An Dakatar da Shugaban Jam'iyyar PDP da Aka Gano Yana biyayya ga ministan Abuja
- Jam’iyyar PDP a Rivers ta dakatar da Robinson Ewor bayan ya zargi Gwamna Sim Fubara da yaudarar jam’iyyar kafin ya fice zuwa APC
- Sabon shugaban riko Ogbam Ojimah ya jaddada cewa an riga an kori Nyesom Wike daga PDP don haka ba shi da wani tasiri a jam'iyyar
- Jam'iyyar ta nada sababbin shugabannin riko tare da jaddada biyayyarsu ga Kabiru Turaki yayin da suka bayyana shirin na tunkarar 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Rivers - Rikicin siyasar Rivers ya ɗauki sabon salo inda PDP ta dakatar da shugaban riƙo na jam'iyyar a matakin jiha, Robinson Ewor.
An dakatar da shugaban jam'iyyar PDP, Robinson Ewor ne bayan ya fito fili ya bayyana goyon bayansa ga Ministan Abuja, Nyesom Wike.

Source: UGC
Zarge-zargen shugaban PDP a jihar Rivers
Mista Ewor ya zargi Gwamna Siminalayi Fubara da yaudarar shugabannin jam’iyyar da magoya baya yayin takaddamar siyasar da ta dabaibaye jihar, in ji rahoton Daily Trust.
Dakataccen shugaban PDP ya kuma ce Gwamna Fubara ya yi basaja kafin daga baya ya fice zuwa jam'iyyar APC a farkon watan Disamba 2025.
Ewor ya bayyana wa manema labarai a Fatakwal cewa Fubara ya jefa shugabannin jam'iyyar "cikin tsakiyar teku" ba tare da kariya ba bayan ya gina musu tunanin cewa zai iya ƙwace ikon siyasar jihar daga hannun Wike.
PDP ta jaddada korar Wike daga jam'iyyar
Sai dai, sakataren kwamitin riƙo na jam'iyyar a jihar, Mista Ogbam Ojimah, wanda yanzu ya karɓi ragamar shugabancin, ya bayyana cewa matakin Ewor na iya tarfa wa jam'iyyar kura, don haka aka dakatar da shi daga matsayinsa da kuma mambancin jam'iyyar baki ɗaya.
A yayin wani taron gaggawa da kwamitin riƙo na jihar ya gudanar a ranar Asabar, sabon shugaban, Chief Ogbam Ojimah, ya jaddada cewa Nyesom Wike ya riga ya zama korarre daga jam'iyyar PDP, don haka ba shi da ikon tsoma baki a cikin al'amuranta.
Ya bayyana cewa duk wani tattaunawa ko iƙirari da Robinson Ewor ya yi a madadin jam'iyyar ba ya wakiltar matsayar PDP a jihar Rivers, kuma sun riga sun janye jiki daga kalaman sa.

Source: Original
Shirin PDP na tunkarar zabukan 2027
Jam'iyyar ta kuma sanar da naɗa Dr. Baribefu Fidunko a matsayin mukaddashin sakataren jam'iyyar a jihar kamar yadda rahoton jaridar Vanguard ta rahoto.
Ojimah ya jaddada cewa PDP a Rivers tana ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Dr. Kabiru Turaki, kuma babban burinsu shi ne sake fasalin jam'iyyar domin tunkarar zaɓuka masu zuwa.
Ya gargaɗi jama'a da su daina hulɗa da Ewor a matsayin shugaban jam'iyyar, yana mai cewa matakinsa na poyon bayan Wike ya yi daidai da murabus daga muƙaminsa.
PDP ta kori Wike daga jam'iyyar
A wani labari, mun ruwaito cewa, PDP mai adawa ta yi ta maza a taronta da aka gudanar a jihar Oyo inda ta sallami wasu daga cikin jiga-jiganta.
Daga cikin wadanda jam'iyyar ta tabbatar da korarsu akwai ministan Abuja, Nyesom Wike, Ayodele Fayose da ta zarga da kawo mata cikas.
Sai dai tsagin Wike ya yi ƙoƙarin dakatar da taron ta hanyar kotu, amma PDP ta samu hukuncin kotun Oyo da ya ba ta damar gudanar da taron .
Asali: Legit.ng

