Sanata Sankara ya bar PDP zuw APC a Jigawa
- Martaban jam’iyyar APC ta jihar Jigawa ta samu karuwa kwanan nan
- Akalla yan jam’iyyar adawa (PDP) guda 8,905 ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a jihar tare da shuwagaban su, Sanata Danladi Sankara
- Wannan taken ya kasance cikin shirin jiran zabe da za'a gudanar a 2019, Alhaji Danladi Sankara, tsohon sanata mai wakiltan yankin Arewa-maso- yammacin Jigawa, ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC
Kamfanin dillancin labarai ta rahoto cewa gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Abubakar Badaru ya karbi bakuncin Sankara, a filinAminu Kano triangle squre a ranar Lahadi, 29 ga watan Oktoba.
Badaru ya fada cewa sauya shekan tsohon sanatan zai kawo cigaba ga jam’iyyar a jiha.
Gwamnan ya fada cewa jam’iyyar APC ta yi kamun babban kifi, don shigar Sankara zuwa jam’iyyar APC idan aka dubi kwarinsa a jam’iyyar sa na da.
Badaru ya tuno cewa Sankara ya taba rike mukamin mataimakin shugaban jam’iyya ta kasa, yankin Arewa-maso-yamma da kuma shugaban jam’iyyar a jihar Sokoto.
“Shekan shi zuwa jam’iyyar APC, PDP zata rushe gaba daya a jihar Jigawa saboda Sankara yana daya daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar PDP a kasar, kuma shine ya kawo ta jihar Jigawa,” cewar shi.
Gwamnan, har ila yau ya fada cewa gwamnatin da ta gabata ta bar alhakin kwangila na kimanin naira biliyan N92 gare shi amman tare da taimakon Allah da kuma taimakon mutanen kwarai a jihan, ya rinjayi al’amrin.
KU KARANTA KUMA: Allah ya yiwa matar da ta haifi ‘yan hudu a jihar Katsina rasuwa (hoto)
Yayi korafi kan dubban matsaloli da gwamnatin PDP da ta gabata ta bari a matakan jihohi da tarayya wanda ya sa shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da kudin beli ga jihohi.
Cif John Oyegun, shugaban jam’iyyar APC ta kasa, wanda ya samu wakilcin shugaban jam’iyyar a yankin Arewa-maso-yamma, Alhaji Shuaibu Lawal a wani taro, ya tabbatar da cewa Sanata Sankara zai samu adalci daidai da yanda sauran mambobin jam’iyyar suke samu a jam’iyyar.
A baya, yayinda yake bayyanawa bisa ka’ida ga jam’iyyar, Sankara ya ce zai shiga jam’iyyar ne tare da magoya bayan shi 8,905.
Sankara yayi alkawarin yin aiki don ganin an samu hadin kai da ci gaban jam’iyyan, don lashe zabuka a jihan da kuma matakin tarayya.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng