Dungurawa: Kotu Ta Yi Hukunci kan Dakatar da Shugaban NNPP na Kano

Dungurawa: Kotu Ta Yi Hukunci kan Dakatar da Shugaban NNPP na Kano

  • Jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano ta samu kanta cikin rikici biyo bayan dakatar da shugabanta, Hashimu Sulaiman Dungurawa
  • Batun dakatar da Hashimu Sulaiman Dungurawa ya kai gaban kotu, inda aka yanke hukunci a kan takaddamar da ake yi
  • Mai shari'a Zuwaira Yusuf ta hana Dungurawa bayyana kansa a matsayin shugaban jam'iyyar NNPP na reshen jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyar NNPP a jihar Kano ya kara tsananta, biyo bayan hukuncin da babbar kotun jihar Kano ta yanke.

Hukuncin kotun ya tabbatar da dakatar da shugaban jam’iyyar NNPP a jihar, Hon. Hashimu Suleiman Dungurawa, da mazabarsa ta Gargari da ke karamar hukumar Dawakin-Tofa ta yi.

Kotu ta tabbatar da dakatar da Hashimu Dungurawa
Dakatacccen shugaban jam'iyyar NNPP na Kano, Hashimu Sulaiman Dungurawa Hoto: Mustapha Kakisu Yalwa
Source: Facebook

Jaridar TheCable ta ce alkalin kotun, mai shari'a Zuwaira Yusuf ta yanke hukuncin a ranar Juma'a, 2 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya tara 'yan Kwankwasiyya a;hali Abba na shirin hada kai da Ganduje a APC

Wane hukunci kotu ta yanke a rikicin NNPP?

A hukuncin da ta yanke, Mai shari’a Zuwaira Yusuf ta bayar da umarnin wucin-gadi da ke hana Dungurawa ci gaba da bayyana kansa a matsayin shugaban NNPP na jihar Kano, har sai kotu ta kammala sauraron karar da ke gabanta.

Hukuncin ya biyo bayan bukatar gaggawa mai dauke da kwanan wata 30 ga Disamba, 2025, wadda Shuaibu Hassan da wasu mambobin NNPP tara daga Mazabar Gargari suka shigar a gaban kotu, suna kalubalantar Dungurawa tare da jam’iyyar.

Masu karar sun roki kotu da ta amince da tsarin ladabtarwa da ya kai ga dakatar da Dungurawa, bisa zargin cin mutuncin mukami da mutuncin gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, haddasa rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar, da kuma gazawa wajen biyan kuɗaɗen jam’iyya.

Da take amincewa da bukatar, mai shari’a Zuwaira Yusuf ta ce dakatarwar za ta ci gaba da aiki har sai an saurari karar, tashar Channels tv ta dauko rahoton.

Kara karanta wannan

Ana rade radin komawa APC, mataimakin gwamnan Kano ya tura sako ga Abba da Kwankwaso

"An bayar da umarni cewa dakatarwar da aka yi wa wanda ake kara na farko a ranar 30 ga Disamba, 2025 ta ci gaba da aiki, har zuwa lokacin da za a saurari kuma a yanke hukunci kan bukatar da aka sanar.”

- Mai shari'a Zuwaira Yusuf

An hana Dungurawa bayyana kansa shugaban NNPP

Haka kuma, kotun ta hana Dungurawa bayyana kansa a matsayin shugaban NNPP a jihar Kano, bayan dakatarwar da mazabarsa ta yi masa.

Mai shari’a Zuwaira Yusuf ta kara da cewa:

"An hana wanda ake kara na farko ci gaba da kiran kansa shugaban jam’iyyar NNPP a jihar Kano, sakamakon dakatar da shi da mazabarsa ta yi.”

Kotun ta kuma umarci dukkan ɓangarorin da su ci gaba da bin matsayin da ake ciki bayan ranar 30 ga Disamba, 2025, tare da umarnin a mika dukkan takardun kotu ga waɗanda abin ya shafa.

An ɗage shari’ar, mai lamba KN/1218/2026, zuwa 19 ga Janairu, 2026, domin sauraron karar.

Kotu ta tabbatar da dakatar da Hashimu Dungurawa daga shugabancin NNPP
Taswirar jihar Kano, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

An nada mukaddashin shugaban jam'iyyar NNPP

A halin da ake ciki, kwamitin zartarwa na NNPP a jihar Kano ya sanar da naɗa Hon. Abdullahi Zubairu Abiya a matsayin muƙaddashin shugaban jam’iyyar a jihar.

Kara karanta wannan

An jefa kwamishinan Bauchi a gidan yari, ana zarginsa da daukar nauyin ta'addanci

An amince da wannan naɗin ne bayan taron gaggawa da kwamitin zartarwa na jam’iyyar ya gudanar a sakatariyar NNPP ta jihar Kano.

Dungurawa ya musanta korarsa daga NNPP

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban NNPP na jihar Kano, Hashimu Sulaiman Dungurawa, ya yi magana kan korarsa daga shugabancin jam'iyyar.

Hashimu Dungurawa ya karyata rahotannin da ke yawo masu cewa an kore shi daga shugabancin jam'iyyar.

Ya ce abin da ake kira korar tasa “wasa ne na yara”, yana mai cewa irin wadannan matakai ba su da wani tasiri a bangaren doka ko siyasa a tsarin NNPP.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng