An Nada Sabon Shugaban NNPP a Kano, Gwamna Abba Ya Kafe Sai Ya Tafi APC
- An nada Abdullahi Zubairu Abiya a matsayin sabon shugaban riko na jam'iyyar NNPP a jihar Kano bayan korar Hashimu Dungurawa
- Abdullahi Abiya ya jaddada cewa za su ci gaba da biyayya ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da kuma gwamnan Kano, Abba K. Yusuf
- Wannan dai na zuwa jim kadan bayan rahotanni kan yiwuwar sauya shekar Gwamna Abba zuwa APC ya karade intanet da cikin gari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Hon. Abdullahi Zubairu Abiya ya zama shugaban riƙo na jam’iyyar NNPP a jihar Kano, bayan tsige Hashimu Dungurawa.
An amince da wannan naɗi ne bayan wani taron gaggawa da kwamitin zartarwa na NNPP a matakin jiha ya gudanar a sakatariyar jam’iyyar da ke Kano.

Source: Twitter
An nada sabon shugaban jam'iyyar NNPP a Kano
Mataimakin mai ba jam’iyyar shawara kan shari’a, Barista Yusuf Mukhtar, ne ya sanar da wannan matsaya, inda ya ce naɗin Abiya ya yi daidai da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam’iyyar NNPP, in ji rahoton NTA.
Majiyoyi daga cikin jam’iyyar sun bayyana cewa matakin ya biyo bayan ƙudurin da kwamitin zartarwa na karamar hukumar Dawakin Tofa ya miƙa, wanda ya ƙunshi tsige da kuma korar Hashimu Suleiman Dungurawa daga jam’iyyar.
Tun da farko, kwamitin zartarwa na Dawakin Tofa, ƙarƙashin jagorancin Hon. Abdullahi Ali Uban Iya Dawanau, ya mika ƙudurin da kwamitin zartarwa na Unguwar Gargari ya yanke zuwa ga shugabancin jam’iyyar a matakin jiha.
An amince da ƙudurin ne a taron zartarwa na biyu da aka gudanar a Unguwar Gargari makonni biyu bayan babban zaɓen da ya gabata, inda aka zargi tsohon shugaban jam'iyyar da aikata ayyukan adawa da NNPP.
Abiya zai warware rikicin NNPP a Kano
Bayan nazari kan rahoton, kwamitin zartarwa na jiha ya amince da matakin tsige shi tare da amincewa da fitowar Hon. Abdullahi Zubairu Abiya a matsayin shugaban riƙo na jam’iyyar NNPP a Kano.
Jami’an jam’iyyar sun ce wannan mataki na da nufin dawo da ɗa’a a cikin jam’iyyar, ƙarfafa haɗin kai da kuma sake tsara yadda za a tunkari al’amuran siyasa a nan gaba a jihar Kano.
Da yake jawabi bayan naɗin nasa, shugaban riƙo na NNPP a Kano, Hon. Abiya, ya ce jam’iyyar za ta yi adalci ga kowa ba tare da nuna bambanci ba.
Ya jaddada cewa za su ci gaba da biyayya ga jagoran jam’iyyar na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da kuma gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf.

Source: Facebook
'Abba ya kafe sai ya tafi jam'iyyar APC'
Rahoton jaridar Daily Nigerian dai ya nuna cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafe kan bakarsa ta tafiya jam'iyyar APC.
Rahoton ya nuna cewa gwamnatin Kano ta umarci ciyamomin jihar da su gudanar da tarurrukan gaggawa domin fitar da matsaya guda na kiran Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamna Abba su koma APC.
Surajo Ibrahim Imam, shugaban ƙaramar hukumar Dala kuma mai magana da yawun ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi, ya fitar da sanarwa a daren Lahadi inda ya buƙaci dukkan shugabanni, kwamishinoni, da masu riƙe da muƙamai su zauna su fitar da saƙon kira ga Kwankwaso da Abba.
A cewarsa, komawa APC ita ce hanyar da za ta fi kawo alheri da ci gaba ga jihar Kano baki ɗaya, duba da yanayin siyasar ƙasar a halin yanzu.

Kara karanta wannan
Kalu: Mataimakin shugaban majalisa ya fara zawarcin gwamna 1 na jam'iyyar LP zuwa APC
Ciyamomi sun roki Abba, Kwankwaso su koma APC
A wani labari, mun ruwaito cewa, wasu ciyamomi a Kano sun roki Sanata Rabiu Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir Yusuf da su jagorance su zuwa jam'iyyar APC.
Masu ruwa da tsaki na jam'iyyar NNPP sun bayyana cewa komawa APC za ta tabbatar da dorewar zaman lafiya da samar da ci gaban ayyukan raya kasa a jihar Kano.
Tuni dama dai Bashir Ahmad ya bayyana yakinin cewa sauya shekar Gwamna Abba Yusuf zuwa jam'iyyar APC za ta tabbata nan da 'yan kwanaki kadan masu zuwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

