Gwamna Abba Ya Dage Lokacin Komawa Jam'iyyar APC, an Ji Dalili

Gwamna Abba Ya Dage Lokacin Komawa Jam'iyyar APC, an Ji Dalili

  • An samu sauyi kan lokacin da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano zai sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa APC
  • Tun da farko an tsara cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf zai tsallaka zuwa jam'iyyar APC a ranar Litinin, 5 ga watan Janairun 2026
  • Sai dai, an dage wannan lokacin yayi da gwamnan ke ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan shirin sauya shekar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - An dage shirin ficewar gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Shirin sauya shekar wanda aka tsara tun da farko a ranar Litinin, 5 ga Janairu, 2026, an dage shi zuwa ranar 12 ga Janairun 2026.

Gwamna Abba ya dage shirin sauya sheka zuwa APC
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Twitter

Jaridar The Nation ta ce majiyoyi suka sanar mata da dage lokacin sauya shekar gwamnan na Kano.

Kara karanta wannan

An 'gano' wadanda ke zuga Abba Kabir ya yi watsi da Kwankwaso, ya shiga APC

Meyasa aka dage lokacin sauya shekar Gwamna Abba?

An ce an dage matakin ne domin ba gwamnan damar yin karin tuntuba da ‘yan majalisar tarayya da na jiha daga Kano, da kuma manyan masu ruwa da tsaki da har yanzu ba su nuna cikakken amincewa da matakin ba, Daily Nigerian ta kawo rahoton.

Majiyoyin siyasa a Kano sun bayyana cewa ‘yan majalisar dokokin jihar Kano, karkashin jagorancin Kakakin Majalisa, Jibril Isma’il Falgore, sun shiga sahun shugabannin kananan hukumomi da dama da suka riga suka sanya hannu kan takardar sauya sheka ta gwamnan.

Ficewar dai na daga cikin sabon tsari na siyasa da zai bai wa Gwamna Abba damar taka muhimmin matsayi na jagoranci a jam’iyyar APC a Kano, tare da yiwuwar samun tikitin takarar gwamna kafin zaben shekarar 2027.

Kwankwaso na adawa da sauya shekar Abba

Sai dai wannan mataki, wanda ake ganin dabara ce ta karfafa karfin APC a Kano, bai samu amincewar uban gidansa na siyasa kuma jagoran NNPP na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso ba, wanda ake rade-radin yana dab da komawa jam’iyyar ADC.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya tara 'yan Kwankwasiyya alhali Abba na shirin hada kai da Ganduje a APC

Idan har ficewar ta tabbata, za ta kasance babbar koma baya ga tafiyar Kwankwasiyya da Kwankwaso ke jagoranta.

Tsohon gwamnan ya taba bayyanawa a fili cewa duk wanda ya ci amanar Kwankwasiyya ba zai tsira ba, ba tare da fuskantar sakamako ba.

An ja layi tsakanin Kwankwaso da Abba

Rikicin da ke tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da Kwankwaso ya riga ya janyo rasa mukamin Hashimu Suleiman Dungurawa a matsayin shugaban NNPP na jihar Kano.

Gwamna Abba Kabir Yusuf na shirin sauya sheka zuwa APC
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: @KyusufAbba
Source: Facebook

Daga bisani, Gwamna Abba Kabir ya nada Alhaji Abdullahi Zubairu Abiya a matsayin mukaddashin shugaban NNPP na jihar Kano.

Sai dai, uwar jam’iyyar NNPP ta kasa ta bayyana wannan sauyin shugabanci a Kano a matsayin mara inganci.

Jam’iyyar APC na kallon yunkurin ficewar Gwamna a matsayin babbar nasarar siyasa. Idan ta tabbata, hakan zai yi babban tasiri ga siyasar Kano da ma kasa baki daya, domin zai kwace kujerar gwamna guda daya da NNPP ke da ita.

Haka kuma, ficewar za ta kara karfin APC a Kano, tare da inganta damar jam’iyyar da ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu a babban zaben 2027.

Kara karanta wannan

A karshe, Abba zai rabu da Kwankwaso, Ganduje zai karbe shi zuwa APC

Hadiman Gwamna Abba sun goya masa baya

A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar masu ba da shawara ta musamman ta jihar Kano, ta nuna goyon bayanta ga Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Kungiyar ta bayyana cikakkiyar biyayyarta ga gwamnan tare da jaddada goyon bayanta ga tafiyarsa ta siyasa.

​Hakazalika, mambobin kungiyar sun yanke shawarar goyon bayan dukkan matakan siyasa da gwamnan zai dauka, muddin hakan na cikin maslahar jihar Kano da walwalar al’ummarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng