Peter Obi Ya Gama Yanke Shawara kan Batun Komawa Jam'iyyar ADC

Peter Obi Ya Gama Yanke Shawara kan Batun Komawa Jam'iyyar ADC

  • Jam'iyyar ADC na shirin yin babban kamu a fagen siyasar Najeriya yayin da ake ci gaba da tunkarar babban zaben shekarar 2027
  • Majiyoyi sun bayyana cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, ya kammala yanke shawara kan batun zama mamba a ADC
  • Hakazalika, an bayyana cewa shirye-shirye sun yi nisa kan shirin shigarsa jam'iyyar bayan ya gana da shugabanta na kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar LP, Peter Obi, na shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar ADC a hukumance.

Peter Obi zai koma ADC ne yayin da ake ci gaba da tattaunawa gabanin babban zaben shekarar 2027.

Peter Obi zai koma jam'iyyar ADC
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi da tambarin jam'iyyar ADC Hoto: @PeterObi
Source: Twitter

Wani babban jami’in jam’iyyar a Abuja ya shaida wa jaridar The Punch cewa Peter Obi ya kammala shirye-shiryen shiga jam’iyyar ADC.

Kara karanta wannan

Bayan harin Amurka, Akpabio ya fadi lokacin kawo karshen matsalar rashin tsaro

Yaushe Peter Obi zai koma ADC?

Ya bayyana cewa za a gudanar da gangamin bayyana matsayarsa a birnin Enugu, cibiyar siyasar yankin Kudu-maso-Gabas, a ranar 31 ga Disamban 2025.

A cewar jami’in, magoya baya da mabiyan Petee Obi sun riga sun fara shirye-shiryen sauya shekar.

Majiyar ta bayyana cewa bayan ADC ta bukaci Peter Obi ya yanke shawara kan ko zai shiga jam’iyyar kimanin makonni uku da suka gabata, sai ya gana da shugabanta na kasa, David Mark, domin sabunta biyayyarsa ga hadakar.

Me ya ja hankalin Peter Obi zuwa ADC?

Ya ce matsayar da jam’iyyar ta dauka na iya zama abin da ya gamsar da tsohon gwamnan na jihar Anambra ya yanke shawarar shiga ADC a karshe.

“Mun san cewa Peter Obi na shirin bayyana matsayarsa a ADC a ranar 31 ga Disamban 2025 a Enugu. Ko da yake bai sanar da jam’iyyar a hukumance ba tukuna, amma shirye-shiryen gaskiya ne.”

Kara karanta wannan

Sanata ya hango abin da zai wargaza APC duk da yawan sauya shekar 'yan adawa

- Wata majiya

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa Peter Obi zai fi son bayyana matsayarsa a Enugu maimakon Anambra, jiharsa ta haihuwa, jami’in jam’iyyar ya ce:

“Enugu ita ce cibiyar siyasar yankin Kudu-maso-Gabas. Peter Obi yana wakiltar yankin gaba daya ne, ba jiharsa kadai ba. Wannan ne ya sa ya dauki wannan mataki.”
Peter Obi na shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC
Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi Hoto: @PeterObi
Source: Facebook

Me ADC ta ce kan sauya shekar Peter Obi?

Sai dai sakataren yada labarai na kasa na jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ya ce ba zai iya tabbatar da shirin sauya shekar Peter Obi ba.

“Abin da yake a fili shi ne, babu wata sanarwa ta hukuma tukuna. Amma ana ci gaba da tattaunawa."

- Malam Bolaji Abdullahi

Haka zalika, shugaban kungiyar Obidient Movement, Dakta Yunusa Tanko, ya ki yin tsokaci kai tsaye kan lamarin, yana mai cewa Peter Obi ne kadai zai iya yin magana a kai.

ADC ta nuna shakku kan Atiku, Peter Obi

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta nuna damuwa kan yiwuwar aiki tare tsakanin Peter Obi da Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

"Zan doke Gwamna Alia," An samu wani farfesa da zai shiga takarar gwamnan Benue

Kakakin ADC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya yi amanna cewa jam’iyyar na cikin damuwa dangane da rashin haɗin gwiwa tsakanin Obi da Atiku.

Hakazalika, ya bayyana cewa manyan 'yan siyasar biyu ba su kadai ba ne ke da burin tsayawa takara a karkashin jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng