NNPP: Uwar Jam'iyya Ta Saba da Reshen Kano kan Korar Hashimu Dungurawa

NNPP: Uwar Jam'iyya Ta Saba da Reshen Kano kan Korar Hashimu Dungurawa

  • Kwamitin zartarwa na ƙasa (NWC) na NNPP ya yi watsi da dakatar da Hashimu Dungurawa da 'ya'yan jam'iyyar suka yi a Kano
  • Hedikwatar NNPP ta ce matakin da aka ɗauka ya saɓa wa kundin tsarin jam’iyyar, saboda haka babu wata maganar tsige shi ko kora
  • Jam’iyyar ta jaddada cewa Dungurawa shi ne halastaccen shugaban NNPP a jihar Kano a yayin da aka dauki zafi kan sauya shekar Gwamna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Kwamitin zartarwa na ƙasa (NWC) na jam’iyyar NNPP ya ƙi amincewa da matakin dakatarwa da tsige Hashimu Dungurawa daga shugabancin jam’iyyar a jihar Kano.

Jam’iyyar a matakin kasa ta bayyana cewa dakatarwar da Dungurawa ba ta da tushe a doka, kuma ba ta da wani tasiri a tsarin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

PDP ta kai INEC kotu kan cire sunan 'dan takararta a zaben gwamnan Ekiti

NNPP na son ceto kujerar Dungurawa a Kano
Korarren Shugaban NNPP a Kano Hoto: Mustapha Kakisu Yalwa
Source: Facebook

The Cable ta wallafa cewa a ranar Litinin ne wasu mambobin zartarwa na jam’iyyar a mazabar Gargari da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa suka sanar da dakatar da Dungurawa, tare da cire shi daga shugabanci.

NNPP: Dalilin tsige Hashim Dungurawa a Kano

Daily post ta wallafa cewa an tsige Hashimu Dungurawa ne bisa zargi shugaban da haddasa rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar tare da tayar da rikicin cikin gida.

Dungurawa dai na daga cikin amintattun tsohon gwamnan Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso.

NNPP ta ce korar Dungurawa ta saba doka
Tambarin jam'iyya mai mulki a Kano, NNPP Hoto: Kwankwasiyya reporters
Source: Twitter

Wannan kusanci ya sanya al’amuransa ke jawo ce-ce-ku-ce a siyasar Kano, musamman a wannan lokaci da ake fama da rikice-rikicen cikin gida a jam’iyyar.

Bayan tsige Dungurawa ne kuma kwamitin zartarwa na NNPP a jihar Kano ya sanar da naɗa Abdullahi Abiya a matsayin shugaban jam’iyyar rikon kwarya.

NNPP NWC ta soke dakatar da Dungurawa

Kara karanta wannan

An nada sabon shugaban NNPP a Kano, Gwamna Abba ya kafe sai ya tafi APC

A cikin wata sanarwa da kakakin NNPP na ƙasa, Ladipo Johnson, ya fitar, ya yi Allah wadai da matakin dakatar da Dungurawa.

Ya bayyana shi a matsayin abin da bai dace ba, ya saba da tsarin dimokuraɗiyya, sannan ta kara da cewa ba shi da tasiri saboda rauninsa.

Sanarwar ta ce matakin da aka ɗauka ya saɓa wa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam’iyyar NNPP. Johnson ya ƙara da cewa abin da ya faru na iya zama babban laifin cin amanar jam’iyya.

Kakakin jam’iyyar ya bayyana Hashimu Dungurawa a matsayin shugaba mai aiki tukuru, mai gaskiya da kishin jam’iyya.

A cewarsa, Dungurawa ya taka rawar gani wajen bunƙasa jam’iyyar NNPP a jihar Kano, musamman wajen haɗa kai da jawo sabbin mambobi.

Yadda aka kori Shugaban NNPP a Kano

A baya, mun wallafa cewa NNPP a mazabar Gargari da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano ta sanar da tsige tare da korar shugaban jam’iyyar na jihar, Hashimu Dungurawa, daga jam’iyya.

Kara karanta wannan

Abin da Shugaban NNPP a Kano ya ce bayan rahoton tsige shi daga kujerarsa

Matakin korar Dungurawa ya zo ne makonni biyu kacal bayan da aka sake zaɓensa a matsayin shugaban NNPP na jihar Kano, kuma a lokacin da magana ta yi zafi kan sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf.

An yanke wannan hukunci ne a wani taro da shugabannin mazabar Gargari suka gudanar ƙarƙashin jagorancin shugaban mazabar, Shuaibu Hassan, tare da sakatarensa, Yahaya Saidu Dungurawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng