Tsohon Sanata Ya Samu Mukami da Shugaban Jam'iyyar APC Ya Nada Hadimai 15

Tsohon Sanata Ya Samu Mukami da Shugaban Jam'iyyar APC Ya Nada Hadimai 15

  • Shugaban APC Nentawe Yilwatda ya nada kwararrun mataimaka da mashawarta domin gudanar da harkokin jam'iyyar a matakin kasa
  • Wadanda aka nada sun hada da tsofaffin sanatoci da kwararru kan yada labarai, bincike, domin karfafa martabar jam'iyyar mai mulki
  • Yayin da Legit Hausa ta jero dukkanin sunayen wadanda aka nada, jam'iyyar ta bukace su da su nuna sadaukarwa ga manufofin APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya amince da naɗin masu ba da shawara na musamman da manyan mataimaka na musamman domin ƙarfafa tsarin gudanarwa da dabarun jam’iyyar.

Nadin sababbin hadiman na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mustapha Dawaki, shugaban ma’aikatan shugaban APC na ƙasa ya sanya wa hannu.

Shugaban jam'iyyr APC na kasa, Nentawe Yilwatda, ya nada sababbin hadimai 15
Shugaban jam'iyyar APC, Nentawe Yilwatda tare da Imran Muhammad, daya daga cikin sababbin hadimansa. Hoto: @jarmari01
Source: Twitter

Shugaban APC ya nada sababbin hadimai

A cikin sanarwar, APC ta ce ana sa ran waɗanda aka naɗa za su yi amfani da ƙwarewarsu da kwarewar aiki wajen tallafa wa ayyukan shugaban jam’iyyar, in ji rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

An gudu ba a tsira ba, PDP ta koma kan shawarar Saraki game da rikicin gida

Sanarwar ta ce:

“Waɗannan naɗe-naɗen na daga cikin ƙoƙarin da ake yi na ƙarfafa daidaitaccen tsari, tsara manufofi, da hulɗa da masu ruwa da tsaki a sakatariyar jam’iyya ta kasa.
“Ana sa ran sababbin mataimakan da aka naɗa za su kawo gagarumar gudunmawa ta kwarewa da ƙwarewar aiki wajen taimaka wa shugaban jam’iyya a aikinsa.”

Tsohon sanata ya samu mukami

An nada Danladi Sankara, tsohon sanatan Jigawa a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa yayin da Daniel Reyenieju Oritsegbubemi ya samu mukamin mai ba da shawara na musamman kan harkokin majalisar dokoki, inda Sorochi Longdet ya zama mai ba da shawara na musamman kan bincike, dabaru da tsare-tsare.

An nada Jibrin Abdullahi Surajo matsayin mai ba da shawara kan hulɗa da al’umma, Paul Domsing ya zama mai ba da shawara kan ayyuka na musamman, in ji rahoton Punch.

Suleiman Bukari ya samu mukamin mai ba da shawara kan daidaita bayanan sirri, yayin da Taiwo Ajibolu Balofin ya zama mai ba da shawara na girmamawa kan haɗin kai da ƙarfafa ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje.

Kara karanta wannan

Sanata ya hango abin da zai wargaza APC duk da yawan sauya shekar 'yan adawa

An nada Imran Muhammad matsayin babban mataimaki na musamman kan sababbin kafafen watsa labarai, Mildred Bako ta zama babbar mataimakiya ta musamman kan ƙungiyoyin farar hula.

An ce sababbin hadiman Nentawe Yilwatda za su taimaka wajen inganta harkokin APC.
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Nentawe Yilwatda yana jawabi a wani taro. Hoto: @nentawe1
Source: Twitter

Sauran sababbin hadiman shugaban APC

Yusuf Dingyadi ya samu mukamin babban mataimaki na musamman kan kafafen watsa labarai, yayin da Enenedu Idusuyi ta zama babbar mataimakiya ta musamman kan ladabi da tsari.

Haka kuma, an nada Ismaila Sadis Mohammed matsayin babban mataimaki na musamman kan kula da rikice-rikice, Zarah Onyinye ta zama babbar mataimakiya ta musamman kan hulɗar jama’a, Adaku Apugo ta zama babbar mataimakiya ta musamman kan hulɗa tsakanin gwamnatoci, yayin da Obinta Juliet Chinenye aka naɗa ta babbar mataimakiya ta musamman kan tunkarar matasa.

Sanarwar ta ƙara da cewa shugaban jam’iyyar ya taya waɗanda aka naɗa murna, tare da buƙatar su nuna jajircewa, aminci da biyayya ga manufofi da muradun jam’iyyar APC.

Shugaban APC ya samu sarautar gargajiya

A wani labari, mun ruwaito cewa, shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya samu sarautar gargajiya a masarautar Tiv.

Farfesa Nentawe Yilwatda zai samu babbar sarautar gargajiya a masarautar Tiv mai daraja, wato Zegbar-u-Tiv tare da matarsa, Dr. Martina Yilwatda.

An bayyana cewa Tor Tiv, mai martaba Farfesa James Iorzua Ayatse, ne zai yi nadin sarautar, wadda za ta samu halartar majalisar sarakunan gargajiya ta Tiv.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com