Zaben 2027: Peter Obi Ya Yi Karatun Ta Natsu, Ya Gano Wanda Ya Dace Ya Mulki Najeriya
- 'Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, ya yi tsokaci kan babban zaben da ake tunkara na 2027
- Peter Obi ya bayyana cewa ba zai yarda ya yi wa wani 'dan siyasa mataimaki a zaben shugaban kasa na shekarar 2027 ba
- Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya yi tsokaci kan abin da ya sa yake ganin shi ne wanda ya fi dacewa ya mulki Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, ya yi magana kan zaben 2027.
Peter Obi ya bayyana cewa ya fi kowa cancanta wajen fuskantar kalubalen tattalin arziki da tsaro na Najeriya idan aka ba shi dama.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta ce Peter Obi ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyi daga ’yan Najeriya daban-daban a wani taron tattaunawa na X Space da aka gudanar.

Kara karanta wannan
Peter Obi: An ji yadda gwamna ya tube, ya wanke bandaki mai kazanta a jirgin sama
Peter Obi ya ce ya fi sauran 'yan takara
Peter Obi ya ce babu wani daga cikin wadanda ke shirin tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027 da zai iya yin ikirarin ya fara karamin kasuwanci daga tushe, ya kula da shi, har ya gina shi ya zama babban kamfani kamar yadda shi ya yi.
Ya yi bayanin cewa gyara tattalin arziki zai taimaka matuka wajen magance matsalolin tsaro a Najeriya, domin a cewarsa, tattalin arziki da tsaro suna tafiya ne tare.
Tsohon gwamnan Jihar Anambra ya ce:
"Na san yadda zan gyara Najeriya. Na gina kasuwancina tun daga tushe, kuma ina da kwarewa fiye da kowane dan takara, har da shugaban kasa mai ci. Ni kwararre ne a harkar kudi, kuma na san yadda ake tafiyar da kudi.”
'Yan kasuwa za su ji dadin Peter Obi
Ya kara da cewa idan yana mulki, kananan ’yan kasuwa da masana’antu za su bunkasa, domin zai mayar da hankali wajen tallafa musu, yana mai jaddada cewa su ne ginshikin tattalin arziki a kasashen da suka ci gaba.
Tsohon dan takarar na LP ya karyata rade-radin da ke cewa yana shirin shiga hadakar jam’iyyar ADC ne domin zama mataimakin dan takarar shugaban kasa, jaridar Tribune ta dauko labarin.
Ya bayyana karara cewa:
“Zan kasance a jerin sunayen ’yan takara a zaben 2027.”
Peter Obi ya ba magoya bayansa shawara
Peter Obi ya kuma bukaci magoya bayansa da kada su tsunduma cikin tashin hankali ko cin zarafi da musayar zagi da abokan hamayya, ko da kuwa an tsokane su.

Source: Facebook
Ya yi wannan kiran ne yayin da yake amsa tambayar wani dan Obidient daga jihar Akwa Ibom, wanda ya koka kan cin mutunci da wasu shugabannin hadakar ADC ke yi masa.
Peter Obi ya bayyana cewa yana goyon bayan hadakar gaba daya, yana mai cewa ya kasance cikin wadanda suka kafa ta tun daga farko.
"Babu wanda zai iya hasashen abin da gobe za ta zo da shi. Mu shiga kawancen da zuciya daya. Ba za mu magance matsalolin Najeriya ta hanyar muzgunawa ba."
"Za mu magance su ne ta hanyar sanya mutanen da suka dace su rike al’amuranmu.”
- Peter Obi
Peter Obi ya shirya shiga ADC
A wani labarin kuma, kun ji cewa Peter Obi wanda ya yi takarar shugaban kasa a zaben 2023, ya shirya shiga jam'iyyar ADC.
Peter Obi zai shiga jam'iyyar ADC ne a hukumance a wani gagarumin biki da za a yi a jihar Enugu da ke yankin Kudu maso Gabas.
Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa magoya baya da mabiyan Peter Obi sun riga sun fara shirye-shiryen sauya shekar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

