'Yan Majalisa 6 da Aka Dakatar da Su a Zamfara Sun Fice daga PDP, Sun Koma APC
- 'Yan majalisar dokoki shida a Zamfara sun fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC sakamakon rikicin cikin gida da zargin gurgunta majalisa
- Masu sauya shekar sun zargi gwamnatin Gwamna Dauda Lawal da mayar da majalisar dokoki tamkar wani sashi na bangaren zartarwa
- 'Yan majalisun sun bukaci majalisar dokokin tarayya da ta binciki dakatar da su da aka yi ba bisa ka'ida ba da kuma gudanar da majalisa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Zamfara - Wasu mambobi shida na Majalisar Dokokin Jihar Zamfara da aka dakatar sun fice daga jam’iyyar PDP mai mulki a jihar zuwa jam’iyyar adawa ta APC.
’Yan majalisar sun bayyana cewa rikicin cikin gida na jam’iyyar PDP, rarrabuwar shugabanci, matsalolin Majalisar Dokokin jihar da kuma abin da suka kira rashin kyakkyawan shugabanci ne ya sa suka sauya sheka.

Source: Facebook
'Yan majalisa 6 sun fice daga PDP
Sun sanar da ficewarsu a hukumance ta wasiku daban-daban amma masu sako iri ɗaya, da suka aike wa Kakakin Majalisar, wadanda jaridar Leadership ta gani a ranar Alhamis.
’Yan majalisar da suka sauya sheƙa sun hada da Hon. Bashar Aliyu Gummi (Gummi I), Hon. Nasiru Abdullahi Maru (Maru ta Arewa), Barr. Bashir Abubakar Masama (Bukkuyum ta Arewa), Hon. Bashir Bello (Bungudu ta Yamma), Hon. Amiru Ahmad Keta (Tsafe ta Yamma), da Hon. Muktar Nasir Kaura (Kaura ta Arewa).
Sun bayyana hakan ne a Gusau, babban birnin jihar Zamfara, bayan wata ganawa da suka yi inda suka tattauna abin da suka kira rashin kyakkyawan tafiyar da ɓangaren majalisa.
A cewarsu, Majalisar Dokokin Zamfara ta kauce wa rawar da kundin tsarin mulki ya dora mata, suna zargin cewa ta koma kamar reshen bangaren zartarwa karkashin Gwamna Dauda Lawal.
Dalilan sauya shekar 'yan majalisar Zamfara
’Yan majalisar sun ce an dakatar da su “ba bisa ka’ida ba” kusan shekaru biyu da suka wuce, lamarin da ya hana al’ummominsu wakilci.
Sun kara da cewa hakan ya sa suka kafa wani bangare na daban na Majalisar domin kalubalantar abin da suka kira kura-kuran majalisa da na bangaren zartarwa, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
Sun kuma zargi sauran ’yan majalisar da yin dokoki da yanke hukunci ba tare da cika ka’idar adadin ’yan majalisa da kundin tsarin mulki ya tanada ba, suna cewa hakan na sanya irin wadannan dokoki su zama marasa inganci.
’Yan majalisar sun yi kira ga Majalisar Tarayya da ta shiga tsakani domin bincike, tare da tabbatar da bin doka da oda a Majalisar Dokokin Jihar Zamfara.

Source: Original
Dalilin shiga APC da martanin majalisa
A dalilinsu na shiga APC kuwa, sun ce an ja hankalinsu ne da manufofin jam’iyyar na adalci, daidaito, hadin kai da siyasa mai zaman lafiya, wanda suka ce zai ba su damar yi wa al’ummominsu aiki yadda ya kamata tare da taimakawa ci gaban jihar.
Bayan karanta wasikun sauya sheƙar, Gummi ya taya su murna bisa shiga APC, yana mai cewa matakin zai taimaka wajen samar da kwanciyar hankali da ci gaba a jihar da ma kasa baki daya.
Haka kuma, sun ambaci matsalar tsaro a Zamfara da kuma abin da suka kira rikice-rikice a cikin PDP a matsayin wasu dalilan barin jam’iyyar.
Sun danganta matakin nasu da tanadin Sashe na 109 (1)(g) na Kundin Tsarin Mulkin 1999 (da aka yi wa kwaskwarima).
Dan majalisar Zamfara ya sha ruwan duwatsu
A wani labari, mun ruwaito cewa, fusatattun mutane sun tayar da kura a garin Dansadau da ke Zamfara, bayan sun yi wa dan majalisar mazabarsu ature da duwatsu.
Fusatattun mutanen sun zargi dan majalisar da rashin ziyartar mazabarsa, rashin jajanta wa wadanda hare-haren ‘yan bindiga suka shafa a yankin.
A cikin wani bidiyo da ya karade kafofin sada zumunta, an ga yadda mutane suka rika jifar dan majalisar, har da marinsa, suna ihun 'ba ma yi' har aka sanya shi a mota.
Asali: Legit.ng


