Tsohon Sanata Ya Fice daga PDP bayan Shekara 27, Ya Koma Jam'iyyar ADC
- Jam'iyyar PDP ta rasa daya daga cikin jiga-jiganta a jihar Enugu bayan ficewar tsohon sanata a majalisar dattawan Najeriya
- Sanata Gilbert Nnaji wanda ya wakilci Enugu ta Gabas ya fice daga jam'iyyar PDP bayan ya kwashe shekara 27 a cikinta
- Tsohon sanatan ya tattara kayansa zuwa ADC wadda ya bayyana a matsayin inda zai samu damar ba da gudunmawarsa wajen gina kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Enugu - Tsohon sanata mai wakiltar Enugu ta Gabas a majalisar dattawa, Gilbert Nnaji, ya raba gari da jam'iyyar adawa ta PDP.
Sanata Gilbert Nnaji wanda yake tsohon shugaban kwamitin majalisar dattawa kan sadarwa, ya aika wasikar ficewa daga jam'iyyar PDP.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 26 ga Disamban 2025, wadda ya aike wa shugaban PDP na gundumar Umuenwene, Iji Nike, a karamar hukumar Enugu ta Gabas.
Tsohon sanatan ya fice daga PDP
Gilbert Nnaji wanda ya shafe shekaru 27 a jam’iyyar PDP ya ce yanke wannan shawara ta kasance mai matukar wahala a gare shi.
Sanatan ya ce matakin ficewa daga jam'iyyar ya zama mai wahala a gare shi ne duba da irin tunanin ci gaban kasa da damar gina Najeriya da PDP ta ke da su tun farkon dimokuradiyya.
Glibert Nnaji ya tuna cewa an kafa PDP ne bisa tushen dimokuradiyya na gaskiya, kamar hadin kai, kishin kasa, adalci, gaskiya, rikon amana, sadaukarwa, mutunta juna da juriya, jaridar The Cable ta dauko labarin.
Tsohon dan majalisar ya kara da cewa ya sadaukar da kansa ga jam’iyyar tsawon shekaru da dama tare da bayar da gagarumar gudummawa ga abin da ya kira jam’iyyar da ta taba zama mafi girma a Afirka.
Meyasa Sanata Nnaji ya rabu jam'iyyar PDP?
Sai dai ya ce abubuwan da ke faruwa a baya-bayan nan sun tabbatar masa da cewa PDP ta zama jam’iyyar da ba za a iya gyarawa ko ceto ta ba, yana mai bayyana wannan hali a matsayin abin takaici matuka.
Nnaji ya ce bayan shawara mai zurfi da ’yan uwansa, abokan hulda da wasu fitattun ’yan kasa, ya yanke shawarar nemo wata sabuwar kafa ta siyasa da zai ci gaba da bayar da gudummawa wajen ci gaban kasa.

Source: Facebook
Gilbert Nnaji ya shiga hadakar ADC
A cewarsa, ya samu wannan dama ne a jam'iyyar ADC wadda ya bayyana a matsayin ingantacciyar kafa mai cike da sabuwar dama da kwararru masu kishin kasa domin hada karfi da karfe wajen gyara alkiblar Najeriya.
A karshe, Nnaji ya gode wa shugabancin tsohuwar jam’iyyarsa bisa fahimta, tare da yi wa PDP fatan alheri a gaba.
An fara zawarcin gwamnan Abia zuwa APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu, na zawarcin gwamnan Abia, Alex Otti zuwa jam'iyyar APC.
Benjamin Kalu ya bayyana cewa a shirye yake ya ba da cikakken goyon bayansa ga Gwamna Otti, ida ya shigo APC.
Mataimakin shugaban majalisar wakilan ya jaddada cewa kofar APC a bude take ga shugabanni masu son yin aiki tare da ita domin karfafa jam’iyyar.
Asali: Legit.ng

