Gwamna Otti Ya Cika Baki kan Tazarce a Zaben Shekarar 2027

Gwamna Otti Ya Cika Baki kan Tazarce a Zaben Shekarar 2027

  • Gwamnan jihar Abia, Alex Otti ya halarci bikin ranar Aro ta shekarar 2025 da aka gudanar a karamar hukumar Arochukwu
  • A jawabin da ya yi a wajen bikin, Gwamna Otti ya yi tsokaci kan batun sake tsayawa takara a zaben shekarar 2027
  • Gwamna Otti ya nuna cewa bai da wata fargaba kan tazarce domin akwai abubuwan da za su sanya ya yi nasara cikin ruwan sanyi a zaben

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Abia - Gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya yi tsokaci kan babban zaben shekarar 2027 da ake tunkara.

Gwamna Otti ya bayyana kwarin gwiwarsa na sake lashe zabe, yana mai cewa zaben shekarar 2027 zai fi masa sauki idan aka kwatanta da zabubbukan da ya shiga a baya.

Gwamna Otti ya hango nasararsa a zaben 2027
Gwamnan jihar Abia, Dr. Alex Otti a ofis Hoto: @alexottiofr
Source: Facebook

Tashar Channels tv ta rahoto cewa Gwamna Otti ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a bikin ranar Aro ta 2025 da aka gudanar a karamar hukumar Arochukwu ta jihar Abia.

Kara karanta wannan

Bayan harin Amurka, Akpabio ya fadi lokacin kawo karshen matsalar rashin tsaro

Me Gwamna Otti ya ce kan zaben 2027?

Gwamna Otti ya ce ba ya jin tsoron zaben 2027, domin nasarorin da gwamnatinsa ta samu tun bayan hawansa mulki za su taimaka masa matuka.

Ya ce ba zai sake alkawurra ga jama’a ba, sai dai zai dogara ne da abubuwan da suke gani da idonsu na ayyukan da gwamnatinsa ke yi.

“Kamar yadda aka yi a 2023, zaben 2027 ma zai fi sauki sosai, ina tabbatar muku. Me ya sa nake da wannan kwarin gwiwa? Ina da kwarin gwiwa ne saboda a 2023 mun yi alkawurra, amma a yanzu akwai abubuwa daya ko biyu da za mu iya nuna wa jama’a."

- Gwamna Alex Otti

Otti ya ce wasu na damuwa kan 2027

Gwamna Otti ya jaddada cewa mutane da dama sun riga sun fara damuwa kan zaben 2027, duk da cewa har yanzu lokacin zaben bai kusa ba.

“Har yanzu 2027 na da nisa, amma mutane da dama sun riga sun fara hallaka kansu tun kafin 2027 ta zo."

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida ya ba wa gwamnonin Arewa mafita game da matsalar tsaro

“Ba mu damu da 2027 ba, domin muna da amanar shekaru hudu da za mu cika wa al’ummarmu. Mun yi watanni 30 kacal, don haka har yanzu muna da dogon zango a gaba."

- Gwamna Alex Otti

Gwamna Otti ya ce zai yi nasara a zaben 2027
Gwamna Alex Otti na jihar Abia na jawabi a wajen taro Hoto: @alexottiofr
Source: Facebook

Sanusi II ya yabawa Gwamna Otti

A nasa jawabin, Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya yaba wa nasarorin da Gwamna Alex Otti ya samu.

Sanusi II ya ce har a wajen jihar Abia da ma Najeriya baki daya, mutane sun lura da gagarumin sauyi da aka samu cikin shekaru biyu da suka gabata na mulkin Gwamna Otti.

“Ina so na taya Dakta Otti murna bisa dukkan ayyukan da ya yi a jihar Abia. Na tabbata a gare ku ’yan Abia, babu bukatar wani ya fada muku."
"Amma yana da kyau ku sani cewa har ma a wajen Abia da wajen Najeriya, kowa ya lura da gagarumin sauyin da aka samu a cikin shekaru biyu da suka gabata."

- Muhammadu Sanusi II

Gwamna Otti zai daina siyasa

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya bayyana shirinsa na daina yin siyasa.

Kara karanta wannan

Tura ta kai bango: Gwamna ya yi nadamar marawa Tinubu baya a 2023

Gwamna Otti ya bayyana cewa ba shi da burin tsayawa takarar shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa ko sanata bayan ya bar mulki.

Hakazalika, ya sake jaddada matsayarsa cewa zai yi ritaya daga siyasa bayan kammala wa’adinsa na gwamna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng