Peter Obi Ya Fadi Shirinsa kan 2027 bayan Shiga Jam'iyyar ADC
- Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta samu karuwa bayan shigowar tsohoh dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi zuwa cikinta
- Peter Obi ya bayyana cewa lokaci ya yi da za a ceto dimokuradiyyar Najeriya daga hannun masu son ruguzata
- Tsohon dan takarar shugaban kasar ya nuna cewa a shirye suke su yi fito na fito da masu son yin magudi a zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Enugu - Tsohon gwamnan jihar Anambra kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, ya shiga ADC a hukumance.
Peter Obi ya bayyana cewa shekara mai zuwa za ta zama farkon tafiyar ceto Najeriya.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta ce Peter Obi ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 31 ga watan Disamban 2025 a birnin Enugu.
Peter Obi ya shiga ADC
Ya yi magana ne yayin wani babban taron siyasa da ya samu halartar jama’a da dama, inda ya ce ya kasance cikin hadakar da ADC ke jagoranta tun daga kafuwarta.
A wajen taron, Peter Obi ya samu rakiyar manyan ’yan siyasa da dama, ciki har da Sanata Enyinnaya Abaribe, wanda ya sanar da ficewarsa daga APGA da Victor Umeh da Tony Nwoye, wadanda dukkansu tsofaffin mambobin LP ne.
Haka kuma, wasu tsofaffin ’yan majalisar wakilai na LP karkashin jagorancin Hon. Victor Ogene sun sauya sheka zuwa ADC, tare da Hon. Peter Uzokwe na jam'iyar YPP, mai wakiltar Nnewi ta Arewa/Kudu/Ekwusigo a majalisar wakilai.
Peter Obi ya koka kan dimokuradiyya
Da yake jawabi a wajen taron, Peter Obi ya koka kan abin da ya kira rugujewar kimar dimokuradiyya, yana zargin wasu da suka amfana da tsarin dimokuradiyya da kokarin rusa shi, jaridar Premium Times ta dauko labarin.
"ADC ba za ta bari a lalata dimokuradiyya ba. Mun kuduri aniyar kare hadin kai, tsaro da samar da ingantacciyar Najeriya. Za mu tunkari duk wani shiri na tafka magudi a zaben 2027.”
- Peter Obi
Peter Obi ya kuma soki alkiblar tattalin arzikin kasar nan, yana mai cewa GDP na Najeriya na raguwa duk da karuwar bashin da gwamnati ke karbowa.
"Tattalin arzikinmu ba ya bunkasa, amma muna ci gaba da karbar bashi ba tare da iyaka ba. Wannan ba alamar shugabanci nagari ba ne.”
- Peter Obi
Me Peter Obi ya ce kan matsalolin Najeriya?
A cewarsa, matsalolin Najeriya ba su fi karfin warwarewa ba, muddin shugabanni sun rungumi hadin kai, kwarewa, jajircewa, tausayi da gaskiya.
“Najeriya ba kasa ce matalauciya ba. Abin da muka rasa shi ne shugabanci nagari da gaskiya. Ba za mu kara amincewa da shugabannin da ke fada mana karya yayin da muke ganin ana ci gaba da cin hanci."
- Peter Obi

Source: Facebook
Ya kara da cewa matsalar tsaro a kasar nan ta kai matakin da ba a taba gani ba, yana mai kira ga ’yan Najeriya da su hada kai domin kawo canjin da ya dace.

Kara karanta wannan
Zaben 2027: Peter Obi ya yi karatun ta natsu, ya gano wanda ya dace ya mulki Najeriya
“Muna da bashin da ya fi na kowace gwamnati a tarihi. A yau, Najeriya na fuskantar wulakanci a idon duniya saboda baragurbin shugabanni."
- Peter Obi
Peter Obi ya bayyana cewa kofar hadaka a bude take domin tattaunawa da sauran jam’iyyun siyasa, yana mai jaddada cewa ba a kafa hadakar domin rusa Najeriya ba, sai dai domin ceto ta.
Peter Obi ya magantu kan zaben 2027
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP, Peter Obi, ya yi magana kan zaben 2027.
Peter Obi ya bayyana cewa ya fi kowa cancanta wajen fuskantar kalubalen tattalin arziki da tsaro na Najeriya idan aka ba shi dama.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa idan ya hau mulki, 'yan kasuwa da kananan masana'antu za su bunkasa domin zai tallafa musu.
Asali: Legit.ng

