Kano: Kwankwaso Ya Ɗauki Zafi game da Abba Kabir, Ya Buƙaci Ya Ajiye Kujerarsa Ta Gwamna
- Jagoran siyasar Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya nuna damuwa kan rikicin siyasar Kano da ke faruwa
- Kwankwaso ya yi kira ga ’yan siyasa da su dakatar da duk wani abu da ke kara rarrabuwar kai domin neman hanyar samar da daidaito
- Jagoran Kwankwasiyya ya ce gwamnatin NNPP har yanzu tana da damar yi wa jama’a aiki, idan aka samu haɗin kai da fahimtar juna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa halin da siyasar Kano ke ciki a yanzu abin damuwa ne.
Kwankwaso ya ce abubuwan da ke faruwa sun yi kama da abin da ba za a yarda da su ba, yana mai bayyana cewa da a ce mafarki ne, da ya fi masa sauƙi.

Source: Facebook
Kwankwaso ya damu da rikicin siyasar Kano
Kwankwaso ya bayyana cewa ya gana da manyan ’yan siyasa domin hana duk wani yunkuri da ka iya kawo cikas ga gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, cewar Aminiya.
Duk da rikice-rikicen, ya jaddada cewa gwamnatin NNPP na da sauran lokaci da za ta iya cika alkawurranta, matuƙar an samu haɗin kai da fahimta.
Ya ce kiran da ake yi na komawa APC raini ne ga magoya bayan NNPP da suka sadaukar da lokacinsu da ƙarfinsu domin samun nasara a Kano.
Kwankwaso ya bayyana cewa magoya bayan tafiyar na cikin mawuyacin hali, amma duk da haka sun nuna haƙuri da jajircewa kan abin da suka yi imani da shi.
Gargadin Kwankwaso ga masu zuga Abba Kabir
Ya gargadi masu matsin lamba kan sauya sheƙar gwamnan Kano, yana cewa idan ana son hakan, to a bukace shi ya bar kujerar gwamna.

Kara karanta wannan
Tirkashi: Kwankwaso ya bi hanyoyi 2, ya yi yunkurin tsige Abba daga kujerar gwamnan Kano
“Wannan lokaci ne mai matuƙar rikitarwa. Abin da ke faruwa a Kano kamar mafarki ne. Da a ce bacci nake yi, idan na farka sai na ga duk ba gaskiya ba ne.
“Na yi magana da duk wanda ya dace na yi magana da shi. Wannan gwamnati har yanzu tana da lokaci, kuma idan muka haɗa kai, mutanen Kano za su amfana.
Idan suna da gwamnoni da yawa, me ya sa dole sai Kano? Su yi hattara, kada su raina mu.”

Source: Facebook
Abin da Kwankwaso ke hangowa Kano
Kwankwaso ya yi gargaɗin cewa tilasta wa gwamnan Kano ya sauya sheƙa zai zama ƙwace ikon gwamnati ne.
“Idan suna so ya tafi, su faɗa masa ya ajiye kujerar gwamna ya tafi. Shi kaɗai ne gwamnan da muke da shi.”
- Rabiu Kwankwaso
Kwankwaso ya magantu kan ficewa zuwa wata jam'iyya
An ji cewa an fara hasashen cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na shirin sauya sheka zuwa wata jam'iyya.
Jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya tabo batun sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa wata jam'iyya.
Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa zai ci gaba da zama a jam'iyyar NNPP tare da 'yan tawagarsa ta Kwankwasiyya.
Asali: Legit.ng
