya.

Rahotanni sun nuna cewa masu ruwa da tsaki na ganin haɗa ƙarfinsu zai iya ba ’yan adawa damar kalubalantar Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Obasanjo na son hada Obi da Kwankwaso

Kara karanta wannan

'Shugaba Bola Tinubu zai sanya wa Najeriya sabon suna'

Jaridar Legit ta ruwaito cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ne ke jagorantar sabon yunƙurin hada-kan Obi da Kwankwaso.

Wasu majiyoyi sun ce Olusegun Obasanjo ya gamsar da Kwankwaso ya amince ya zama mataimakin Obi a tikitin shugaban ƙasa a ADC.

An ce Kwankwaso ya gana da Obasanjo a Abeokuta, inda aka shawarce shi da ya shiga ADC domin ƙarfafa haɗin gwiwar 'yan adawa.

Atiku Abubakar, Olusegun Obasanjo
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo da Atiku Abubakar.Hoto: Paul O Ibe.
Source: Twitter

Wasu rahotanni sun kuma ambaci cewa tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida ya ba da irin wannan shawara, duk da bai yi batun wanda zai zama mataimakin shugaban ƙasa ba.

Majiyoyi sun bayyana cewa manufar wannan shiri ita ce a haɗa ƙarfin Obi da Kwankwaso domin fuskantar Atiku a zaɓen fidda gwani na ADC, ganin cewa Atiku na da ƙarfi sosai a cikin jam’iyyar.

Kwankwaso ya tara 'yan Kwankwasiyya

A wani labarin, mun kawo muku cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya tara magoya bayan tafiyar Kwankwasiyya a jihar Kano.

Hadimin tsohon gwamnan ya bayyana cewa magoya bayan NNPP daga dukkan kananan hukumomin Kano ne suka gana da Kwankwaso.

Hakan na zuwa ne yayin da ake jita-jitar cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf na shirin fita daga NNPP zuwa APC mai mulki a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng