Wike Ya Yi Barazanar Bude Asiri kan Sulhunsa da Fubara da Tinubu Ya Umarta
- Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya zargi Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, da karya yarjejeniyar da Bola Tinubu ya sasanta
- Wike ya ce nan ba da jimawa ba zai fallasa cikakkun bayanan yarjejeniyar da aka cimma a gaban Shugaban kasa domin kawo karshen rikicin
- Ministan ya gargadi Fubara kan makomarsa ta siyasa, yana mai cewa magoya bayansa sun shirya “gyara kuskuren” zaben 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya zargi Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, da bijirewa yarjejeniyar da aka yi.
Wike na magana na kan yarjejeniyar da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sasanta domin warware rikicin siyasa da ya dabaibaye jihar.

Source: Facebook
Zargin da Wike ke yi kan Fubara
Wike ya yi wannan zargi ne a yayin wata ziyarar godiya da ya kai ga al’ummar Karamar Hukumar Tai a Jihar Rivers, cewar Punnch.
Wike ya bayyana cewa ba da jimawa ba zai fito ya bayyana wa al’ummar Rivers cikakkun bayanan yarjejeniyar da aka cimma a gaban Shugaban kasa.
An cimma yarjejeniyar ne bayan wani taro na sirri da Shugaba Tinubu ya kira a Fadar Shugaban kasa da ke Abuja a watan Yunin 2025.
Taron ya ya hada Wike da Fubara, a kokarin kawo karshen rikicin iko da ya jefa jihar cikin mawuyacin hali, har ya kai ga ayyana dokar ta-baci da dakatar da gwamnan da ’yan majalisar dokokin jihar.
Ko da yake daga baya bangarorin biyu sun yi alkawarin yin aiki tare domin samar da zaman lafiya, babu wanda ya bayyana sharuddan yarjejeniyar a wancan lokaci.

Source: Facebook
Wike ya rena wayon Fubara a siyasa
Sai dai a wannan karon, Wike ya ce gwamnan bai cika wasu daga cikin abubuwan da aka amince da su ba.
Ya ce:
“Bayan an amince kan wani abu, sai ka koma ka saba shi. Kana tunanin kai dan siyasa ne mai wayo? Wayonka kadan ne.
“Ba da jimawa ba, za mu sanar da al’ummar Rivers abin da muka amince da shi a gaban Shugaba kasa. Wannan yarjejeniya ba a yi ta a ko’ina ba face a gaban Shugaban kasa. Idan har za a karya abin da aka amince da shi a gabansa, to wa ake mutunta wa?”
Wike ya sake gargadin Fubara kan makomarsa ta siyasa, yana mai jaddada cewa magoya bayansa sun shirya tsaf domin “gyara kuskuren” zaben 2023.
Ya kuma ce ba kudi ne ke tasiri a siyasa ba, yana mai cewa sun taba doke masu dimbin kudi a baya, kuma za su sake yin hakan, cewar Daily Post.
Ya ce:
“Mun shirya yaki, ku guji wadanda ba su cika alkawari. Suna cewa siyasa ce, amma wannan siyasar ba za ta yi aiki a nan ba.”
Wike ya magantu kan komawar Fubara APC
An ji cewa bayan tsawon lokaci, Ministan Harkokin Abuja, Nyesom Wike ya yi magana kan sauya shekar Gwamna Siminalayi Fubara zuwa APC.
Gwamna Fubara dai ya bayyana cewa ya bar PDP zuwa APC ne domin samun damar goyon bayan tazarcen Shugaba Bola Tinubu.
Wike wanda ya yi mulki a Rivers ya ce Gwamna Fubara na da yancin komawa kowace jam'iyyar siyasa ba tare da ya nemi izininsa ba.
Asali: Legit.ng

