2027: Kwankwaso Ya Faɗi Sharadin da Zai Sanya Shi Sauya Sheka zuwa Wata Jam'iyya

2027: Kwankwaso Ya Faɗi Sharadin da Zai Sanya Shi Sauya Sheka zuwa Wata Jam'iyya

  • Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi magana game da yiwuwar komawa wata jam'iyya a Najeriya
  • Kwankwaso ya fadi sharadin komawa ko sauya sheƙa zuwa wata jam’iyya yayin da siyasar Kano ke kara zafi
  • Jagoran NNPP ya ce APC ta nemi ya shiga jam’iyyar amma ya ƙi saboda rashin tayin da zai amfanar da shi da magoya bayansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Jagoran NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya yi karin haske kan yiwuwar komawa wata jam'iyyar siyasa game da zaben 2027.

Kwankwaso ya ce zai yi tunanin sauya jam’iyya ne kawai idan aka ba shi tikitin shugaban ƙasa ko mataimaki a 2027.

Kwankwaso ya magani kan shirin komawa wata jam'iyya
Jagoran Kwankwasiya, Sanata Rabiu Kwankwaso. Hoto: Rabi'u Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

Kwankwaso ya magantu kan komawa wata jam'iyya

Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga magoya bayansa a gidansa da ke Kano, yana ambaton tafiyar siyasa ta kusan shekaru arba’in, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Kano: Kwankwaso ya ɗauki zafi game da Abba Kabir, ya buƙaci ya ajiye kujerarsa ta gwamna

Tsohon gwamnan ya ce magoya bayansa a faɗin ƙasa ba za su amince da sauya sheƙarsa ba sai idan hakan ya ba shi manyan muƙamai.

Ya bayyana cewa APC ta gayyace shi shiga jam’iyyar, amma ya ƙi saboda babu wata tayin da ta dace da shi da shugabannin NNPP.

Ya ce:

“Mun ce musu mun yarda mu tafi tare da ku, amma me za ku ba ni? Muƙamai? Nawa? Wanne ne ya dace da ni da zan karɓa? Wanne kuma ya dace da shugaban jam’iyya na ƙasa da shugabanninsa, kasancewar su mutane ne masu daraja? Ba su ba da amsa ba."
Kwankwaso ya faɗi bakin cikinnsa game da rade-radin komawar Abba APC
Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso. Hoto: Rabi'u Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

Kwankwaso ya fusata da shirin Abba Kabir

Kwankwaso ya jaddada cewa akidar Kwankwasiyya na mayar da hankali kan tallafa wa talakawa da matasa ta hanyar ilimi, aiki, lafiya da noma, cewar Arise News.

Game da shirin Abba Kabir Yusuf na komawa APC, Kwankwaso ya nuna takaici, yana cewa gwamnan bai tuntube shi ba kuma hakan cin amana ne.

“Wasu na cewa shiri ne kawai na samun zaɓuɓɓuka na ɗaya, na biyu, na uku da sauransu. Mun kawo waɗannan zaɓuɓɓukan a wancan lokaci, amma yanzu lamari ne na ƙasa, kuma dole ne Kano ta kasance a haɗe domin mu sake yin nasara a zaɓe na gaba,” ya ƙara.

Kara karanta wannan

APC ta manta da rawar da Wike ya taka, ta fadi jagoran jam'iyyar a Rivers

“Wannan darasi ne gare mu duka. Mun yi tunanin kowa ya fahimta. Ba mu taɓa tsammanin cin amana ba. Abu mafi raɗaɗi shi ne bayan duk abin da muka yi wajen ceto Kano daga Ganduje da APC, yanzu kun miƙa kujerar gwamna gare su kyauta."

- Rabiu Kwankwaso

An gano masu zuga Abba Kabir

Kun ji cewa an gano cewa manyan jiga-jigan NNPP a kananan hukumomi 44 na Kano na matsa wa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya koma APC.

Kwamishinan yada labarai a Kano ya ce an yi imanin cewa sauya sheƙar za ta amfani Kano idan ta yi daidai da jam’iyyar da ke mulki.

Ana tattaunawa da Gwamna Abba Kabir Yusuf da Rabiu Kwankwaso, kuma babu alamun rikici a Kano a halin yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.