Atiku Ya Yi Wa Peter Obi Maraba zuwa ADC, Ya Fadi Amfanin Shigarsa Jam'iyyar

Atiku Ya Yi Wa Peter Obi Maraba zuwa ADC, Ya Fadi Amfanin Shigarsa Jam'iyyar

  • Atiku Abubakar ya yi magana kan sauya shekar da tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, ya yi zuwa jam'iyyar ADC
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa shigowar Peter Obi zuwa ADC, babban ci gaba ne ga bangaren adawa
  • Atiku ya yi fatan cewa shigowarsa za ta kara karfin bangaren adawa domin kalubalantar masu rike da mulki da kawo ci gaba a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya yi wa Peter Obi maraba zuwa jam'iyyar ADC.

Atiku Abubakar ya bayyana sauya shekar Peter Obi zuwa ADC a matsayin babban ci gaba a tarihin kawancen siyasa a Najeriya.

Atiku ya yi wa Peter Obi maraba zuwa ADC
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar tare da Peter Obi Hoto: @atiku
Source: Facebook

Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Laraba, 31 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya fadi shirinsa kan 2027 bayan shiga jam'iyyar ADC

Peter Obi ya koma jam'iyyar ADC

Tohon gwamnan na jihar Anambra ya sauya sheka zuwa ADC a hukumance a ranar Laraba, a Nike Lake Resort da ke jihar Enugu.

Da yake magana a wajen taron, Peter Obi ya bukaci ’yan Najeriya da 'yan adawa da su hada kai karkashin babban kawancen kasa, domin ceto Najeriya daga talauci, rarrabuwar kai da durkushewar dimokuradiyya.

Tsohon dan takarar shugaban kasa na LP ya kuma zargi shugabannin siyasar da ke mulki da kwace ikon kasa, tabarbarewar tafiyar da tattalin arziki da kuma rushe ginshikan dimokuradiyya a hankali.

Me Atiku ya ce kan sauya shekar Obi?

Atiku ya ce shigar Peter Obi ADC a hukumance alama ce ta farkon adawa mai karfi, tsari da hadin kai, wadda za ta iya kalubalantar masu rike da mulki tare da samar da shugabanci nagari ga ’yan Najeriya.

"Yau wata rana ce mai matukar muhimmanci a tarihin kawancen siyasa a kasarmu, da shigar dan uwana kuma abokina, Peter Obi, cikin jam’iyyar ADC hukumance.”

Kara karanta wannan

Sanatoci 3 da 'dan majalisar wakilai sun bi Atiku da Peter Obi, sun sauya sheka zuwa ADC

- Atiku Abubakar

Ya bayyana fatan cewa shigowar Peter Obi jam’iyyar zai kara dankon hadin kai a tsakanin ’yan adawa tare da zaburar da kokarin samar wa ’yan Najeriya ingantaccen shugabanci daban da irin wanda ake da shi a yanzu.

Atiku ya yi magana bayan Peter Obi ya shiga ADC
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar Hoto: @atiku
Source: Twitter
"Abin farin ciki ne a gare ni na yi masa maraba a hukumance, yayin da muke sa ran kyakkyawan hadin aiki da zai gina adawa mai karfi, wadda daga karshe za ta kafa gwamnati da za ta kawo ci gaba da zaman lafiya ga al’ummarmu.”

- Atiku Abubakar

Atiku ya kuma yi nuni da bikin kaddamar da kawancen ADC, yana mai bayyana fatan cewa wannan ci gaba zai zaburar da karin ’yan Najeriya su rungumi manufofin siyasar kawancen.

Peter Obi ya yi magana bayan shiga ADC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC a hukumance.

Kara karanta wannan

Tsohon sanata ya fice daga PDP bayan shekara 27, ya koma jam'iyyar ADC

Peter Obi ya koka kan abin da ya kira rugujewar kimar dimokuradiyya a Najeriya, da halin wadanda suka ci gajiyarta na kokarin rusa ta.

Tsohon dan takarar shugaban kasar ya ce matsalolin Najeriya ba su fi karfin warwarewa ba, muddin shugabanni sun rungumi hadin kai jajircewa, tausayi da nuna gaskiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng