Gudun Shan Jifa: 'Dan APC Ya Bukaci Gwamna Ya ba Su Hular Kwano kafin Su Iya Tallata Tinubu
- Wani jagoran APC a Katsina ya bayyana fargabar wajen tallata APC saboda jama'a suna cikin fushi da takaicin yadda ake tafiyar da gwamnati
- Hon. Bashir Yandoma ya bayyana cewa duk da ba wai gwamnati ce kai tsaye ta sabawa jama'a ba, ana takaicin kamun ludayin wasu jami'a
- Ya nemi daukin Gwamna Umaru Dikko Radda wajen sama masu hular kwano domin ya ba su damar shiga kamfen cikin kwanciyar hankali
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Katsina – Jagora a APC reshen jihar Katsina, Hon. Bashir Yandoma, ya bayyana fargaba kan shirin fita tallata jam’iyyar APC ga talakawan Najeriya gabanin babban zaɓe mai zuwa.
Ya ce halin fushi da jama’a ke ciki a yanzu ka iya hana masu yaƙin neman zaɓe samun damar kusantar jama’a cikin kwanciyar hankali.

Source: Twitter
Jigo a APC ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da Katsina Post, wacce aka wallafa a shafin Facebook na kafar.
Jigon APC ya yi magana kan tallata APC
Hon. Yandoma, wanda ya rantse da sunan Allah SWT domin jaddada maganarsa, ya bayyana cewa akwai barazana wajen shirin tallata APC a nan gaba.
A cewarsa, rashin kyautata wa jama’a da ake zargin wasu jami’an gwamnati da yi ne ya haddasa fushin da ke kara kamari a tsakanin talakawa.
Hon. Bashir Yandoma ya bayyana cewa jama’a da dama na cikin fushi da takaici. Saboda haka, akwai yiyuwar wannan fushi ya juya zuwa kai masu hari idan sun fita tallata APC.
An nemi taimakon Gwamna kan tallata APC
Hon. Bashir Yandoma ya roƙi Gwamnan Jihar Katsina, Umaru Dikko Radda, da ya taimaka masu ta hanyar samar da kariya da kayan aiki domin su samu damar fita tallata jam’iyyar APC cikin aminci.
Ya ce idan ana so masu yaƙin neman zaɓe su iya shiga cikin jama’a ba tare da tsoro ba, dole ne a tanadi matakan tsaro da za su kare rayukansu.
A kalaman Yandoma:
“Magana ɗaya, na rantse da Allah, ka ji na yi rantsuwa, idan ba a yi gyara ba, idan Allah Ya kai mu, mu da muke zuwa mu tallata jam’iyyarmu ta APC, sai mun wayi gari ba mu iya zuwa mu tallata ta,” in ji Yandoma.
“In kuwa za mu yi, to Mai Girma Gwamna, idan za a kawo kayan zaɓe, a haɗa da hular kwano,” ya ƙara da cewa, yana nuni da buƙatar kariya.
Dalilin jigon APC na neman daukin Gwamna
Hon. Yandoma ya bayyana cewa akwai yiyuwar wasu fusatattun talakawan Najeriya su bi masu tallata APC da jifa ko cin zarafi idan suka je wuraren taro.
Ya ce wannan fargaba ta samo asali ne daga yadda jama’a ke nuna rashin jin daɗi da halin da suke ciki saboda sakacin wasu jami'an gwamnati.

Source: Facebook
Ya ƙara da cewa:
“Muna iya zuwa wani wuri, wasu da ba su kyautata ba, fushinsu zai sa su jefe mu. Ba don Mai Girma Gwamna ba, kowa ya san abin da ya kamata ya yi, yana yi. Amma akwai wasu da ke riƙe da makamai, waɗanda ba sa kyautata wa mutanen da suke wakilta.”
Hon. Bashir Yandoma ya bayyana fatan cewa Gwamna Umaru Dikko Radda zai saurari koken da suka gabatar, tare da ɗaukar matakan taimaka masu.
Gwamnan Katsina ya wanke gwamnoni
A baya, mun wallafa cewa Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya buƙaci ’yan Najeriya da su daina ɗora wa gwamnonin jihohi laifin tabarbarewar tattalin arzikin ƙasar nan dajefa jama'a a wahala.
Gwagwaren Katsina ya kara da bayyana cewa tsarin rabon kudin shiga ne ke jefa jihohi da ƙananan hukumomi cikin matsin lamba, ya ce a hakikanin gaskiya, gwamnatin tarayya ce ke karɓar fiye da rabin kudadi.
Gwamnan ya yi ƙoƙarin fayyace wa jama’a yadda tsarin rabon kuɗaɗen shiga ke aiki, tare da kare gwamnonin jihohi daga zargin da ake musu a kan tsadar rayuwa da tabarbarewar tattalin arziki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


