An Gudu ba a Tsira ba, PDP Ta Koma kan Shawarar Saraki game da Rikicinta
- Shugabannin PDP na duba yiwuwar komawa tsarin sulhu na tsohon gwamnan Kwara, Sanata Bukola Saraki
- Jiga-jigan sun bayyana haka ne domin shawo kan rikicin cikin gida da ya raba jam’iyyar gida biyu wanda ke jawo mata asara
- Wannan mataki ya biyo bayan wasikar INEC da ta ƙi amincewa da kwamitin NWC ƙarƙashin Tanimu Turaki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugabannin jam’iyyar PDP na tunanin komawa tsarin sasanci na tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki.
Sanata Saraki ya taba gabatar da tsari mai kyau domin warware rikicin da ya raba jam’iyyar gida biyu.

Source: Facebook
Abin da INEC ta ce kan kwamitin Turaki
An ce hakan ya samo asali ne bayan Hukumar INEC ta ƙi amincewa da Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa ƙarƙashin jagorancin Tanimu Turaki, cewar Daily Trust.
A cikin wata wasika wadda aka bayyana ga jama’a, INEC ta sanar da lauyoyin PDP cewa ba za ta iya amincewa da NWC na Turaki ba saboda batun yana gaban kotu.
Hukumar ta ce ba za ta ɗauki wani mataki na gudanarwa da zai iya shafar hukuncin da kotu za ta yanke ba.
Kwamitin Turaki na samun goyon bayan Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, da takwaransa na Jihar Bauchi, Bala Mohammed.
Taron jam’iyyar na watan Nuwambar 2025 da ya haifar da sababbin shugabanni ya biyo bayan hukuncin kotuna masu karo da juna.
Hukuncin kotuna mabambanta kan rikicin PDP
Yayin da wasu kotunan tarayya a Abuja suka hana PDP gudanar da taron bisa zargin saba wa kundin tsarin jam’iyya da dokar zabe, wata babbar kotu a Ibadan, Jihar Oyo, ta ba jam’iyyar damar ci gaba tare da umartar INEC ta sa ido.
INEC ta gayyaci bangarorin biyu a makon da ya gabata domin tattaunawa, musamman ganin shirye-shiryen zaben kananan hukumomin Abuja na 2026 na karatowa.

Source: Facebook
Yadda PDP ke neman dawowa shawarar Saraki
Majiyoyi sun ce shugabannin PDP na tsoron barin kotuna su warware rikicin, domin hakan na iya haifar da masu nasara da masu shan kaye, abin da zai ƙara raba jam’iyyar.
Wani jagoran PDP ya ce:
“Matsaya ta gaba ita ce komawa tsarin Saraki. Kada mu jira kotu ta yanke hukunci, domin hakan zai ƙara lalata al’amura.”
Sanata Saraki, wanda ya taɓa jagorantar kwamitin sasancin jam’iyyar, ya sha gargadin cewa yawan shari’o’i na iya hana PDP samun ci gaba.
Ya ce hakan kuma zai lalata haɗin kan jam’iyyar, yana mai kira da a gudanar da taron ƙasa mai haɗe da kowa da kowa, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Sanata Moro ya yi hasashen wargajewar APC
An ji cewa 'yan jam'iyyun adawa musamman PDP na ci gaba da tururuwar sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Sanata Abba Moro na jihar Benue ya nuna damuwa kan yadda mambobin PDP ke ci gaba da barin jam'iyyar zuwa APC.
Sai dai, shugaban masu rinjayen na majalisar dattawa ya bayyana illar da hakan yake da ita ga APC da dimokuradiyyar Najeriya.
Asali: Legit.ng

