2027: APC Ta Hararo Makomar Tinubu bayan Obi Ya Hade da Atiku a ADC
- Jam’iyyar APC ta yi magana kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben shugaba kasa na 2027 bayan sabon shirin hadakar ‘yan adawa a Najeriya
- Hakan na zuwa ne bayan tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, ya fice daga LP zuwa ADC domin kafa kawancen 'yan adawa
- APC ta soki matakin da Peter Obi ya dauka, tana mai cewa sauya jam’iyya zuwa wata jam’iyya alama ce ta rashin daidaito da tsari a siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Bayan Peter Obi ya sauya sheka, jam’iyyar APC ta sake jaddada cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu zai dawo kan karagar mulki a zaben shugaban kasa na 2027.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Obi ya bayyana ficewarsa daga LP a wani taro da aka gudanar a Nike Lake Resort da ke Enugu, inda ya yi kira ga ‘yan Najeriya da jam’iyyun adawa da su dunkule wuri guda domin ceto kasar daga APC.

Source: Twitter
Punch ta wallafa cewa APC ta bayyana cewa sauya jam’iyyar da Obi ya yi ba zai girgiza karfin Tinubu ba, tana mai cewa ‘yan Najeriya sun riga sun amince da jam’iyyar.
Obi da shirin hadakar ‘yan adawa
Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, ya bayyana cewa shigarsa jam’iyyar ADC na daga cikin kokarin gina babbar hadakar ‘yan adawa da za ta kalubalanci APC a zaben 2027.
Tun a watan Yulin 2025, Obi tare da wasu fitattun ‘yan adawa sun fara gabatar da ADC a matsayin dandali na kawance, inda jam’iyyar ke karkashin jagorancin tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, da tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola.
Kafin shigar Obi ADC, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, wanda ya shiga jam’iyyar a watan Nuwamban 2025, ya riga ya tabbatar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2027.
Obi: APC ta ce Tinubu ne zai yi nasara
Sakataren jam’iyyar APC na kasa, Ajibola Basiru, ya bayyana Obi a matsayin dan siyasa marar tabbas da gaskiya, yana mai cewa APC ba za ta bata lokacinta wajen mayar da martani ga kalamansa ba.
Basiru ya ce Obi da sauran abokan tafiyarsa a ADC sun riga sun sha kaye a baya, kuma hakan zai sake faruwa a 2027. A cewarsa, Tinubu zai sake doke su kamar yadda aka yi a zaben da ya gabata.

Source: Twitter
Ya kara da cewa APC jam’iyya ce ta kasa baki daya, mai karfi a dukkan yankunan Najeriya, kuma duk wata hadaka ko kananan kawance ba za su rage mata karfi ba a zabe mai zuwa.
Martanin fadar shugaban kasa ga Obi
MAi magana da ywun Tinubu, Bayo Onanuga, ya soki Peter Obi, yana mai cewa bai da kwarewar jagoranci da za a damka masa shugabancin Najeriya.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Onanuga ya zargi Obi da rashin daidaito, yana mai cewa yana yawan sauya jam’iyya daga APGA zuwa PDP, LP, yanzu kuma ADC, saboda muradin kansa.
Onanuga ya ce Obi ya gaza a lokacin da ya shugabanci karamar jiha kamar Anambra na tsawon shekaru takwas, yana mai cewa ya kamata a dauki irin wadannan bayanai da muhimmanci.
Atiku ya yi maraba da Obi a ADC
A wani labarin, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi maraba da shigar Peter Obi jam'iyyar adawa ta ADC.
Atiku Abubakar ya bayyana cewa lokaci ya yi da dukkan 'yan Najeriya za su hadu a jam'iyyar ADC domin ceto kasar daga halin da ta ke ciki.
Tun a kwanakin baya Peter Obi ya halarci taruka daban daban na jam'iyyar ADC amma sai a karshen 2025 ya yanki katin zama dan jam'iyya.
Asali: Legit.ng


