Bayan Tsawon Lokaci, Wike Ya Yi Magana kan Sauya Shekar Gwamna Fubara zuwa APC
- Bayan tsawon lokaci, Ministan Harkokin Abuja, Nyesom Wike ya yi magana kan sauya shekar Gwamna Siminalayi Fubara zuwa APC
- Gwamna Fubara dai ya bayyana cewa ya bar PDP zuwa APC ne domin samun damar goyon bayan tazarcen Shugaba Bola Tinubu
- Ministan Abuja ya ce Gwamna Fubara na da yancin komawa kowace jam'iyyar siyasa ba tare da ya nemi izininsa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers, Nigeria - Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, na da ’yancin sauya sheka zuwa jam’iyyar APC ba tare da neman izini daga gare shi ba.
Sai duk da haka, Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas, ya jaddada cewa hakan ba ya nufin zai sake samun nasara kai tsaye a zaɓen 2027 ba.

Source: Twitter
Wike ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawarsa ta wata-wata da kafafen yaɗa labarai a gidansa da ke Fatakwal a ranar Litinin, kamar yadda Vanguard ta kawo.
Dalilin Gwamna Fubara na shiga APC
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Fubara ya fice daga babbar jam’iyyar adawa, PDP zuwa jam’iyya mai mulki a farkon watan Disamba, bayan wata ganawa ta sirri da Shugaba Bola Tinubu a Abuja.
Da yake magana a wani taron manema labarai bayan ganawa da Tinubu, Fubara ya ce ya sauya sheka ne domin bayar da “cikakken goyon baya” ga Shugaban Ƙasa a zaɓen 2027.
Da aka tambayi Wike game da sauya shekar Fubara zuwa APC, ministan ya ce gwamnan ba ya buƙatar izini daga gare shi ba.
Abin da Wike ya ce kan sauya shekar Fubara
Ya bayyana matakin a matsayin abu na dabi’a da ya saba faruwa, duba da yadda ’yan Majalisar Dokokin Jihar Ribas da shugabannin ƙananan hukumomi suka riga suka sauya sheka.
Ya ƙara da cewa bai yi mamakin sauya shekar Gwamna Fubara ba, yana mai cewa wasu daga cikin mutanen da a baya suka zarge shi da yiwa APC da Shugaba Tinubu aiki, su ma yanzu sun koma jam’iyya mai mulki.
Ya ce:
“Ba zan ce ina da ikon hana wani shiga kowace jam’iyya ko yin duk abin da ya ga dama ba. Daga abin da ka faɗa, babu abin da ya rage domin ba sai ya nemi izini ba.
“Abin da nake faɗa shi ne, mutane da yawa suna tunanin cewa idan suka sauya sheka, za su zamu tikitin takara babu hamayya. Ba haka abin yake ba,, dole sai mutum ya yi aiki tukuru, ya nuna cewa ya cancanci wannan tikiti.

Source: Facebook
Wike ya kara da cewa gwamnoni da dama da suka zarge dhi da yi wa Bola Tonubu aiki sun bar PDP zuwa APC mai mulki.
Wike ya gargadi masu shiga APC
A wani rahoton, kun ji cewa Nyesom Wike ya bayyana cewa shiga jam'iyyar APC ko nuna biyayya ga Shugaba Bola Tinubu ba zai ba 'yan siyasa tikitin tazarce kai tsaye ba.
Ministan Abuja ya jaddada cewa dole ne a auna dan siyasa a kan alkawuran da ya cika da ayyukan da ya aiwatar, domin tantance wanda zai yi takara a 2027.
Wike ya fadi haka ne ne yayin da yake jawabi ga magoya bayansa a ƙaramar hukumar Emohua da ke jihar Rivers a wata ziyara da ya kai ranar Litinin.
Asali: Legit.ng

