Sauya Shekar Gwamna Mutfwang daga PDP zuwa APC Ta Bar Baya da Kura
- Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa gwamnan Plateau, Caleb Mutfwang, ya shiga jam'iyya mai mulkin kasa
- Tuni jam'iyyar APC a jihar Plateau ta fara shirye-shiryen tarbar gwamnan zuwa cikinta, inda ta shirya gagarumin bikin maraba da shi da mutanensa
- Sai dai, babbar jam'iyyar hamayya ta PDP ta ce ba ta da masaniya kan sauya shekar domin har yanzu gwamnan ne shugabanta a jihar Plateau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Plateau - Jam’iyyar PDP reshen Plateau ta bayyana cewa Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang har yanzu cikakken mamba ne kuma shugabanta a jihar.
Hakan na zuwa ne duk da ikirarin da shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yi cewa gwamnan ya sauya sheka zuwa APC.

Source: Twitter
Jaridar Tribune ta ce sakataren yada labarai na PDP a jihar, Dr Felix Choji, ya jaddada cewa Gwamna Mutfwang har yanzu mamba ne kuma shugaban PDP a Plateau.

Kara karanta wannan
Kalu: Mataimakin shugaban majalisa ya fara zawarcin gwamna 1 na jam'iyyar LP zuwa APC
An ce Gwamna Mutfwang ya koma APC
A baya-bayan nan dai shugaban APC na kasa ya sanar a taron NEC na jam’iyyar da aka gudanar a Abuja cewa Gwamna Mutfwang ya shiga APC.
Wannan sanarwa ta biyo bayan wani taron masu ruwa da tsaki na APC da aka yi a Jos, babban birnin jihar Plateau, inda aka bayyana sauya shekar gwamnan, jaridar The Punch ta kawo labarin.
APC a matakin jiha da na kasa sun cimma matsaya na karbar gwamnan a hukumance cikin jam’iyyar kafin ranar, 20 ga Janairu, 2026, a filin wasan Polo da ke Jos.
Sai dai magoya bayan gwamnan sun nuna damuwa kan dalilin da ya sa bai sanar da PDP ba a matakin gunduma, karamar hukuma da shiyya, ganin cewa taron karbarsa zuwa APC zai gudana cikin kasa da makonni uku.
Me jam'iyyar PDP ta ce kan ficewar Mutfwang?
Dr Felix Choji ya bayyana cewa ba su samu wata takarda a hukumance ba daga gwamnan ko wakilinsa da ke nuna cewa yana ficewa daga jam’iyyar.

Kara karanta wannan
Gudun shan jifa: 'Dan APC ya bukaci gwamna ya ba su hular kwano kafin su iya tallata Tinubu
"Gaskiyar magana ita ce, a matsayinmu na jam’iyya a Plateau, har yanzu ba mu samu wata wasika daga gare shi ko daga wani wakilinsa da ke nuna niyyarsa ta ficewa daga PDP ba. A yau, gwamnan har yanzu cikakken mamba ne kuma shugaban PDP a jihar Plateau.”
"Shi ne shugaban jam’iyyar a yanzu. Ba mu samu wata wasika ko sanarwa da ke nuna yana barin jam’iyyar ba. Don haka a wurinmu, jirgi ba ya motsi ba tare da direba ba, shi ne shugaba kuma jam’iyyar na jiran matsayarsa a fili.”
- Dr. Felix Choji

Source: Facebook
Dr. Felix Choji ya bayyana cewa a siyasa, kasancewa mamba a jam'iyya na farawa ne daga matakin gunduma, yana mai cewa babu wata sanarwa daga gundumar gwamnan, ko karamar hukumarsa, ko shiyyar da ya fito.
“Mun yi bincike, kuma har zuwa yanzu babu wata takarda ko sanarwa daga wadannan matakai uku. A halin da muke ciki, babu wani abu makamancin haka."
- Dr. Felix Choji
Gwamnan Filato na shirin komawa APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang ya yanke shawarar sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.
Mai ba Gwamna Mutfwang shawara kan harkokin siyasa, Istifanus Nwansat, ya tabbatar da cewa mai gidansa na dab da komawa APC.
Nwansat ya bayyana cewa rikicin cikin gida da ya dabaibaye PDP ya sa jam’iyyar ta zama wuri mara tabbas ga ’yan siyasa da ke son tsayawa takara a zaɓe na gaba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng