Kalu: Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Fara Zawarcin Gwamna 1 Tilo na Jam'iyyar LP zuwa APC

Kalu: Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Fara Zawarcin Gwamna 1 Tilo na Jam'iyyar LP zuwa APC

  • Mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu, ya fara zawarcin gwamnan jihar Abia, Dr. Alex Otti zuwa jam'iyyar APC
  • Benjamin Kalu ya yi kira da gwamnan jam'iyyar hamayya ya sauya sheka daga jam'iyyarsa ta LP zuwa APC mai mulki a Najeriya
  • Mataimakin shugaban majalisar wakilan ya bayyana cewa zai bada cikakken goyon baya ga gwamnan idan ya shigo jam'iyyar APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Abia - Mataimakin shugaban majalisar wakilai, Rt. Hon. Benjamin Kalu, ya mika kokon bararsa ga gwamnan jihar Abia, Dr. Alex Otti.

Benjamin Kalu ya yi kira a bainar jama’a ga Dr Alex Otti, kan ya fice daga jam’iyyar LP ya koma APC mai mulki.

Benjamin Kalu ya fara zawarcin gwamnan jihar Abia zuwa APC
Mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu da Gwamna Alex Otti na jihar Abia Hoto: @BenKalu, @alexottiofr
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta ce Kalu ya bayyana hakan ne yayin rabon kayan abinci na Kirsimeti na shekara-shekara da ya gudanar a Agbamuzu, cikin karamar hukumar Bende ta jihar Abia a ranar Litinin, 29 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan

Sauya shekar Gwamna Mutfwang daga PDP zuwa APC ta bar baya da kura

Ana zawarcin Gwamna Alex Otti zuwa APC

Benjamin Kalu ya ba da tabbacin cikakken goyon baya ga Gwamna Otti idan ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

"Bari na sake amfani da wannan dama, a fili a gaban jama’a, na gayyaci Gwamna Alex Otti ya shiga jam’iyyarmu. Idan ya zo jam’iyyarmu, za mu ba shi cikakken goyon baya."

- Benjamin Kalu

Ya jaddada cewa kofar APC a bude take ga shugabanni masu son yin aiki tare da ita domin karfafa jam’iyyar da kuma cimma manufofinta na siyasa a jihar Abia.

Kalu ya fadi amfanin gwamnatin Tinubu

Da yake magana kan ziyararsa, Kalu ya ce majalisa tare da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu suna aiki ne domin amfanin ’yan Najeriya, rahoton Daily Post ya tabbatar da hakan.

Mataimakin shugaban majalisar wakilan ya kara da cewa yana da alhakin bai wa al’ummar mazabarsa bayani kan ayyukansa.

Ya bukaci ’yan Najeriya da su ci gaba da goyon bayan Shugaba Tinubu, jam’iyyar APC da kuma shirin Renewed Hope Agenda.

Kara karanta wannan

Wike ya yi magana kan shiga APC, ya fadi abin da zai faru idan ya bar PDP

Yayin da yake karfafa gwiwar ’ya’yan jam’iyyar da ke sha’awar tsayawa takara a zaben 2027, Kalu ya tabbatar musu da cewa Shugaba Tinubu zai goyi bayan ’yan takarar APC, tare da kira da a kara kaimi wajen wayar da kan jama’a a jihar.

Mataimakin shugaban majalisar wakilai zai ba da tallafi a jihar Abia
Benjamin Kalu a zauren majalisar wakilai Hoto: @BenKalu
Source: Twitter

Benjamin Kalu zai ba da tallafi

Mataimakin shugaban majalisar ya kuma sanar da shirin tallafin Naira biliyan 1 domin taimaka wa kanana da matsakaitan ’yan kasuwa 2,000 a dukkan kananan hukumomin jihar.

Ya ce kowanne daga cikin masu cin gajiyar shirin zai samu kimanin N500, 000, tare da hadin gwiwar hukumomi kamar bankin masana'antu, bankin noma da SMEDAN, domin fadada shirin.

Yayin da yake bayyana jihar Abia a matsayin jiha mai hazaka a harkar kasuwanci, Kalu ya ce wannan shiri zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da karfafa al’ummar jihar.

Gwamna Otti na shirin daina siyasa

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya bayyana shirinsa na yin ritaya daga harkokin siyasa.

Gwamna Otti ya bayyyana cewa da zarar ya kammala wa'adin mulki sau biyu a matsayin gwamnan Abia, zai hakura da siyasa.

Ya bayyana bai da burin yin takarar shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa ko wata kujerar siyasa idan ya sauka daga mukamin gwamna.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng