An ‘Gano’ Wadanda Ke Zuga Abba Kabir Ya Yi Watsi da Kwankwaso, Ya Shiga APC
- An gano cewa manyan jiga-jigan NNPP a kananan hukumomi 44 na Kano na matsa wa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya koma APC
- Kwamishinan yada labarai a Kano ya ce an yi imanin cewa sauya sheƙar za ta amfani Kano idan ta yi daidai da jam’iyyar da ke mulki
- Ana tattaunawa da Gwamna Abba Kabir Yusuf da Rabiu Kwankwaso, kuma babu alamun rikici a Kano a halin yanzu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Rahotanni sun bayyana sababbin bayanai game da jita-jitar sauya sheƙar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, daga NNPP zuwa jam'iyyar APC mai mulki.
An ruwaito cewa manyan jiga-jigan NNPP daga dukkan kananan hukumomi 44 na jihar ne ke jagorantar matsin lambar, inda suke kira ga gwamnan da ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC domin amfanin jihar Kano.

Kara karanta wannan
Kwankwaso ya tara 'yan Kwankwasiyya a;hali Abba na shirin hada kai da Ganduje a APC

Source: Facebook
Yadda jiga-jigan NNPP ke zuwa wajen Abba Kabir
Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Ibrahim Waiya, ya bayyana hakan a wata hira ta musamman da AIT Live.
Ya ce masu ruwa da tsaki a NNPP sun yi imanin cewa hadin kai da jam’iyyar da ke mulki a kasar zai kawo cigaba da dama ga jihar.
Waiya ya ce tattaunawar sauya sheƙar na ci gaba da gudana cikin natsuwa da kwanciyar hankali, kuma wasu fitattun ‘yan NNPP na tuntubar ra’ayin Gwamna Abba Yusuf da kuma jagoran jam’iyyar a kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, kan yiwuwar daukar wannan mataki.

Source: Facebook
An yaba kishin Gwamna Abba da Kwankwaso
A cewarsa, duka Kwankwaso da Gwamna Abba Yusuf shugabanni ne masu kishin Kano, wadanda ke fifita muradin al’umma.
Ya ce suna fifita muradun jama'arsu fiye da bukatun kansu ko na siyasa, don haka akwai yiyuwar su amince idan sun ga hakan zai amfani jihar.
Sai dai har yanzu babu wata alama da ke nuna samun sabani tsakanin gwamnan da jagoransa Rabiu Kwankwaso, duk da rade-radin da ke yawo a wasu kafafen yada labarai.
Halin da ake ciki game da siyasar Kano
Rahotanni sun kuma nuna cewa a halin yanzu, Kano na cikin kwanciyar hankali, kuma tattaunawar siyasar na gudana ba tare da tashin hankali ba.
Sai dai ana ganin lamarin na ci gaba da zafafa siyasar Kano duba da yadda Rabiu Kwankwaso ya raini Abba Kabir a siyasa kuma a matsayinsa na mai gidansa wanda ya mara masa baya ya zama gwamnan Kano.
Kwankwaso ya cire kansa cikin masu komawa APC
An ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya tabbatar da cewa ba ya cikin tawagar da za ta koma jam'iyyar AapC tare da Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Jagoran NNPP na kasa ya bukaci magoya bayansa da ka da su tayar da hankulansu kan abubuwan da ke faruwa a jihar Kano saboda abin da ke faruwa.
Tsohon gwamnan ya fadi haka ne a cikin wata sanarwa da aka fitar jim kadan bayan ganawarsa da masu ruwa da tsaki na Kwankwasiyya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
