Hadiman Gwamna Abba Sun Yi Matsaya kan Sauya Shekarsa zuwa APC
- Kungiyar masu ba da shawara ta musamman ta jihar Kano, ta nuna goyon bayanta ga Gwamna Abba Kabir Yusuf
- Mambobin kungiyar sun yi kira ga masu ruwa da tsaki, masu rike da mukamai da su rika auna kalamansu kafin su furta su
- Hakazalika, sun jaddada cewa Gwamna Abba ne jagoran gwamnati kuma mai cikakken ikon yanke muhimman shawarwarin siyasa a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Kungiyar masu ba da shawara na musamman ta jihar Kano ta bayyana cikakken biyayyarta ba tare da tangarda ba ga Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Kungiyar ta jaddada goyon bayanta ga tafiyarsa ta siyasa a daidai lokacin da ta bayyana yanayin siyasar jihar a matsayin mai cike da kalubale.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta ce kungiyar ta bayyana hakan ne a ranar Asabar, 3 ga watan Janairun 2026 a Kano cikin wata sanarwa da sakatarenta Dakta Idris Salisu Rogo, ya sanya wa hannu.
Wace matsaya suka dauka?
Sanarwar ta jaddada cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf shi ne jagoran gwamnati kuma shi ne ke da cikakken ikon yanke dukkan muhimman shawarwarin siyasa a jihar.
A cewar sanarwar, mambobin kungiyar sun yanke shawarar goyon bayan dukkan matakan siyasa da gwamnan zai dauka, muddin hakan na cikin maslahar jihar Kano da walwalar al’ummarta.
“Mai Ggrma gwamnan jihar Kano shi ne jagoran gwamnati, kuma shi ne ke da cikakken ikon jagorantar tafiyar siyasa da yanke shawara."
- Dakta Idris Salisu Rogo
Mashawarta na musamman na tare da Abba
Sanarwar ta kara da cewa mambobin kungiyar sun yi na'am da shugabancinsa, hangen nesansa da manufofinsa, jaridar Tribune ta dauko labarin.
Mashawartan sun kuma bukaci ’yan siyasa, mambobin jam’iyya, masu rike da mukamai da magoya baya da su takaita kalamai da dabi’unsu.
Sun yi gargadin cewa maganganun tayar da hankali, cin mutunci da kuma yada sakonnin sirri na iya rage amincewar jama’a tare da karkatar da hankalin gwamnati daga ayyukan ci gaba.
Duk da amincewa cewa siyasa abu ne mai sauyawa a tsarin dimokuraɗiyya, kungiyar ta jaddada cewa dole ne siyasar ta kasance bisa dattaku, ladabi da mutunta juna, domin kare kyakkyawan tarihin Kano na wayewar siyasa da zaman lafiya.

Source: Facebook
Sanarwar ta sake jaddada goyon bayan hadin gwiwa da kungiyar ke bai gwamnatin Abba Yusuf, musamman a fannoni kamar ingantaccen shugabanci, manufofi masu amfani ga jama’a, bunkasa ababen more rayuwa, jin kai da walwalar al’umma, da gyaran hukumomi.
“Ci gaban da aka samu a muhimman fannoni karkashin jagorancinsa a bayyane yake, kuma ya cancanci kariya da karfafa shi."
- Dakta Idris Salisu Rogo
A karshe, kungiyar ta bukaci dukkan masu ruwa da tsaki da su dora maslahar jihar Kano a gaba fiye da son rai ko takaddamar siyasa, tana mai jaddada cewa hadin kai a cikin gwamnati shi ne ginshikin zaman lafiyar siyasa da ingantaccen yi wa jama’a hidima.
Matsayar Kwankwaso kan sauya sheka
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi magana kan sauya sheka zuwa wata jam'iyya.
Kwankwaso ya jaddada cewa da shi da 'yan tafiyar Kwankwasiyya za su ci gaba da zama a cikin jam'iyyar NNPP.
Hakazalika, ya nuna cewa bai da wani shiri na ficewa daga jam'iyyar NNPP zuwa wata jam'iyya daban.
Asali: Legit.ng

