Sanatan APC Ya Sha Alwashin Korar Gwamna daga Mulki, Zai Iya Yin Komai a 2027

Sanatan APC Ya Sha Alwashin Korar Gwamna daga Mulki, Zai Iya Yin Komai a 2027

  • Sanata Orji Kalu ya sha alwashin ganin jam'iyyar APC ta kwace mulkin jihar Abia a zaben shekarar 2027 da ke tafe
  • Tsohon gwamnan Abia ya ce zai goyi bayan Shugaba Bola Tinubu da dan takarar APC, domin doke jam’iyyar LP mai mulki
  • Kalu ya bukaci gwamnoni su dauki tsaron jihohinsu da muhimmanci, yana yabawa gwamnan Ebonyi bisa tabbatar da zaman lafiya da tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abakaliki, Ebonyi - Sanata Orji Uzor Kalu ya yi alkawarin amfani da dukkan dukiyarsa domin taimaka wa jam’iyyar APC a zaben 2027.

Kalu ya ce zai yi hakan ne domin ganin APC ta yi nasara a jihar Abia a zaben shekarar 2027 da kwace mulki daga LP.

Sanata Kalu ya sha kasashin kaso APC Abia
Sanata Orji Kalu da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Orji Uzor Kalu.
Source: Facebook

Ya bayyana hakan ne yayin ziyarar sabuwar shekara da ya kai wa shugaban APC na Ebonyi, Cif Stanley Okoro-Emegha, a Ekoli, karamar hukumar Edda, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Ta faru ya ƙare, Gwamna Caleb na Plateau ya yi murabus daga jam'iyyar PDP

Kalu ya sha alwashin kwace mulki a Abia

Tsohon gwamnan Abia ya ce zai yi duk mai yiwuwa domin APC ta kwace mulki daga jam’iyyar LP mai rike da madafun iko a jihar.

Kalu ya ce zai mara wa Shugaba Bola Tinubu da dan takarar gwamna na APC baya, yana mai jaddada cewa zai sa zuciyarsa gaba daya a yakin neman nasara.

Ya ce gwamnan Abia na yanzu, Dakta Alex Otti, abokinsa ne, amma ba batun siyasa ba ne, illa tabbatar da cikakkiyar nasarar APC, kamar yadda rahoton Punch ya tabbatar.

Sanatan ya bukaci gwamnoni su dauki alhakin kare jihohinsu, yana cewa bai dace a dora dukkan nauyin tsaro kan Shugaba Tinubu kadai ba.

Ya tuno da lokacinsa a matsayin gwamna, inda ya ce Abia ta samu cikakken tsaro ba tare da satar mutane ba, duk da matsalolin tsaro a wasu jihohi.

Sanata Kalu ya ce APC za ta yi nasara a Abia
Sanata Orji Uzor Kalu daga jihar Abia. Hoto: Senator Orji Uzor Kalu.
Source: Facebook

Sanata Kalu ya yabawa gwamnan Ebonyi

Kalu ya yabawa gwamnan Ebonyi, Francis Nwifuru, yana cewa ya kafa tubalin zaman lafiya da tsaro, wanda sauran gwamnoni ya dace su kwaikwaya.

Kara karanta wannan

2027: APC ta hararo makomar Tinubu bayan Obi ya hade da Atiku a ADC

Ya kara da cewa ya kirkiro ziyarar sabuwar shekara ne saboda amincin Cif Okoro-Emegha, wanda ya ce mutum ne mai cikakken rikon amana.

Kalu ya ce tun yana yaro ya raini Okoro-Emegha, kuma yana daga cikin mutanen da suka taka rawa a nasarorin da ya samu a lokacin gwamna.

Ya ce ya mika shi hannun tsohon gwamnan Ebonyi, Sanata David Umahi, inda ya bukace shi da cikakken biyayya, wacce ya ci gaba da nunawa.

'Na cancanci neman shugaban kasa' - Sanata Kalu

Kun ji cewa Sanata Orji Kalu ya bayyana cewa yana da gogewar zama shugaban kasa idan jam'iyyar APC ta ba shi dama a 2027.

Tsohon gwannan jihar Abia ya ce a shirye yake ya nemi takara a 2027 idan Bola Tinubu ya haƙura da tazarce domin kawo ci gaba a fadin kasar.

Kalu ya ce lissafinsa shi ne dawowa majalisar dattawa amma idan ya samu dama, zai nemi kujera lamba ɗaya a Najeriya saboda na daga cikin muradunsa a rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.