Ta Faru Ya Ƙare, Gwamna Caleb na Plateau Ya Yi Murabus daga Jam'iyyar PDP
- Gwamnan Plateau, Caleb Mutfwang, ya kore dukkan jita-jitar da ake yadawa na barin jam'iyyar PDP mai mulki a jihar
- Caleb Mutfwang ya tabbatar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP, yana cewa yana bukatar shugabanci mai maida hankali da ingantaccen aiki
- A wasikar da ya rubuta ranar 29 ga Disamba, 2025, Mutfwang ya sanar da shugaban PDP na mazabarsa cewa ya janye daga jam’iyyar nan take
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jos, Plateau - Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya.
Gwamnan ya tabbatar da haka yana mai cewa yana bukatar shugabanci mai tsari da ingantacciyar hidima ga al'ummarsa domin kawo abubuwan ci gaba.

Source: Twitter
Mutfwang ya bayyana hakan ne cikin wata wasika mai kwanan wata 29 ga Disamba, 2025, cewar Vanguard.
Yadda APC ta shirya karbar Gwamna Caleb
Tun a watannin baya ake ta yada rade-radin cewa Gwamna Caleb ya bar jam'iyyar PDP mai mulki a jihar zuwa APC.
Har ma jam'iyyar APC reshen jihar Plateau ta shirya gagarumin biki domin tarbar gwamnan zuwa cikinta a shekarar 2026.
Shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda, ya nuna cewa sauya shekar Gwamna Mutfwang za ta kara karfafa jam'iyyar.
Gwamna Caleb ya yi murabus daga PDP
Caleb Mutfwang ya bayyana haka ne a wasikar da ya aikewa shugaban PDP na unguwar Ampang ta Yamma, a karamar hukumar Mangu.
Wasikar, wadda shugabannin mazabar suka karɓa, ta nuna godiyar gwamnan ga jam’iyyar bisa damar da ta ba shi a tsarin dimokuraɗiyya.
Gwamnan ya gode wa shugabannin jam’iyya da magoya bayanta bisa goyon bayan da suka ba shi tsawon shekaru, yana cewa halin siyasar yanzu ya tilasta masa daukar wannan mataki.
Sanarwar ta ce:
“Ina matuƙar godiya ga goyon bayan shugabannin jam’iyya, mambobi da magoya baya a dukkan matakai a lokacin da nake cikin jam’iyyar, kuma ina ci gaba da godewa bisa amincewar da suka ba ni.
“La’akari da halin da ake ciki a yanzu, tare da jajircewata kan shugabanci mai ma’ana, tsayayyen alkibla da ingantaccen bayar da hidima, na ga ya zama wajibi in nemi wata sabuwar dandali ta siyasa.
“Ina rokon a karɓi gaisuwata da matuƙar girmamawa.”
Wannan lamari ya tayar da hankalin ‘yan siyasa a Plateau, inda ake hasashen cewa Mutfwang na shirin komawa APC, duk da babu sanarwa a hukumance har yanzu, cewar rahoton Punch.
Obi ya watsar da LP, ya koma ADC
A wani labarin, tsohon dan takarar shugaban kasa a LP, Peter Obi ya tabbatar da ficewa daga jam'iyyar da ya yi mata takara a zaben 2023.
Peter Obi ya fice a hukumance daga jam’iyyar tare da komawa ADC da aka shirya domin hadaka game da zaben 2027.
Manyan jiga-jigan siyasa daga sassa daban-daban sun halarci taron kaddamar da ADC a Enugu da aka yi a karshen shekarar nan.
Asali: Legit.ng

