Magana Ta Kare, An Ji Matsayar Kwankwaso kan Shirin Gwamna Abba na Komawa APC
- Jagoran NNPP na kasa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso bai amince Gwamna Abba Kabir Yusuf da mukarrabansa su sauya sheka zuwa APC ba
- Kabiru Adamu Kofar Ruwa, jigo a darikar Kwankwasiyya, ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da manema labarai a Kano
- Ya gargadi Gwamna Abba da sauran masu mara masa baya da su canza shawara, yana mai cewa ba abin da za su samu a APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Ana ci gaba da tattake wuri tsakanin mabiya darikar Kwankwasiyya yayin da jita-jitar da ke cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf zai sauya sheka daga NNPP zuwa APC ke kara karfi.
An tattaro cewa jagoran NNPP na kasa kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso bai amince Gwamna Abba ya sauya sheka zuwa APC ba.

Kara karanta wannan
Ana rade radin komawa APC, mataimakin gwamnan Kano ya tura sako ga Abba da Kwankwaso

Source: Twitter
'Daya daga cikin jagororin Kwankwasiyya a karamar hukumar Dala ta jihar Kano, Kabiru Adamu Kofar Ruwa ne ya tabbatar da hakan a wata hira da Preedom Radio ta wallafa a Facebook.
Kwankwaso ya amince Abba ya tafi APC?
Kabiru Kofar Ruwa ya yi ikirarin cewa yana magana ne da yawun Madugun Kwankwasiyya kuma babu sa hannunsa a wannan shiri da gwamnan Kano ke yi na hada kai da APC.
Ya gargadi 'yan majalisar dokokin jihar Kano da na tarayya, kwamishinoni da ciyamomin kananan hukumomi da ke shirin bin Abba Gida-Gida.
Jigon ya jaddada cewa duk da taimakon da ya yi wa Gwamna Abba, ba ya bukatar komai daga wurinsa, yana mai nanata mubaya'arsa ga Kwankwaso.
Jigon NNPP ta gargadi Gwamna Abba
Kabiru ya ja kunnen gwamnan Kano da cewa da wahala ya ci zaben fidda gwani a APC idan har ya canza jam'iyya saboda kurayen da ke hangen kujerarsa a jam'iyya mai mulkin kasa.

Kara karanta wannan
Ana rade radin zai koma APC, Gwamna Abba ya yi jawabi bayan sa hannu kan kasafin 2026
"Maganar da ake yi ta Gwamna Abba zai koma APC babu sa hannun jagoranmu Injiniya Rabiu Kwankwaso, wanda ya ga zai bi su, su je su ci dadi lafiya. Muna muku Allah Ya isa kuma ba za ku yi nasara ba.
"Jam'iyyar APC da kuke shirin tafiya, ba sa hannun madugu (Kwankwaso), kuma ba umarninsa, sannan ina tabbatar muku da cewa abin da za ku samu a jikinsu, ba zai ci muku zaben fitar da gwani ba.
"Akwai yiwuwar ba za su iya cin zaben fitar da gwani a APC ba, daga shi Gwamna Abba har wadanda za su bi shi. Don haka ina ba ku shawara mu zauna a NNPP mu yi wa jagora Kwankwaso biyayya."
- In ji Kabiru Adamu Kofar Ruwa.

Source: Facebook
Sanata Hanga ya soki masu kiran Abba ya tafi APC
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Rufa’i Sani Hanga ya ce masu kiran Gwamna Abba Kabir Yusuf ya koma APC ba masoyinsa na gaskiya ba ne.
Ya ce bai kamata a zuga Abba Kabir ya juya wa talakawan Kano da suka tsaya tsayin daka suka zaɓe shi a karkashin jam’iyyar NNPP ba.
A cewarsa, duk wanda ke kiran Abba ya koma APC yana so ne ya jefa shi cikin rikici da rashin amincewar jama’a saboda ba a goyon bayan butulci a Kano.
Asali: Legit.ng