Wike Ya Fadi Abin da Shugaba Tinubu Ya fi Shi Samu a Fagen Siyasar Najeriya

Wike Ya Fadi Abin da Shugaba Tinubu Ya fi Shi Samu a Fagen Siyasar Najeriya

  • Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya jaddada goyon bayansa ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
  • Nyesom Wike ya bayyana cewa shi ne dan siyasar da aka fi zagi a Najeriya bayan Shugaba Bola Tinubu
  • Ministan ya kuma bayyana cewa daga watan Janairun shekarar 2026 za a buga kugen siyasa a jiharsa ta Rivers

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Rivers - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Cif Nyesom Wike, ya kwatanta kansa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Wike ya bayyana kansa a matsayin dan siyasar da ake zagi fiye da kowa a Najeriya a halin yanzu bayan Shugaba Bola Tinubu.

Wike ya ce ana zaginsa a fagen siyasar Najeriya
Ministan babban birnin tarayya Abuja tare da Shugaba Bola Tinubu Hoto: @GovWike
Source: Twitter

Jaridar The Nation ta ce Wike ya fadi hakan ne yayin wani taron godiya na musamman da shugaban hukumar ci gaban yankin Kudu maso Kudu (SSDC), Prince Chibudom Nwuche, ya shirya.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Shugaba Tinubu ya nemi daukin kasar waje bayan Amurka

An shirya taron ne a gidan Prince Chibudom Nwuche da ke Ochiba, a karamar hukumar Ahoada ta Gabas ta jihar Rivers a karshen mako.

Ministan ya kuma bayyana cewa daga watan Janairun 2026, siyasa za ta sake daukar zafi a jihar Rivers.

Wike ya jaddada goyon bayansa ga Tinubu

Tsohon gwamnan na jihar Rivers, wanda ya jaddada matsayinsa na goyon bayan Shugaba Tinubu ba tare da tangarda ba, ya ce bai taba karya wata yarjejeniya da ya kulla ba, jaridar Vanguard ta dauko labarin.

Wike ya yi amfani da damar taron godiyar wajen yabawa al’ummar kananan hukumomin Ahoada ta Gabas da Ahoada ta Yamma bisa goyon bayan da suka ba shi wajen mara wa Shugaba Tinubu baya.

Wike ya yi godiya ga mutanen Rivers

"Wannan ita ce karamar hukuma ta farko da muka zo domin mu yi godiya saboda tsayawa tare da mu tsawon wadannan shekaru.”
“Kun sani, kamar yadda fasto ya fada a yau, Allah ba Ya son marasa godiya. Don haka bisa abin da kuka yi mana, da tsayawa tare da mu, muna cewa mun gode. Mun gode, mun gode sosai."

Kara karanta wannan

Bayan harin Amurka, Akpabio ya fadi lokacin kawo karshen matsalar rashin tsaro

“Kun tuna a shekarar 2023, lokacin da abubuwa suka yi tsauri, babu wanda ya san abin da zai faru a wancan zaben. Wani ma yana cewa zai yi wahala Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya lashe zaben.”
“Ba mu taba ja da baya ba wajen goyon bayan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Idan kuna son sani, bayan Bola Tinubu, ni ne dan siyasar da aka fi zagi. Me ya sa ake zagina? Saboda sun san yarjejeniyar mene ne?"
“Idan mun amince da wani abu, dole a aiwatar da shi. Idan ba za ka iya aiwatarwa ba, kada ma ka kuskura ka shiga yarjejeniya. Don haka tun tuni mun yanke shawarar cewa dole mu ci gaba da goyon bayan Ahmed Bola Tinubu."
“Wannan shi ne matsayar da kuka dauka. Kuma wannan shi ne matsayar da za mu ci gaba da dauka. Don haka a madadin tawagarmu, muna so mu gode muku, jarumanmu na kasa, wadanda suka tsaya daram duk da dukkan tsokanar da ake yi."

- Nyesom Wike

Wike ya ce zai ci gaba da goyon bayan Tinubu
Tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike Hoto: @GovWike
Source: Facebook

Wike ya ragargaji gwamnonin PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ragargaji gwamnonin Bauchi da Oyo.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tuna abota, rikon amanar Ganduje da ya cika shekaru 76

Wike ya bayyana cewa Gwamna Bala Mohammed da Seyi Makinde sun yi kadan su kore shi daga jam'iyyar PDP.

Ministan ya bayyana cewa ya bayyana cewa ya kasance cikin PDP tun daga lokacin da aka fara shirin kafa ta a shekarar 1990.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng