Yahaya Bello zai Nemi Kwace Kujerar Sanata Natasha a Zaben 2027

Yahaya Bello zai Nemi Kwace Kujerar Sanata Natasha a Zaben 2027

  • Tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Sanatan Kogi ta Tsakiya a babban zaɓen 2027
  • Ya sanar da wannan mataki ne a fadar Ohinoyin Ebira, inda manyan shugabannin gargajiya da addini suka nuna masa goyon baya
  • Matakin nasa ya haifar da rade-radi game da fafatawa kai tsaye da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, wadda ke rike da kujerar a yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kogi - Tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana cewa ya amince da kiran da aka yi masa na tsayawa takarar Sanatan Kogi ta Tsakiya a babban zaɓen 2027.

Wannan sanarwa ta fito ne a yayin wata ziyara da ya kai fadar Ohinoyin Ebira, inda ya gana da sarakunan gargajiya, malamai da sauran masu ruwa da tsaki daga yankin.

Kara karanta wannan

Abin da muka sani game da jita jitar harin Amurka ya hallaka Turji a Sokoto

Yahaya Bello da Sanata Natasha Akpoti
Sanata Natasha Akpoti da tsohon gwamna Yahaya Bello. Hoto: Alhaji Yahaya Bello|Nigerian Senate
Source: Facebook

Sanarwar ta fito ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa a fagen siyasar Kogi.

Yahaya Bello zai nemi kujerar Natasha

A yayin taron da aka gudanar a fadar Ohinoyin Ebira, Yahaya Bello ya ce ya amince da roƙon da al’ummar yankin suka yi masa na tsayawa takarar Sanata a 2027.

Ya bayyana hakan ne bayan ya saurari jawaban shugabannin gargajiya, na addini da na siyasa daga sassan Kogi ta Tsakiya.

Yahaya Bello ya ce kiran da aka yi masa ya nuna amincewa da irin rawar da ya taka a lokacin da yake gwamnan jihar, inda ya jaddada cewa zai yi amfani da gogewarsa domin wakiltar muradun al’ummar yankin a matakin ƙasa.

Rahotanni sun nuna cewa wannan taro ya samu halartar gwamnan Jihar Kogi na yanzu, Ahmed Usman Ododo, tare da wasu manyan ’yan siyasa da sauransu.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fadi ainihin dajin da bama baman Amurka suka sauka a Najeriya

Shugabannin Ebira sun yabi Yahaya Bello

A yayin taron, Gwamna Ahmed Usman Ododo ya roƙi Yahaya Bello da ya amince da kiran da shugabannin jam’iyya da al’ummar yankin suka yi masa na tsayawa takarar.

Vanguard ta rahoto an ce wannan roƙo ya gudana ne a gaban Ohinoyin Ebira da wasu fitattun mutane, lamarin da ya ƙara ba wa lamarin armashi.

Haka zalika, shugaban Karamar Hukumar Okehi, Amoka Eneji, ya taya tsohon gwamnan murna bisa matakin da ya ɗauka na yin takara a 2027.

Ya bayyana cewa Yahaya Bello ya taka rawar gani wajen haɗa kan al’ummar Ebira da kuma bunƙasa yankin a lokacin mulkinsa.

Tsohon gwamnan Kogi a ofis. Hoto: Alhaji Yahaya Bello
Yahaya Bello da ya ce zai yi takarar Sanata a 2027. Hoto: Alhaji Yahaya Bello
Source: Facebook

Eneji ya ƙara da cewa tarihin shugabancin Yahaya Bello zai ci gaba da kasancewa abin tunawa a kasar Ebira, yana mai cewa wakilcinsa a majalisar dattawa zai zama wata dama ta ci gaba da kare muradun yankin.

Kalubale a siyasar Kogi ta Tsakiya

Kujerar Sanatan Kogi ta Tsakiya a halin yanzu na hannun Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, wadda aka zaɓa a shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Sokoto ta fito da bayanai kan harin da Amurka ta kai jihar

Sanatar lauya ce kuma tsohuwar ’yar takarar gwamna, wadda ta kafa tarihi a matsayin mace ta farko da ta wakilci yankin a majalisar dattawa.

Shigowar Yahaya Bello cikin takarar na nuni da yiwuwar fafatawa mai zafi a zaɓen 2027, duba da irin tasirin da yake da shi a jam’iyyar APC da kuma gogewarsa a siyasar jihar bayan ya yi gwamna daga 2016 zuwa 2024.

Akpabio ya sake maka Sanata Natasha a kotu

A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya kara maka Sanata Natasha Akpoti a kotu.

Hakan na zuwa ne bayan kotu tarayya da ke Abuja ta kori karar da ya shigar da Sanatar saboda gaza cika ka'idojin doka wajen shigar da kara.

Biyo bayan matakin, Sanata Akpabio ya garzaya kotun koli inda ya yi zargin cewa ba a masa adalci ba a karar da ya shigar a karon farko.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng